Sauke Application na zana jarabawar JAMB da waya ko computer (Practice App)
Application nayin jarabawar JAMB da waya ko computer
Cikin wannan rubutu Zan yi bayani ne game da wani Application Wanda a ke yin jarabawar JAMB dashi, Akwai na computer akwai Kuma Wanda za ka iya amfani dashi a waya.
Kamar yadda wata kila ka Sani a shekarun baya a na rubuta jarabawar JAMB ne da pepper da pencil, bayan an kammala rubuta jarabawar sai wadanda suke lura da rubuta jarabawar su tafi dashi su Kai a yi marking bayan wani lokaci sai a fito musu da Sakamakon jarabawar su.
Bayan daukan lokaci Mai tsayi a na wannan wahala ta rubuta jarabawar da pencil da pepper sai a ka samu ci gaba na fasahan zamani a ka fara rubutawa da Computer.
Ana amfani ne da software don gudanar da jarabawar, da Yake da computer a ke amfani don gudanar da jarabawar a yanzu.
Karanta: JAMB ta Dakatar da duba result ta website din ta, ta Bada sabuwan hanyar duba sakamako
An samar da software da dama da a ke amfani dashi don gwada rubuta jarabawar (JAMB UTME practice software) sai daga baya a ka samar da Manhajojin waya (JAMB UTME practice App) Wanda duk dai aikin su daya da na computer.
An samar dasu ne a ka yadawa duniya domin masu sha'awan rubuta jarabawar JAMB su Rika gwadawa (practice), duk Wanda ya gwada amfani dashi zai bambanta da Wanda bai taba amfani dashi ba a gurin rubuta jarabawar.
Dalili na kuwa a Nan shine, duk Wanda bai Saba da amfani da computer ba sai a ranar rubuta jarabawar tabbas hakan zai iya kawo mishi Cikas.
A wannan Application ko software akwai Questions na JAMB a ciki Kuma duk wadanda a kayi sune a shekarun baya, idan ka Saba amfani da Application ko software na CBT Exam ko a gurin zana jarabawar baza ka wahala sosai ba don ka Saba amsa tambayoyin tun kafin lokacin exam.
Yadda zaka sauke CBT practice App/Software
Kamar yadda na baiyana tun farko akwai Application Wanda shi na waya ne, sannan Kuma akwai software Wanda shi kuma da computer ake aiki dashi.
Karanta: Gaskiya ne JAMB tayi cancel na sakamakon jarabawan ta na Bana?
- Idan da waya kake Amfani ga link da za kabi ka sauke don ka fara gwadawa saboda Shirin rubuta jarabawar JAMB Mai zuwa Application na rubuta jarabawar JAMB CBT
- Idan Kuma da Computer kake aiki sai ka sauke wannan don shine na computer Software na rubuta jarabawar JAMB UTME
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.


Comments
Post a Comment