Yadda ake dora Audio a Facebook Cikin Sauki




























Tun ba yau ba Na ga wasu daga Cikin abokai na musamman na Facebook suna tambayar yadda zasu Dora audio a Facebook, Har wasu suna cewa "Ko dai ba a iya saka audio ne a Facebook?

Masu wannan tambayar suna da Yawa wanda har wasu sun fara tunanin kila ba a Dora audio a Facebook ne, wannan tunanin tayi tasiri sosai a zukatan wasu daga cikin ma'abota amfani da dandalin sada zumunta na zamani na Facebook.

Ko kasan dalilin da yasa tayi tasiri a zukatan su?
Babban dalilin yin tasirin shine Idan kaje gurin yin posting a Facebook za a baka daman dauko Abu daga Kan computer ko wayar ka Kai tsaye Kuma zaka Dora Shi a Facebook.

Daga cikin Abubuwan da zaka iya daukowa za kaga akwai Hotuna da Videos Amma Kuma babu audio a gurin

Dalilin da yasa suke cewa ba a Dora audio a Facebook kenan Kuma shine babban dalilin da yasa "ba a Dora audio a Facebook tayi tasiri a zukatan wasu"






To wai shin da Gaske ne ba a Dora audio a Facebook?

A'ah ba gaskiya bane a akwai Hanyoyi masu Yawa da a ke bi a Dora audio a Facebook Kuma duk Wanda Yake bukata zai iya saurara idan Kuma yaso zai iya sauke Audion zuwa Kan Computer ko wayar sa.

Ganin cewa ba a iya Dora audio a Facebook Kai tsaye sai an bi wata hanya, Kuma ba kowa ne yasan Wannan Hanyar ba maimakon yayi tambaya kawai don bai iya ba sai yace ba a yi.

Kana neman yadda zaka Dora audio a Facebook?
Baka San yadda zaka Dora audio a Facebook ba?

Toh kwantar da hankalin ka cikin wannan rubutun zaka koyi yadda ake dora Audio a Facebook cikin Sauki Kuma a Kyauta ba tare da ka biya ko sisin Kobo ba.

Menene Amfanin dora Audio a Facebook?

Dora audio a Facebook Yana da matukar muhimmanci Wanda suna da Yawa ba sai na tsaya dogon surutu a Kai ba domin na San Kai ma zaka iya fadan amfanin shi.

Sai dai daga cikin amfanin saka audio a Facebook akwai;

  1. Dora audio a Facebook Yana da saukin Jan Data, ba Kamar Video ba.
  2. A karamin lokaci zaka Dora cikin 'yan dakika kadan
Wadannan sune kadan da Zan iya ambata daga cikin amfanin Dora audio a Facebook.

Ta wace hanya zan Dora audio a Facebook?

Hanyoyin Dora audio a Facebook suna da Yawa domin link zaka hada na audion da kake bukatan dorawa, sai ka Dora link din a Facebook, duk Wanda Yake bukatan sauraro ko saukewa zai bi link din sai yaji ko ya sauke.

Kamar yadda nace hanyoyin Dora audio a Facebook suna da yawa, Hakane sai dai zan yi bayani ne a Kan guda daya Wanda wannan da Zan yi bayani a Kai shine Google Drive.

Duk Wanda Yake da email Address na kamfanin Google (Gmail) wato Mai @gmail.com a karshe shine zai iya amfani da wannan hanyar har ya Dora audio a Facebook.

Yadda zaka mallaki Google Drive a Kan wayar ka

Idan baka dashi kaje Browser na wayar ka ka rubuta "Gmail Sign up" Sai ka bude email Address a gurin, Bayan ka bude ne zaka Samu daman amfani da Google Drive.

Bayan ka bude Email address, Ka duba jerin Applications dake Kan wayar ka za kaga wani Mai suna "Drive" sai ka Shiga


Toh yanzu dai ka mallaki email Address na Gmail, a cikin Google Drive za ka Dora audion sai ka Dauki link din shi ka Dora a Facebook.

Ka Fahimta sai ka dora Audio a Drive kafin ka Dora Shi a Facebook, Yanzu Zan fara nuna maka yadda zaka ajiye audio a Drive din ka.



Karanta: Matakan kariya daga kamuwa da Coronavirus



Yadda zaka Dora audio a Google Drive

Bayan ka mallaki Gmail account ma'ana email Address na kamfanin Google Sai ka Shiga Drive, Nayi bayanin inda zaka Samu Drive a sama kadan.

Idan ka Shiga Drive za kaga alaman Tarawa (+) Sai ka shiga, Za kaga inda a ka rubuta "Upload" Nan zaka Shiga Kuma Nan take zai Kai ka Kan memory na wayar ka sai ka zabi Audion da kake bukatan dorawa a Facebook ka taba Kan shi.

Zai dawo da Kai Drive, sai ka taba alaman refresh Nan take zai karasa Hawa Drive din na ka Kamar yadda zaka gani a hoton dake kasa

Ka tabbatar ka kunna Data domin Dora audio a Google Drive da data Yake amfani,
Yanzu dai ka Dora audion ka a Drive Abu na gaba Shine dorawa a Facebook.

Yadda zaka Dora audio a Facebook ta hanyar amfani da Google Drive.

Bayan ka Dora audio a Google drive Kuma dama kana da bukatan Dora shine a Facebook, zaka copy link na Audion ne a Google Drive sai kayi paste din shi a Facebook shikenan an wuce gurin.

Yadda zaka copy link a Google Drive

Yanzu Kasan yadda ake dora Audio a Google Drive Abu na gaba da zaka koya shine dauko link na audio ko na wani abun daban daga Google Drive.

Don daukan link na Audion da ka ajiye a Drive kabi wadannan matakai;

  • Ka Shiga Drive
  • Kaje Audion da ka Dora, a dab jikin Audion za kaga wani Abu Kamar haka
  • Sai ka taba gurin da Nayi alama, zai nuna maka Abubuwa da Yawa sai ka Shiga Copy Link shikenan sai kaje ka Dora link a Facebook





Duk Wanda yabi link din daga Facebook zai iya sauraro har da saukewa idan ya ga dama.









Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky