Coronavirus: Hukumar zana jarabawar JAMB ta Dakatar da zuwa Ofishin ta saboda Coronavirus
























Hukumar zana jarabawar sharan fage na Shiga makarantun gaba da sakandare JAMB ta Dakatar da zuwa afishin ta a fadin Nigeria saboda gudun yaduwan cutar coronavirus Wanda a ka chanjawa suna zuwa Covid-19

Hukumar ta Bada sanarwan ne bayan Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin rufe makarantun fadin kasar na tsawon wata daya saboda tsoron kar cutan ta yawaita a kasan Baki daya.

Hukumar ta Bada sanarwan ne ta bakin Mai magana da Yawun hukumar a kafofin sada zumunta na zamani Mr Fabian a ranar Talata a Birnin tarayya Abuja.






Ga abunda Yake cewa; "Muna sanar da wadanda suka rubuta jarabawar JAMB na Bana da sauran jama'a, saboda shawarwarin masana da gudun yaduwan cutar Covid 19 mun Dakatar da wasu ayyukan mu na Dan wani lokaci."



Dakatarwan ya shafi duk office na JAMB dake Nigeria saboda gudun cunkoson jama'a a guri daya, Bayan komai ya daidaita zamu koma Aiki ba tare da Bata lokaci ba.

Yaci gaba da cewa Hukumar ta Kara inganta shafin ta na yanan Gizo Wanda duk Mai korafi Yana da daman yi

Duk Mai korafi ko neman Karin bayani zai iya yi a portal na JAMB a support.jamb.gov.ng

Akwai wasu Abubuwan da zaku iya yi idan Kun Shiga portal na JAMB Wanda gashi Nan kamar haka www.jamb.gov.ng Haka ma ta profile din ku.




Sannan Kuma hukumar ta Dakatar da bincike (biometric verification) har sai zuwa lokacin da ta sake sanarwa a Kai

Zaka iya yin Abubuwa da dama ta shafin JAMB na yanan Gizo (JAMB portal), Idan baka iya ba kayi kokarin neman Wanda kasan ya iya ya koya maka kar a Yi want abun baka Sani ba, wannan shawara ce daga gare Ni.














Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky