Taron Horaswa kyauta don koyar da yadda ake kirkiran 3d video Animation da Business Card
Taron Horaswa kyauta don koyar da yadda ake kirkiran 3d video Animation da Business Card
Kamar yadda muka Saba gabatar da training, Idan ba a manta ba a shekaran data gabata mun gabatar da free training da dama wadanda su kafi shahara daga cikin su sune na koyar da blogging da sharing block url a Facebook
A wannan karon ma Asagist.com.ng ta shirya taro na musamman don koyar da Al'umma yadda ake hada 3d video Animation da Business Card a kyauta.
Menene 3d animation video da Business Card?
- Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN
- Yadda zaka samu kudi da blog din ka ta Hanyoyi 5
- Hanyoyi 5 da zaka samu kudi a Internet
- Tsarin Kira masu sauki a layin Glo
✓3d animation video shine video da ake hadawa na cartoon, wasu suna comedy dashi wasu Kuma tallata kasuwanci su keyi dashi.
✓Business card shine katin shaidan kasuwanci, kamar ID Card yake Wanda kamfanoni da 'yan kasuwa suke amfani dashi a matsayin shaida na kasuwancin su.
3d video Animation da Business Card a na samun makodan kudade dasu domin idan ka iya za a Rika neman ka musamman kamfanoni da 'yan kasuwa domin ka tallata musu kanfani ko shagon su ta video na cartoon, Shi Kuma business Card zasu bukaci kayi musu saboda duk inda su kaje zai Zama shaida na cewa lallai a kamfani ko shago kaza suke aiki.
Bayan wannan daga cikin hanyoyin samun kudin akwai koyarwa, Bayan ka koya Kai ma zaka iya bude ajin koyarwa Wanda zaka Rika samun kudin Shiga ta hanyar koyarwan, Eyh tunda da data za ka koyar ai za kasa kudin register ko?
Kuma za a Yi tururuwan Shiga ajin na ka saboda dubban mutane ne suke bukatan iyawa musamman video Animation.
Yaushe ne za a fara Training?
Zamu fara Training ranar lahadi 05/04/2020 Insha Allah, kayi kokari ka kasance online a lokacin domin Bayan mun kammala darasi ba zamu Bada kofan tambaya ko kace Mana baka Nan a kayi darasin ba, Baza mu lamunci wannan ba.
Idan Allah ya yadda bazai wuce kwana 2 ba zamu kammala training.
Ga Mai bukatan Shiga ajin da zamu koyar, Ga link sai ka Shiga Kuma kayi sharing saboda a Samu mutane da Yawa https://chat.whatsapp.com/HDDFEa3Lto9E7VLAjUGjVI
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment