Hanyoyin da zaka Kare Kan ka daga kamuwa da Coronavirus
Coronavirus cuta ce Mai yaduwa wacce ake iya kamuwa da ita ta Hanyoyi da dama Kamar mu'amala da Mai dauke da ita da sauran su.
Ga wasu daga cikin hanyoyin kamuwa da cutar:
1. Idan Mai dauke da cutan yayi tari ko atishawa, kwayoyin cutan zasu fito daga bakin shi Kuma cutar zata watsu har ta iya kama Wanda Yake kusa dashi.
Shiyasa masana kiwon lafiya su kace a kalla a samu ratan kamar mita daya da rabi tsakanin ka da Mai yin Tari saboda Kariya daga coronavirus da sauran dangogin ta
2. Idan Mai cutan yayi kaki ya tofar (zubar) a kasa, Iska zai iya dauko kwayan cutan daga jikin wannan kakin da a ka zubar, Duk Wanda ya shaki Iskan zai iya kamuwa da ita.
3. Mutum zai iya kamuwa da cutan Idan ya taba gurin da a ka zubar da kwayan cutan sai ya taba Baki, Hanci ko Idanun shi.
Misali Mai dauke da cutan Idan ya zauna a guri Yayi kaki, atishawa, fece majina ko wani Abu Mai kama da wannan, Bayan ya bar gurin sai wani ya zauna a gurin shima zai iya kamuwa da cutan.
Matakan Kariya ko Riga-kafin Covid19
Daga cikin matakan Kariya na wannan muguwar cuta da ake ambata Akwai wadannan;
Karanta: Saurari audio na Hiran da a kayi da Wanda a ke zargi ya kamu da Coronavirus a Katsina
1. Ka Bada rata tsakanin ka da Mai yin tari ko atishawa
2. Wanke Hannu kafin, lokacin da Bayan kammala abinci
3. Tarewa ko kuma rufe Hanci da Baki a lokacin da za kayi atishawa ko tari Musamman idan ba Kai kadai bane a gurin
4. Ka nisanci duk wani Abu Mai dauke da kazanta
Muna Rokon Allah ya tsare mu daga kamuwa da wannan cuta da makamantan ta, wadanda suke fama da ita Allah ya Yaye musu.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment