Yadda zaka samu data 100mb da kyautan Kira na minti 12 akan Naira 100 a Layin MTN

























Yadda zaka sayi 100mb a Kan #100 da kyautan minti 12 na Kira a layin MTN


A wannan lokaci na zaman Gida, kamfanin sadarwan layin waya na MTN suna fitowa da sabbin tsare-tsare Masu Sauki na sayan data Wanda duk Wanda Yake bibiyan shafukan su na Yanan Gizo zai tabbatar da hakan


Ko da yake ba a shafukan su na Yanan Gizo kadai suke sanar da ire-iren sabbin garabasa da suke sakewa ba, Hatta sakon Kar ta kwana (text message) suna turawa wasu daga cikin Masu mu'alama dasu kamar yadda wata Kila zaka iya gani a cikin wannan rubutun idan mun samu daman dorawa




Karanta: Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN




A cikin garabasa da suka bayar Kuma yanzu sun Bada daman za a iya sayan 100mb data a Kan Naira 100 kacal, ba wannan kadai ba zasu baka kyautan Minti 10 ka Kira duk Wanda kake so da layin Bayan ka sayi wannan data


Kenan dai garabasa har guda biyu ka samu a wannan tsari, Bayan ka sayi 100mb a Kan Naira 100 zaka iya Kiran waya na tsawon Minti 12


Ba tare Dana cika ka da surutu ba yanzu Zan nuna maka yadda zaka sayi data 100mb a Kan Naira dari Kuma ka samu daman Kiran waya na tsawon min Sha biyu (12) a Layin ka na MTN.


Ko da yake MTN Suna da wani Abu guda daya, wannan abun kuwa shine wasu lokutan suna bada garabasa Amma kuma sai ka samu ba ko wane layi bane ya keyi, wani lokacin Kuma ko wane layi Yana iya cin moriyan garabasan su.


Sai ka gwada idan Allah yasa da rabon Kan sai ka kasance cikin Wadanda suke da daman samun wannan garabasa, idan Kuma baka samu wannan ba kaci gaba da kasancewa da asagist tabbas wata rana zaka samu Wanda Yafi wannan Sauki domin zamu ci gaba da kawo muku Tsaruka Masu Sauki na Layukan sadarwa da muke amfani dasu a Nigeria.





Karanta: Tsarin Kira mafi sauki a layin MTN


Yadda zaka sayi 100mb a Kan #100 da kyautan minti 12 na Kira


Don samun wannan garabasa ba wata doguwar hanya ake bi ba don Sauki gare shi kawai lambobin sayan zaka dannan Nan take zai baka daman Saya


Idan zaka Saya ka tabbata kudin dake layin ka na MTN ya Kai Naira 100, daga Nan sainka danna wadannan lambobi *567*121#



Karanta: Hanyoyi 5 da zaka samu kudi a Internet



A Nan muka kawo karshen wannan bayani na sayan data cikin Sauki a Layin MTN da fatan za a ci gaba da kasancewa damu don sanin Hanyoyin sayan data Masu Sauki a Layin MTN, Airtel, Glo, Etisalat da sauran Layukan sadarwan zamani da ake amfani dasu.













Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky