Yadda zaka sayi 250mb data a Kan Naira 100 a Layin MTN
Kamar yadda kusan kowa yasan tsare-tsare na sayan data na kamfanin layin waya na MTN, a kullum a na Kara Samun wasu hanyoyin da a ke sayan data cikin Farashi Mai sauki a Layin MTN.
Akwai hanyoyi da dama na sayan data sai dai wani lokacin za samu wani hanyan yafi wani hanyan saukin sayan data.
Layin MTN layi ne na kamfanin kasar Afirka ta kudu Wanda su kayi karfi sosai a Nan gida Nigeria Kai ka ce mallakin Gwamnati ne ko na wani Dan kasuwa a Nigeria
Rubutu Mai Alaka: Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN
Wannan tsari na MTN garabasa ne har Kashi uku a cikin, ma'ana ba 1GB kadai zaka iya saya ba har sama ko kasa da haka zaka iya saya Kuma ka more Datan ka a yanan gizo da duk inda a ke bukatan data kafin a shiga.
Bayan 1GB a Kan Naira 200, zaka iya sayan 250 mb a Kan Naira #100 sai Kuma 4GB a Kan Naira 1000 kacal.
Wannan tsarin sayan data ya taimaka sosai wa mutane da dama musamman masu kananan karfi domin Hawa Internet da social media.
Ba tare da Bata lokaci ko dogon surutu ba Zan tafi Kai tsaye domin nuna maka yadda zaka sayi data Mai sauki a Layin MTN.
Sai dai kuma abun da ya kamata ka Kara Sani a Kai shine ba ko wane bane Yake yi, wasu zababbun layuka ne suke da daman more wannan garabasa Kai ma sai ka jarraba ko za ka dace.
Ko da Yake ba sabon Abu bane ya Dan Dade ana amfani dashi sai dai ba kowa ne ya Sani ba, wannan tsarin Sayan Datan a na mishi lakabi da suna "MTN welcome Back Data).
Mafi Yawan layukan da suke yi sune wadanda a ka Dan ajiye su suka Dan yi kwana biyu ba a Dora su a Kan waya ba.
A farkon fitowan tsarin, sai sim card yayi wata daya a kasa kafin Yake yi Amma a yanzu Dace ne Samun wannan garabasa ba sai layi ya Dade a ajiye ba.
Karanta: Tsarin Kira mafi sauki a layin MTN
Yadda zaka sayi datan welcome Back na MTN
Kamar yadda nace tsari uku ne Kuma Abu kadan ne Yake bambanta su, zamu fara da na farkon.
Yadda zaka sayi 250mb a Kan Naira 100
Idan zaka sayi 250mb dole ne layin ka ya kasance da adadin katin Naira 100 ko sama da haka.
Bayan ka tanadi katin 100 a Layin ka sai ka Danna wadannan Lambobi *131*65*1#
Nan take zasu cire Naira 100 su baka 250mb Wanda zai Dauki tsawon kwana 3 kana mora.
Yadda zaka sayi 1GB data a Kan Naira 200
Shi Kuma wannan sai ka sayi katin Naira 200 a Layin Kan kafin zaka iya sayen shi, zaka sayi 1GB ne a Kan Naira 200.
Wannan data na #200 zai Dauki tsawon sayi daya wato kwanaki bakwai kana amfani dashi kafin zai Kare aiki
Idan zaka Saya ga lambobin da zaka dannan *131*65*2#.
Yadda zaka sayi 4GB a Kan Naira 1000
Tsarin sayan datan welcome back na karshe shine Wanda zaka sayi data 4GB a Kan Naira dubu daya a Layin ka na MTN.
Zaka Dauki kimanin wata guda kana amfani da Datan ka domin kwana talatin Yake yi kafin yayi expire.
Zaka saya ne ta hanyar Danna wadannan Lambobi *131*65*3#
Kafin ka sayi 4GB sai kana da Kati na #1000 a Layin ka.
Wadannan sune tsarin sayan data masu sauki a Layin MTN Wanda zaka more su tun daga Kan na kwan 1,7 har zuwa kwana 30.
Sai dai kar kaanta ba ko wane layin MTN ne yake yi ba sai Wanda yayi Dace ne zai samu daman morewa garabasan.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment