Osibanjo ya Sha da kyar a hatsarin mota a Birnin Abuja
Motocin dake yiwa mataimakin shugaban kasan Nigeria Professor yemi Osibanjo sun gamu da hatsari a Birnin Abuja
Ayarin motocin Mai girma Mataimakin shugaban kasan Nigeria professor yemi Osibanjo sun yi hatsari a cikin Birnin tarayya Abuja a lokacin da suke rakiyan shi zuwa filin jirgin sama na Nmamdi Azikwe dake babban Birnin tarayyar Nigeri, Abuja.
Mun samu labarin cewa daya daga cikin 'yan tawagan ya rasa rayuwar shi a wannan hatsari da ya auku a Birnin Abuja.
Majiyar mu tace Wanda ya rasun jami'in Dan sanda ne Mai mukamin sufeta Dan kimanin shekaru Arba'in da biyar (45) Mai suna Ali.
Majiyar mu ta nakalto Mana cewa Hadimin mataimakin shugaban kasan a bangaren yada labarai ya tabbatar da rasuwan inda yace "cikin jimami nake sanar muku da mutuwar daya daga cikin 'Yan Sanda dake cikin ayarin mataimakin shugaban kasa"
Karanta: Kalli yadda wani matashi yayi yunkurin Cakumo Buhari a Argungu
Wannan Hatsari ya auku ne shekaran jiya juma'a 13/03 na shekaran da muke ciki wato 2020 yayin da suke kokarin tafiya filin jirgin saman Nigeria dake Abuja.
Mataimakin shugaban kasan Yana Kan Hanyar Sa ne ta zuwa Birnin Lagos Sai Hatsarin ya faru kafin ya Isa filin jirgin da zai Shiga ya tafi zuwa Lagos din.
Osibanjo ya tabbar da cewa tabbas marigayi Ali Mutumin kwarai ne Wanda Yake aikin Sa tukuru Kamar yadda ake bukata ko wane ma'aikaci ya kasance.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment