Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya
Baturiyar da tazo ganin saurayin ta tun daga kasar Amurka har zuwa Nigeria ta mutu a wani hotel Bayan wani Rashin lafiya da ya kama ta
Baturiyar 'yar kimanin shekaru sittin (60) ta taso ne takanas ta Kano tun daga Amurka musamman don kawo wa saurayin ta ziyara ta gamu da ajalin ta ne a wani hotel dake warri a jahar delta.
Karanta: Tsarin Kira mafi Sauki a layin MTN
Kamar yadda muka samu labari, budurwar ta mutu ne sanadiyan wani Rashin lafiya Wanda a kace yayi kama da Cuta me sakale numfashin Dan Adam Wanda yake addaban duniya a yanzu haka.
Tabbas wannan saurayi da tazo wurin shi yana tsaka Mai wuya domin majiyar mu ta tabbatar mana da cewa yanzu haka Yana Hanun jami'an tsaro na 'Yan sanda.
Hafiz Inuwa ne kwamishinan 'yan Sanda na jahar Delta shi ya tabbatar da mutuwar wannan baturiya da ta kawo wa saurayin ta ziyara Nigeria.
Kwamishinan 'yan Sandan yaci gaba da cewa "Yanzu Haka saurayin Yana Hanun mu Kuma mun yi magana da jami'an yaki da cututtuka Masu yaduwa na Nigeria bisa ga alamu da a ka gani kafin mutuwar ta"
Karanta: Hanyoyi 5 da zaka samu kudi a Internet
A wani bangaren Kuma ya umarci 'yan sanda dake ofishin da a ka ajiye matashin su yi taka tsan-tsan da mu'amala dashi saboda gudun Kar ko cutar ce tayi ajalin baturiyar.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment