Dalilin da yasa muka Kori Gudaji kazaure Daga APC Inji jam'iyar APC
An Kori Dan majalisa Honourable Muhammad Gudaji kazaure Daga jam'iyar
APC
Jam'iyar APC ta jahar jigawa ta baiyana dalilin ta na koran fitaccen Dan Majalisan Nan Mai suna Honourable Muhammad Gudaji kazaure Daga jam'iyar.
Jam'iyar ta baiyana hakan ne a wata takadda ta musamman da ta fitar Mai dauke da sa Hannun shugabannin jam'iyar APC na Yankunan da Dan Majalisan Yake wakilta a Jahar jigawa.
Kamar yadda sanarwan ta gabata shugabannin jam'iyar ne suka yanke hukuncin koran shi daga jam'iyar in ji su.
Honourable Muhammad Gudaji kazaure dai shine Dan Majalisa Mai wakiltan wasu kananan hukumomi a jahar jigawa, kananan hukumomin sune kamar haka; Kazaure, Roni, Gwiwa da 'yan kwashi.
Cikin sanarwan, shugabannin jam'iyar sun ce sun Kori Gudaji kazaure Daga APC ne saboda ba ya bin dokoki da ka'idodin jam'iyar.
Mutane da dama sun baiyana Ra'ayin su Kan lamarin yayin da wasu suke ganin fadan cikin Gida ne wasu Kuma sun nuna Rashin Jin dadin su game da dambarwan.
Karanta:
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.


Comments
Post a Comment