Posts

Showing posts from March, 2020

Taron Horaswa kyauta don koyar da yadda ake kirkiran 3d video Animation da Business Card

Image
Taron Horaswa kyauta don koyar da yadda ake kirkiran 3d video Animation da Business Card Kamar yadda muka Saba gabatar da training, Idan ba a manta ba a shekaran data gabata mun gabatar da free training da dama wadanda su kafi shahara daga cikin su sune na koyar da blogging da sharing block url a Facebook A wannan karon ma Asagist.com.ng ta shirya taro na musamman don koyar da Al'umma yadda ake hada 3d video Animation da Business Card a kyauta. Menene 3d animation video da Business Card? Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN Yadda zaka samu kudi da blog din ka ta Hanyoyi 5 Hanyoyi 5 da zaka samu kudi a Internet Tsarin Kira masu sauki a layin Glo ✓3d animation video shine video da ake hadawa na cartoon, wasu suna comedy dashi wasu Kuma tallata kasuwanci su keyi dashi. ✓Business card shine katin shaidan kasuwanci, kamar ID Card yake Wanda kamfanoni da 'yan kasuwa suke amfani dashi a matsayin shaida na kasuwancin su. 3d v...

Sakamakon Gwajin Sunusi Lamido Sunusi na Coronavirus Ya Fito

Image
Sakamakon Gwajin Coronavirus da a ka yiwa tsohon Sarkin Kano malam Muhammad Sunusi Lamido Sunusi ya Fito. Idan baku baku manta ba Gwamnan Jahar kaduna ya kamu da cutar dake sakale numfashin na Covid 19 Wanda a kafi Sani da Coronavirus. A jiye ne 28 ga watan uku sakamakon gwajin da a kayi mishi ya fito Wanda ya nuna ya kamu da cutar Kuma yanzu Haka an killace shi domin gabatar mishi da jinya. Karanta:  Malam Nasir Elrufa'i ya kamu da Coronavirus Da yake cutan a na kamuwa da ita ne ta hanyar mu'amala da Wanda ya kamu da cutar Kuma an Samu mu'amala Mai karfi a tsakanin Sunusi Lamido Sunusi da Gwamnan Kano. Tun Bayan da a ka tabbatar da Gwamnan kaduna ya kamu da cutar,  mutane da dama suke Kira ga tsohon Sarkin Kano malam Sunusi Lamido Sunusi da yaje a mishi gwajin coronavirus Sakamakon cudanya da su kayi da Nasir Elrufa'i Bayan an sauke shi daga sarautar Sarkin Kano. Idan baku manta ba Bayan an sauke Sarkin Kano daga sarautar shi mal...

Sauke Application na zana jarabawar JAMB da waya ko computer (Practice App)

Image
Application nayin jarabawar JAMB da waya ko computer Cikin wannan rubutu Zan yi bayani ne game da wani Application Wanda a ke yin jarabawar JAMB dashi, Akwai na computer akwai Kuma Wanda za ka iya amfani dashi a waya. Kamar yadda wata kila ka Sani a shekarun baya a na rubuta jarabawar JAMB ne da pepper da pencil, bayan an kammala rubuta jarabawar sai wadanda suke lura da rubuta jarabawar su tafi dashi su Kai a yi marking bayan wani lokaci sai a fito musu da Sakamakon jarabawar su. Bayan daukan lokaci Mai tsayi a na wannan wahala ta rubuta jarabawar da pencil da pepper sai a ka samu ci gaba na fasahan zamani a ka fara rubutawa da Computer. Ana amfani ne da software don gudanar da jarabawar, da Yake da computer a ke amfani don gudanar da jarabawar a yanzu. Karanta:   JAMB ta Dakatar da duba result ta website din ta, ta Bada sabuwan hanyar duba sakamako An samar da software da dama da a ke amfani dashi don gwada rubuta jarabawar (JAMB UTME pr...

Gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya kamu da Coronavirus

Image
Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i Ya kamu da wannan cuta ta Covid 19 a sanarwan da Yake fitowa yanzu Haka daga gare shi. Sanarwan ya fito ne daga shafin shi na Facebook cikin video ya baiyana cewa lallai sakamakon gwajin da a ka mishi ya fito Kuma ya nuna Yana dauke da cutar dake sakale numfashin Dan Adam wato Covid 19. Ya fitar da sanarwan ne a yammacin ranar Asabar 28 ga watan Maris na shekarar 2020 da misalin karfe   8 da rabi na Yamma a shafin shi na Facebook Karanta:   Dalilin da yasa muka Kori Gudaji kazaure Daga APC- Shugabannin jam'iyar APC Lokacin da Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i Yake bayani game da sakamakon gwajin coronavirus da a ka mishi. A cikin Videon Wanda yakai tsawon kusan Minti daya, El-Rufa'i ya baiyana cewa yanzu Haka an kebe shi domin gabatar da jinya na wannan cuta da ta kama shi. Zaka iya kallon jawabin da yayi ta wannan Link  Shiga Nan Idan Mai karatu bai manta ba a satin da ya gabat...

Dalilin da yasa muka Kori Gudaji kazaure Daga APC Inji jam'iyar APC

Image
An Kori Dan majalisa Honourable Muhammad Gudaji kazaure Daga jam'iyar APC Jam'iyar APC ta jahar jigawa ta baiyana dalilin ta na koran fitaccen Dan Majalisan Nan Mai suna Honourable Muhammad Gudaji kazaure Daga jam'iyar. Jam'iyar ta baiyana hakan ne a wata takadda ta musamman da ta fitar Mai dauke da sa Hannun shugabannin jam'iyar  APC na Yankunan da Dan Majalisan Yake wakilta a Jahar jigawa. Kamar yadda sanarwan ta gabata shugabannin jam'iyar ne suka yanke hukuncin koran shi daga jam'iyar in ji su. Honourable Muhammad Gudaji kazaure dai shine Dan Majalisa Mai wakiltan wasu kananan hukumomi a jahar jigawa, kananan hukumomin sune kamar haka; Kazaure, Roni, Gwiwa da 'yan kwashi. Cikin sanarwan, shugabannin jam'iyar sun ce sun Kori Gudaji kazaure Daga APC ne saboda ba ya bin dokoki da ka'idodin jam'iyar. Mutane da dama sun baiyana Ra'ayin su Kan lamarin yayin da wasu suke ganin fadan cikin Gida ne wasu Kuma sun ...

An baiyana sunan Dan kwallon da yafi Yawan Albashi a 2019

Image
An bayyana albashin 'yan kwallon da suka fi yawan albashi a shekarar da ta gabata na 2019, ko da yake akwai manyan 'yan wasa guda uku (3) da suke karban albashi iri daya a shekaran baya, wadannan manyan 'yan wasa sune kamar haka; Cristiano Ronaldo Lionel Messi  Neymar Messi da Cristiano ne kadai 'yan wasan kwallon kafa da suka Zarce yuro miliyan 100 a yayin da Messi yake Samun Yuro miliyan 131, christiano Ronaldo kuma Yuro miliyon 118 sai Neymar Ya biyo Bayan su da Yuro miliyon 95. Abunda Yafi jan Hankalin mutane shine yadda kylian Mbappe Yake da karancin albashi Wanda dukan su uku sun Ninka abunda Yake karba domin yuro miliyon 27 kacal ne albashin shi amma Kuma shine mafi tsada (valuable footballer) cikin Yan kwallon duniya. Shine na goma (10) a cikin su Amma Kuma sai Yafi su tsada wai ko me ya janyo Haka? Zaka iya bamu amsa idan ka sani Sunayen 'yan kwallo da su kafi samun kudi a shekaran 2019 * Lionel Mes...

Coronavirus: Hukumar zana jarabawar JAMB ta Dakatar da zuwa Ofishin ta saboda Coronavirus

Image
Hukumar zana jarabawar sharan fage na Shiga makarantun gaba da sakandare JAMB ta Dakatar da zuwa afishin ta a fadin Nigeria saboda gudun yaduwan cutar coronavirus Wanda a ka chanjawa suna zuwa Covid-19 Hukumar ta Bada sanarwan ne bayan Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun fadin kasar na tsawon wata daya saboda tsoron kar cutan ta yawaita a kasan Baki daya. Hukumar ta Bada sanarwan ne ta bakin Mai magana da Yawun hukumar a kafofin sada zumunta na zamani Mr Fabian a ranar Talata a Birnin tarayya Abuja. Karanta:  Hukumar WAEC ta daga zana jarabawar Bana Ga abunda Yake cewa; " Muna sanar da wadanda suka rubuta jarabawar JAMB na Bana da sauran jama'a, saboda shawarwarin masana da gudun yaduwan cutar Covid 19 mun Dakatar da wasu ayyukan mu na Dan wani lokaci." Dakatarwan ya shafi duk office na JAMB dake Nigeria saboda gudun cunkoson jama'a a guri daya, Bayan komai ya daidaita zamu koma Aiki ba tare da Bat...

Yadda ake dora Audio a Facebook Cikin Sauki

Image
Tun ba yau ba Na ga wasu daga Cikin abokai na musamman na Facebook suna tambayar yadda zasu Dora audio a Facebook, Har wasu suna cewa "Ko dai ba a iya saka audio ne a Facebook? Masu wannan tambayar suna da Yawa wanda har wasu sun fara tunanin kila ba a Dora audio a Facebook ne, wannan tunanin tayi tasiri sosai a zukatan wasu daga cikin ma'abota amfani da dandalin sada zumunta na zamani na Facebook. Ko kasan dalilin da yasa tayi tasiri a zukatan su? Babban dalilin yin tasirin shine Idan kaje gurin yin posting a Facebook za a baka daman dauko Abu daga Kan computer ko wayar ka Kai tsaye Kuma zaka Dora Shi a Facebook. Daga cikin Abubuwan da zaka iya daukowa za kaga akwai Hotuna da Videos Amma Kuma babu audio a gurin Dalilin da yasa suke cewa ba a Dora audio a Facebook kenan Kuma shine babban dalilin da yasa " ba a Dora audio a Facebook tayi tasiri a zukatan wasu" Karanta:  Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN To ...

Hukumar WAEC ta daga zana jarabawar ta na Bana

Image
Hukumar zana jarabawar WAEC Ta kasa ta daga Rubuta jarabawar ta na shekaran Nan da muke ciki na 2020/2021 Daga jarabawar ya faru ne a dalilin rufe makarantu saboda gudun yaduwan annoban  cutan coronavirus a Nigeria. Idan baku manta ba cutar coronavirus ta shigo cikin Nigeria Wanda a jahar lagos ne a ka fara gano cutar, wannan ne yasa Gwamnatin jahar lagos ta Dakatar da haduwan jama'a a guri daya a fadin Jahar. An Samu wasu daga cikin Gwamnonin Nigeria da suka bayar da umarnin Dakatar da sallar Juma'a a wannan juma'a ta yau 20/03/2020.  *   Gaskiya ne JAMB tayi cancel na sakamakon jarabawan ta na Bana? *  JAMB ta Dakatar da duba result ta portal din ta, ta Bada sabuwan hanyar dubawa Bayan Nan Kuma sai Gwamnatin tarayya itama ta Bada umarnin rufe makarantun Gwamnati da masu zaman Kan su na kasa. Ganin cewa makarantun za a rufe sune daga ranar Litinin Mai zuwa, wasu Kuma an riga an kulle su a Yankunan da a ka Samu masu dauke da c...

Hanyoyin da zaka Kare Kan ka daga kamuwa da Coronavirus

Image
Coronavirus cuta ce Mai yaduwa wacce ake iya kamuwa da ita ta Hanyoyi da dama Kamar mu'amala da Mai dauke da ita da sauran su. Ga wasu daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar: 1. Idan Mai dauke da cutan yayi tari ko atishawa, kwayoyin cutan zasu fito daga bakin shi Kuma cutar zata watsu har ta iya kama Wanda Yake kusa dashi. Shiyasa masana kiwon lafiya su kace a kalla a samu ratan kamar mita daya da rabi tsakanin ka da Mai yin Tari saboda Kariya daga coronavirus da sauran dangogin ta 2. Idan Mai cutan yayi kaki ya tofar (zubar) a kasa, Iska zai iya dauko kwayan cutan daga jikin wannan kakin da a ka zubar, Duk Wanda ya shaki Iskan zai iya kamuwa da ita. 3. Mutum zai iya kamuwa da cutan Idan ya taba gurin da a ka zubar da kwayan cutan sai ya taba Baki, Hanci ko Idanun shi. Misali Mai dauke da cutan Idan ya zauna a guri Yayi kaki, atishawa, fece majina ko wani Abu Mai kama da wannan, Bayan ya bar gurin sai wani ya zauna a gurin shima zai iya kamuwa da cut...

Saurari Hira da a kayi da Wanda ake zargin Ya kamu da Covid19 a katsina cikin audio

Image
An yi Hira Kai tsaye da wani bawan Allah a dutsinma na jihar katsina Wanda a ke zargin Yana da wannan cuta na zamani Mai sarkafe numfashi wato Coronavirus. Ko da Yake zuwa Yanzu an chanjawa cutan suna daga Coronavirus zuwa Covid-19, tun farkon fitowan cutan a na Mata lakabi ne da sunan Dana ambata a farko Amma daga bisani sai a ka chanja mata suna. Karanta:   Gaskiya ne JAMB tayi cancel na sakamakon jarabawan ta na Bana? Cutan ta fara bullowa ne daga kasar chana Wanda ta salwantar da rayukan al'umma da dama Wanda har yanzu tana Kai. Wannan cuta dai a yanzu haka ta yadu a kasashen duniya da dama Wanda a wasu kasashen an Hana duk taron da zai hada Jama'a su cunkushe guri daya ciki har da guraren ibada. A ci gaba da yaduwa da cutan take yi, yanzu haka ta shigo Nigeria yayin da a ka samu kusan mutane uku da suka kamu a jahar Lagos bayan sun yi mu'amala da wani Dan kasar chana daya shigo Birnin Lagos. A karon farko a yankin arewascin Ni...

Da Gaske ne JAMB tayi Cancel sakamakon jarabawan da a ka rubuta ranar Asabar?

Image
Ko Gaskiya ne Hukumar JAMB ta kasa tayi Cancel na sakamakon jarabawan da a ka rubuta ranar asabar, litinin da Talata? Idan Mai karatu bai manta ba an fara rubuta jarabawar JAMB ne na 2020 a ranar asabar 14/03/2020 Wanda har sakamakon ya fito Kuma ya zuwa yanzu dai kusan idan Akwai wadanda basu duba nasu ba to tabbas sune su kafi kadan. Kamar yadda wata Kila Kai ma kaji labarin, Jita-jita Yana yawo Wanda Yake nuni da cewa Hukumar JAMB ta kasa tayi watsi da sakamakon jarabawan da a ka zana a  ranar asabar, Litinin da Talata. Karanta:  JAMB ta Dakatar da duba result ta portal din ta, ta Bada sabuwan hanyar dubawa Wannan Jita-jitan ya biyo ne Bayan hukumar ta fitar da sakamakon jarabawar Wanda adadi masu Yawa na wadanda suka zana jarabawar tuni suka duba sakamakon su. Bayan yaduwan wannan labari ne sai Hukumar JAMB ta fito tayi bayani Kuma ta tabbatar da gaskiyan lamari game da wannan labari da a ke yadawa a tsakanin al'umma. Hukumar ta JA...

JAMB ta Dakatar da duba result ta website, Ta sanar da sabon Hanyan dubawa

Image
JAMB ta sanar da sabon Hanyar duba result ga wadanda suka rubuta jarabawa ranar Litinin. Hukumar JAMB ta sanar da cewa a yanzu haka ta fito da wata sabuwar Hanya da za a duba result saboda matsalar da portal din ta Yake fiskanta a daidai wannan lokaci. Idan baku manta ba ranar asabar 14/03/2020 ne a ka fara rubuta jarabawar JAMB Kuma sakamakon ya fara fitowa har wasu sun duba nasu Bayan kwana biyu da rubuta jarabawar. Tun farko hukumar ta Bada sanarwan cewa wadanda suka rubuta jarabawa ranar asabar su  duba sakamakon a portal na JAMB ranar Litinin, Bayan kwana biyu da rubuta jarabawar su kenan. Bayan an yi wannan sanarwan ne mutane da dama sun duba Kuma sun kalli sakamakon na su sai dai kuma a yau ranar laraba 18/03/2020 Hukumar JAMB tace Wadanda suka rubuta jarabawa daga ranar litinin kar su duba ta website saboda barazanar masu kutse a portal na JAMB din. Karanta:   Yadda za kayi wa abokin ka transfer na kudi a Layin Airtel Ma...

Yadda zaka sayi 250mb data a Kan Naira 100 a Layin MTN

Image
Kamar yadda kusan kowa yasan tsare-tsare na sayan data na kamfanin layin waya na MTN, a kullum a na Kara  Samun wasu hanyoyin da a ke sayan data cikin Farashi Mai sauki a Layin MTN. Akwai hanyoyi da dama na sayan data sai dai wani lokacin za samu wani hanyan yafi wani hanyan saukin sayan data. Layin MTN layi ne na kamfanin kasar Afirka ta kudu Wanda su kayi karfi sosai a Nan gida Nigeria Kai ka ce mallakin Gwamnati ne ko na wani Dan kasuwa a Nigeria Rubutu Mai Alaka:  Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN Wannan tsari na MTN garabasa ne har Kashi uku a cikin, ma'ana ba 1GB kadai zaka iya saya ba har sama ko kasa da haka zaka iya saya Kuma ka more Datan ka a yanan gizo da duk inda a ke bukatan data kafin a shiga. Bayan 1GB a Kan Naira 200, zaka iya sayan 250 mb a Kan Naira #100 sai Kuma 4GB a Kan Naira 1000 kacal. Wannan tsarin sayan data ya taimaka sosai wa mutane da dama musamman masu kananan karfi domin Hawa Internet...

Sanarwa ga wadanda su kayi Katin Dan Kasa daga 2012—2014 (National I.D Card)

Image
Hukumar dake da alhakin  samarwa da bayar da katin shaidan Zama Dan Kasa a Nigeria (National Identity Card) Ta fitar da sanarwa zuwa ga wadanda su kayi Katin Zama Dan Kasa tun daga shekaran 2013 zuwa 2015. Sanarwan Yana kunshe ne a shafin su na dandalin sada zumunta na zamani wato Facebook Wanda suka fitar da sanarwan a Ranar 13/03/2020 da misalin karfe shida na yammaci. Karanta:  Yadda zaka duba result din ka na jamb A cewar ta, Hukumar ta fara ne da cewa "wadanda basu karbi katin su na shaidan Zama Dan Kasa ba (National I.D Card) daga 2013 zuwa 2015 Su Kara Hakuri domin Muna kirkiran wata hanya ce wacce zamu baku link da zaku iya dubawa ko Katin ku na shaidan Zama Dan Kasa na dindindin (Plastic I.D Card) ya fito." Hukumar taci gaba da cewa "gaba daya National I.D card da a kayi a 2012 an gama kammala su, Idan a 2012 kayi Kuma baka samu ganin na ka ba. Kayi mana bayani a Comment zamu yi maka tsokaci. Mun gode. Kana da...

Npower; Sanarwa Mai muhimmanci zuwa ga 'yan Npower Tech

Image
Npower ta fitar da sanarwa na musamman zuwa ga wadanda suke yin Npower bangaren Na'ura Mai kwakwalwa Wanda a ke Kira da Npower Tech. Shi dai Npower ya kasu Bangare-Bangare ne Wanda a ka rarraba shi kashi-kashi, kuma ko wane bangare Yana da adadi Mai Yawa na masu yin shi. Daga cikin bangarorin akwai; *. wadanda suke koyarwa a makarantu *. Masu aikin asibiti *. Bangaren sana'o'i Kamar koyar da aikin kafinta, plumbing da sauran su *. Bangaren koyar da ilimin Na'ura Mai kwakwalwa. Yanzu haka Hukumar tsare-tsare na Npower tayi sanarwa na Musamman zuwa ga masu cin moriyan Shirin Npower a Nigeria a cikin shafin su na Facebook. Karanta:  Yadda zaka duba result din ka na jamb Npower sun fitar da sanarwan ne yau Litinin 16/03/2020 Wanda suka ja Hankalin wadanda suke cin gajiyar Npower bangaren Computer wato Npower Tech. npower ta fara ne da cewa "Sanarwa Mai muhimmanci gare ku cikin wannan hoto dake kasa. Kuyi subscribe kafin Ran...

Yadda zaka duba Result din ka na Jamb (Jamb UTME Result 2020)

Image
Duba sakamakon ka na JAMB Cikin Sauki Idan baku manta ba an fara rubuta jarabawar Shiga makarantun gaba da sakandare na Jamb na shekaran Nan da muke ciki a karshen wannan mako Hukumar kula da zana jarabawar Shiga makarantun gaba da sakandare ta kasa (Jamb) ta gabatar da yadda ake duba sakamakon jarabawar ga wadanda suka zana jarabawar a shekaran Nan. Hukumar zana jarabawar ta JAMB ta ce "sakamakon jarabawar Yana fitowa bane Bayan kwana 2 zuwa 3 da rubuta jarabawar, zaka iya zuwa ka fara duba sakamakon ka Bayan ka rubuta jarabawar da kwana 2 zuwa 3. Duk Wanda ya zana jarabawar zai iya duba sakamakon shi (JAMB result) da Kan shi ba sai yaje ya biya kudi an duba mishi ba, kana daga cikin wadanda suka rubuta JAMB? Karanta:   Yadda za kayi wa abokin ka transfer na kudi a Layin Airtel Idan kana daga cikin su toh kayan ka ya tsinke a bakin kaba domin yanzun Nan zaka koyi yadda ake duba sakamakon ba tare da kaje cafe ba. Yadda zaka duba sakamakon ...

Osibanjo ya Sha da kyar a hatsarin mota a Birnin Abuja

Image
Motocin dake yiwa mataimakin shugaban kasan Nigeria Professor yemi Osibanjo sun gamu da hatsari a Birnin Abuja Ayarin motocin Mai girma Mataimakin shugaban kasan Nigeria professor yemi Osibanjo sun yi hatsari a cikin Birnin tarayya Abuja a lokacin da suke rakiyan shi zuwa filin jirgin sama na Nmamdi Azikwe dake babban Birnin tarayyar Nigeri, Abuja. Mun samu labarin cewa daya daga cikin 'yan tawagan ya rasa rayuwar shi a wannan hatsari da ya auku a Birnin Abuja. Majiyar mu tace Wanda ya rasun jami'in Dan sanda ne Mai mukamin sufeta Dan kimanin shekaru Arba'in da biyar (45) Mai suna Ali. Majiyar mu ta nakalto Mana cewa Hadimin mataimakin shugaban kasan a bangaren yada labarai ya tabbatar da rasuwan inda yace "cikin jimami nake sanar muku da mutuwar daya daga cikin 'Yan Sanda dake cikin ayarin mataimakin shugaban kasa" Karanta:   Kalli yadda wani matashi yayi yunkurin Cakumo Buhari a Argungu Wannan Hatsari ya auk...

Kalli Videon matashin da yayi kokarin Damko Buhari a Argungu

Image
Mutumin kwatsam sai gashi a Gaban shugaba Buhari da sauri Yana kokarin Mika Hannu domin ya riko Buhari yayin da jami'an tsaron dake gurin suke jan shi domin nesantar dashi daga inda Buharin Yake. Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ya halarci taron biki na al'adun gargajiya Wanda a ka gabatar a Argungu dake cikin jahar kebbi. Wannan taro an Saba gabatar dashi ne duk shekara a jahar kebbi sai dai Kuma an Dauki tsawon shekaru goma Sha daya (11) ba tare da an Gabatar dashi ba sai wannan shekaran a ka dawo dashi. Jaridan Daily Trust ta ruwaito cewa an harbi matashin a kafa a lokacin da ya kutso Kai domin kusantar shugaban kasan na Nigeria Karanta:  Osibanjo ya Sha da kyar a Hatsarin mota a Abuja Ko da Yake majiyar mu ta tabbatar Mana da cewa daga baya daily trust ta Bada Hakuri, tace lallai ba a Harbi matashin ba sai dai jami'an tsaro sun ja shi zuwa gefe. Abun da wasu daga cikin jama'an Nigeria kenan suke CeCe kuce a Kai, Was...