JAMB ta Dakatar da duba result ta website, Ta sanar da sabon Hanyan dubawa
JAMB ta sanar da sabon Hanyar duba result ga wadanda suka rubuta jarabawa ranar Litinin.
Hukumar JAMB ta sanar da cewa a yanzu haka ta fito da wata sabuwar Hanya da za a duba result saboda matsalar da portal din ta Yake fiskanta a daidai wannan lokaci.
Idan baku manta ba ranar asabar 14/03/2020 ne a ka fara rubuta jarabawar JAMB Kuma sakamakon ya fara fitowa har wasu sun duba nasu Bayan kwana biyu da rubuta jarabawar.
Tun farko hukumar ta Bada sanarwan cewa wadanda suka rubuta jarabawa ranar asabar su duba sakamakon a portal na JAMB ranar Litinin, Bayan kwana biyu da rubuta jarabawar su kenan.
Bayan an yi wannan sanarwan ne mutane da dama sun duba Kuma sun kalli sakamakon na su sai dai kuma a yau ranar laraba 18/03/2020 Hukumar JAMB tace Wadanda suka rubuta jarabawa daga ranar litinin kar su duba ta website saboda barazanar masu kutse a portal na JAMB din.
Mai tallafawa Hukuman ta bangaren yada labarai Dr. Fabian Benjamin yace Mun Dakatar da duba sakamakon jarabawa ta shafin mu na yanan Gizo (JAMB portal) Saboda mun lura da akwai masu kutse wadanda suke kokarin lalata sakamakon jarabawar JAMB ta bana.
"Sakamakon jarabawar wadanda suka rubuta ranar Litinin ya fito Kuma za a duba ne ta hanyar tura sakon kar ta kwana ta lamban wayar da a kayi rijistan JAMB dashi".
Ya ci gaba da cewa "kar ku duba sakamakon ku ta Yanan Gizo (Portal /website na Jamb) saboda an Dakatar da dubawan, Hakan Kuma ya biyo Bayan Hari da a ka kawo wa portal din ne"
"Hukumar tana Nan tana bincike domin zakulo wadanda su kayi kokarin yin wannan aika-aika don su fiskanci Hukunci Inji" Dr. Fabian.
Sannan Kuma yayi Martani game da wadanda suke cewa JAMB ta tura su guri Mai nisa daga Inda suke domin rubuta jarabawa yayin da Yake cewa "Jamb Bata tura Mutum inda taga dama haka kawai.
Kowa shi yake zaban garin da zai rubuta jarabawa, Idan guraren rubuta jarabawa na wannan garin suka cika sai a tura shi center mafi kusa da garin da ya cika don rubuta jarabawar shi.
Yadda zaka duba result din ka na JAMB
Hanyar da Hukumar JAMB ta fito dashi na duba sakamakon jarabawa, ana tura sakon kar ta kwana ne ta lamban wayar da a kayi rijistan jamb dashi.
Don ganin Yadda zaka duba sakamakon ka na JAMB ka bi wadannan matakai;
Ka tura 'RESULT' Zuwa Wadannan lambobi 55019
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment