Npower; Sanarwa Mai muhimmanci zuwa ga 'yan Npower Tech
Npower ta fitar da sanarwa na musamman zuwa ga wadanda suke yin Npower bangaren Na'ura Mai kwakwalwa Wanda a ke Kira da Npower Tech.
Shi dai Npower ya kasu Bangare-Bangare ne Wanda a ka rarraba shi kashi-kashi, kuma ko wane bangare Yana da adadi Mai Yawa na masu yin shi.
Daga cikin bangarorin akwai;
*. wadanda suke koyarwa a makarantu
*. Masu aikin asibiti
*. Bangaren sana'o'i Kamar koyar da aikin kafinta, plumbing da sauran su
*. Bangaren koyar da ilimin Na'ura Mai kwakwalwa.
Yanzu haka Hukumar tsare-tsare na Npower tayi sanarwa na Musamman zuwa ga masu cin moriyan Shirin Npower a Nigeria a cikin shafin su na Facebook.
Karanta: Yadda zaka duba result din ka na jamb
Npower sun fitar da sanarwan ne yau Litinin 16/03/2020 Wanda suka ja Hankalin wadanda suke cin gajiyar Npower bangaren Computer wato Npower Tech.
npower ta fara ne da cewa "Sanarwa Mai muhimmanci gare ku cikin wannan hoto dake kasa. Kuyi subscribe kafin Ranar 31/03/2020"
Sai suka bayar da link na wani Channel na YouTube Wanda a ka kawata shi da Darussa da dama Wanda ya shafi koyon Ilimin Computer.
Sun bayar da link na wannan channel ne domin wadanda suke Npower tech su ziyarta su Kuma Kara gogewa a harkan computer.
Akwai abubuwan amfanarwa masu Yawan Gaske a ciki, videos ne masu kyau da inganci Wanda Suke koyarwa Kuma idan kana bibiyan channel din tabbas zaka samu Karin ilimi Mai yawa fiye da tunanin ka.
Ba su kadai har Wanda baya Npower Tech idan ya je zai koyi Abubuwan da ba a ko Ina ne zai same su ba, ya kamata ka duba channel din zaka samu ilimi.
Ga link na channel da suka bayar Npower Tech Subscribe channel.
A wancan hoton da suka bayar sun Kara da cewa duk Dan Npower Tech da bai yi susbcribe na channel din ba zai iya Samun matsalar.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.


Comments
Post a Comment