Da Gaske ne JAMB tayi Cancel sakamakon jarabawan da a ka rubuta ranar Asabar?

























Ko Gaskiya ne Hukumar JAMB ta kasa tayi Cancel na sakamakon jarabawan da a ka rubuta ranar asabar, litinin da Talata?

Idan Mai karatu bai manta ba an fara rubuta jarabawar JAMB ne na 2020 a ranar asabar 14/03/2020 Wanda har sakamakon ya fito Kuma ya zuwa yanzu dai kusan idan Akwai wadanda basu duba nasu ba to tabbas sune su kafi kadan.

Kamar yadda wata Kila Kai ma kaji labarin, Jita-jita Yana yawo Wanda Yake nuni da cewa Hukumar JAMB ta kasa tayi watsi da sakamakon jarabawan da a ka zana a  ranar asabar, Litinin da Talata.



Karanta: JAMB ta Dakatar da duba result ta portal din ta, ta Bada sabuwan hanyar dubawa



Wannan Jita-jitan ya biyo ne Bayan hukumar ta fitar da sakamakon jarabawar Wanda adadi masu Yawa na wadanda suka zana jarabawar tuni suka duba sakamakon su.

Bayan yaduwan wannan labari ne sai Hukumar JAMB ta fito tayi bayani Kuma ta tabbatar da gaskiyan lamari game da wannan labari da a ke yadawa a tsakanin al'umma.

Hukumar ta JAMB tace "JAMB bata kashe sakamakon wannan jarabawa da a ka rubuta ranar 14, 16 da 17 ga watan uku na shekaran 2020 wato ranar asabar, Litinin da Talata.

Don haka wadanda su kayi jarabawar JAMB su yi watsi da wannan Batu domin karya ce kuka Babu wata magana Mai kama da wannan."

Hukumar ta JAMB ta wallafa bayanin ne a sahihin shafin ta na dandalin sada zumunta na Facebook, inda ta baiyana cewa wannan zance ba shi da tushe balle makama.











Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky