Hukumar WAEC ta daga zana jarabawar ta na Bana
Hukumar zana jarabawar WAEC Ta kasa ta daga Rubuta jarabawar ta na shekaran Nan da muke ciki na 2020/2021
Daga jarabawar ya faru ne a dalilin rufe makarantu saboda gudun yaduwan annoban cutan coronavirus a Nigeria.
Idan baku manta ba cutar coronavirus ta shigo cikin Nigeria Wanda a jahar lagos ne a ka fara gano cutar, wannan ne yasa Gwamnatin jahar lagos ta Dakatar da haduwan jama'a a guri daya a fadin Jahar.
An Samu wasu daga cikin Gwamnonin Nigeria da suka bayar da umarnin Dakatar da sallar Juma'a a wannan juma'a ta yau 20/03/2020.
* Gaskiya ne JAMB tayi cancel na sakamakon jarabawan ta na Bana?
* JAMB ta Dakatar da duba result ta portal din ta, ta Bada sabuwan hanyar dubawa
Bayan Nan Kuma sai Gwamnatin tarayya itama ta Bada umarnin rufe makarantun Gwamnati da masu zaman Kan su na kasa.
Ganin cewa makarantun za a rufe sune daga ranar Litinin Mai zuwa, wasu Kuma an riga an kulle su a Yankunan da a ka Samu masu dauke da cutar.
Wannan ne dalilin da yasa Hukumar zana jarabawar ta Afirka ta Yamma (WAEC) Ta dage zana jarabawar na Bana har sai komai ya daidaita kafin za a sake sa ranar da za a gudanar da jarabawar.
Dama dai an shirya fara gudanar da jarabawar ne ranar 6 ga watan 4 Wanda a yanzu haka dai bai Kai wata daya ba sai a ka Samu wannan matsala ta cutar da har yanzu ba a Kai ga gano maganin ta ba.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment