Saurari Hira da a kayi da Wanda ake zargin Ya kamu da Covid19 a katsina cikin audio


























An yi Hira Kai tsaye da wani bawan Allah a dutsinma na jihar katsina Wanda a ke zargin Yana da wannan cuta na zamani Mai sarkafe numfashi wato Coronavirus.

Ko da Yake zuwa Yanzu an chanjawa cutan suna daga Coronavirus zuwa Covid-19, tun farkon fitowan cutan a na Mata lakabi ne da sunan Dana ambata a farko Amma daga bisani sai a ka chanja mata suna.



Karanta: Gaskiya ne JAMB tayi cancel na sakamakon jarabawan ta na Bana?



Cutan ta fara bullowa ne daga kasar chana Wanda ta salwantar da rayukan al'umma da dama Wanda har yanzu tana Kai.

Wannan cuta dai a yanzu haka ta yadu a kasashen duniya da dama Wanda a wasu kasashen an Hana duk taron da zai hada Jama'a su cunkushe guri daya ciki har da guraren ibada.

A ci gaba da yaduwa da cutan take yi, yanzu haka ta shigo Nigeria yayin da a ka samu kusan mutane uku da suka kamu a jahar Lagos bayan sun yi mu'amala da wani Dan kasar chana daya shigo Birnin Lagos.

A karon farko a yankin arewascin Nigeria mun Samu labarin wani Mutum da a ke zargin shima ya kamu da ita Bayan dawowan shi gida Nigeria daga wata kasa.



Karanta: Matakan kariya daga kamuwa da Coronavirus



Ko da Yake kasan da ya fito ba a samu ko Mutum daya Wanda ya kamu ba, mutumin da ake zargin Dan Dutsinma ne a cikin jahar katsina.

Wanda ake zargin yace "Bayan na dawo ne sai nake Jin ban ganewa jiki na ba, Sai nayi kokarin zuwa asibiti a ka ja jini na domin yin gwaje-gwaje.

Tun kafin Sakamakon gwajin ya fito sai a ka fara yadawa a gari wai an same Ni da wannan cuta Kuma an kebe ni a wani guri a asibitin"

Mutumin yayi mamaki sosai ganin yadda Jita-jitan ta yadu a ko ina, Ana cikin Hakane sai a ka samu wani Dan jarida yayi Hira dashi.

Zaku ji cikakken Hiran a Audion Nan, Idan kaso zaka iya saukewa ko ka kalla ba tare da ka sauke ba.
Ga audion Nan Hira da Wanda ake zargi Yana da Covid19 a Dutsinma









Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky