Kalli Videon matashin da yayi kokarin Damko Buhari a Argungu





























Mutumin kwatsam sai gashi a Gaban shugaba Buhari da sauri Yana kokarin Mika Hannu domin ya riko Buhari yayin da jami'an tsaron dake gurin suke jan shi domin nesantar dashi daga inda Buharin Yake.

Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ya halarci taron biki na al'adun gargajiya Wanda a ka gabatar a Argungu dake cikin jahar kebbi.

Wannan taro an Saba gabatar dashi ne duk shekara a jahar kebbi sai dai Kuma an Dauki tsawon shekaru goma Sha daya (11) ba tare da an Gabatar dashi ba sai wannan shekaran a ka dawo dashi.

Jaridan Daily Trust ta ruwaito cewa an harbi matashin a kafa a lokacin da ya kutso Kai domin kusantar shugaban kasan na Nigeria



Karanta: Osibanjo ya Sha da kyar a Hatsarin mota a Abuja



Ko da Yake majiyar mu ta tabbatar Mana da cewa daga baya daily trust ta Bada Hakuri, tace lallai ba a Harbi matashin ba sai dai jami'an tsaro sun ja shi zuwa gefe.

Abun da wasu daga cikin jama'an Nigeria kenan suke CeCe kuce a Kai, Wasu na cewa mutumin ya iso har inda Buhari Yake Kuma kadan ya Hana ya taba shi sai jami'an tsaro suka rike shi, toh Bayan sun rike shin ne suka harbe shi?

Kamar yadda zaka gani a Videon, matashin da Saurin shi ya iso har inda shigaba Buhari yake Yana kokarin Mika Hannu Sai mutanen dake gurin suka ankara su kayi kokarin rike shi da Jan shi baya

Wasu mutannen suna ganin wannan a matsayin masoyin Buhari ne Wanda yazo gurin ne kawai domin ya gaisa dashi Hannu da hannu.

Wasu Kuma suna ganin wai mutumin yazo ne domin ya cutar da Buhari Wanda Kuma a wannan lokacin babu komai a jiki ko Hanun shi na cutarwa.

Ko da Yake fadan shugaban kasa ta tabbatar da cewa mutumin masoyin Buhari ne kuma ya zo ne domin su gaisa da shugaba Buhari Amna sai wasu suka juyar da labarin

An ruwaito cewa daga cikin jawabin Shugaba Buhari a gurin taron yace Tsawon shekaru 11 kenan rabon da a yi wannan bikin, tabbas tsaro ya samu tunda a ka ci gaba dayi a wannan shekara ta 2020.

Ganin cewa Videon Yana kunshe da duk jawaban har ma da yadda wani matashi ya nufi Kan Buhari da sauri kafin ya cafkoshi jami'an tsaro suka rike shi.


Ga Link na Videon, Shiga ka gani Videon matashin da ya tinkari Buhari a Argungu









Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky