Tsarin Kira mafi sauki na Layin Glo (Glo Tariff plan) a 2020
Tariff plan mafi Saukin Kira a layin Glo Glo daya ne daga cikin layin waya na sadarwa Wanda ake amfani dashi a wannan kasa ta Nigeria Kamar yadda wata kila ka sani Glo layi ne Wanda yayi kaurin suna a bayar da data, duk ma'abocin yanan gizo zai yi wahala kaga bai mallaki layin Glo ba saboda yadda suke Bada data kamar ba gobe. Wannan ne babban dalilin da yasa Zan gabatar da wannan rubutu don baiyana muku tsare-tsaren da Glo suka fitar kuka suke amfani dashi bisa ga tsarin su. Zan yi bayanin Yadda tsarin Glo yake (Glo Tariff plan) da Kuma yadda ake shiga ko wane tsari, duk tsarin Glo a na iya amfani da su a wayar Android, Tablet, Laptop da sauran makarantan su. Idan kana so kasan tsari masu sauki Na Glo ka karanta wannan rubutu domin har yadda ake shiga ko wane tsari duk nayi bayani a ciki. Yadda saka kaura zuwa wani tsari a layin Glo Kaura daga tsarin da kake zuwa wani tsarin a layin Glo yana da matukar sauki ba abu bane Wanda sai ka...