Gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa'i ya kamu da Coronavirus
Gwamnan jahar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i Ya kamu da wannan cuta ta Covid 19 a sanarwan da Yake fitowa yanzu Haka daga gare shi.
Sanarwan ya fito ne daga shafin shi na Facebook cikin video ya baiyana cewa lallai sakamakon gwajin da a ka mishi ya fito Kuma ya nuna Yana dauke da cutar dake sakale numfashin Dan Adam wato Covid 19.
Ya fitar da sanarwan ne a yammacin ranar Asabar 28 ga watan Maris na shekarar 2020 da misalin karfe 8 da rabi na Yamma a shafin shi na Facebook
Karanta: Dalilin da yasa muka Kori Gudaji kazaure Daga APC- Shugabannin jam'iyar APC
![]() |
| Lokacin da Malam Nasir Ahmad El-Rufa'i Yake bayani game da sakamakon gwajin coronavirus da a ka mishi.
A cikin Videon Wanda yakai tsawon kusan Minti daya, El-Rufa'i ya baiyana cewa yanzu Haka an kebe shi domin gabatar da jinya na wannan cuta da ta kama shi.
Zaka iya kallon jawabin da yayi ta wannan Link Shiga Nan
Idan Mai karatu bai manta ba a satin da ya gabata ne Gwamnan Jahar Bauchi shi ma a ka tabbatar ya kamu da cutar Wanda shima a yanzu Haka Yana kebe a asibitin da a ke jinyar coronavirus.
Karanta: Matakan kariya daga kamuwa da Coronavirus
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka. |


Comments
Post a Comment