Yadda zaka samu kudi a Facebook
Hanyoyin samun kudi a Facebook
Barka da zuwa wannan shafi mai albarka, Cikin taimakon Allah, yau kuma zan kawo muku wasu hanyoyi ne masu muhimmanci wadanda zaku samu kudi a Facebook
Tambayoyi suna ta yawo a dandalin sada zumunta na zamuni musamman Facebook kamar haka; 'Ta wace Hanya ake samun kudi a Facebook?
Ta yaya zan samu kudi a Facebook?'
Duk da dai tambayar daya ce sai dai kawai sigan ce take zuwa da bambanci, kowa da irin yanayin da zai yi ta shi tambayar.
To ko ma dai yaya ne cikin wannan rubutu zan yi maka bayanin yadda ake samun kudi da Facebook ta wasu hanyoyi daban-daban.
Kullum sai ka sayi data ka hau Facebook kuma duk lokacin da ba kada data hankalin ka baya kwanciya har sai ka nemi kudi ka sayi datan.
Kudin ka yana karewa a gurin sayan data don ka hau Facebook, ko ka taba tunanin ta wace hanya zaka samu kudi da Facebook?
Tabbas ana samun kudi da Facebook sai dai kila kai baka San ta wace hanya zaka samu kudi a Facebook ba.
Baka san Yadda zaka samu kudi da Facebook ba?
Ah to ai kar ka daga hankalin ka ba gani ba?
Zan nuna maka wasu daga cikin hanyoyin da zaka samu kudi da Facebook din ka.
Wanene zai iya samun kudi a Facebook?
Eh Kowa zai iya samun kudi da Facebook kamar yadda kowa ne zai iya amfani da Facebook.
Ka sani cewa akwai 'yan damfara da yawa a Facebook kar ka kasance cikin su matukar kana bukatan Neman kudi da Facebook.
Idan ka kasance mayaudari baza ka kulla komai ba saboda mutane zasu gane ka kuma zasu kafa maka kahon zuka.
Ka kasance mai gaskiya a lamarin ka za kaga yadda mutane zasu yi ta turuwa a kan ka kai kuma kana samun kudin ka.
Ka saka hoton ka a profile picture na Facebook din ka tanan ne mutane zasu gamsu cewa kai mutum ne kuma ba Dan damfara ba.
Ya danganci yadda kake son Neman kudin ka ya kasance .
Idan kaso zaka iya bude wani account na Facebook musamman ya zama na kasuwancin ka.
Idan kaga dama kuma za a iya yi a account daya, ya danganci dai yadda kake Bukata.
Wane irin kasuwanci zaka iya yi a Facebook?
Akwai abubuwa da dama wadanda zaka iya tallatawa kuma ka sayar dasu a Facebook, sai dai kuma akwai wadanda Facebook basa bari a tallata a Facebook.
A takaice dai duk wani kasuwancin yake iya kawancewa bai da kyau Facebook basa bukatan shi.
Daga cikin abubuwan da Facebook suke hana kasuwancin su a Facebook akwai wadannan;
- Giya da sauran kayan maye
- Taba (Sigari)
- Dabbobi
- Wasu Abubuwan da suka shafi kiwon lafiya, Da sauran su.
Yaya ake samun kudi a Facebook?
Kamar yadda na fada a sama hanyoyin samun kudi a Facebook suna da yawa ba zai yiwu a ce zamu ambace su duka ba, sai dai zan ambaci wasu daga cikin.
- Rubutu a Facebook
Daga cikin hanyoyi mafi shahara na Neman kudi a Facebook akwai rubutu a kan abunnda zaka sayar gami da hadawa da hotunan abun da kake da bukatan sayarwa.
Yadda wannan tsarin yake shine, Idan ka samu abunda kake son sayarwa sai ka hau Facebook kaje gurin da a keyin posting, kayi rubutu na tallata abun da zaka sayar din sai ka saka hotunan shi sannan ka tura shi a Facebook
Bayan ka Dora duk Wanda ya gani kuma yana so zai yi maka magana.
Ta wannan hanya mutane da dama sun yi kudi kai ma kar ka tsaya tunanin wai me zaka sayar?
Kai dai kayi tunanin meye ne mutane suke bukata.
Bayan kun yi ciniki kun daidaita Wanda ya saya idan yaga dama zai iya aikowa har inda kake ya karba ko kuma ka tura mishi zuwa inda yake.
- Shiga Group na saye da sayarwa
Akwai group da dama a Facebook wadanda a ka Gina su don saye da sayarwa.
Duk Wanda yake da kayan sayarwa zai Dora ne a group din da haka za a samu mai saya Ku daidaita har a turo maka kudi kai kuma ka tura kaya.
Don shiga irin wannan group kaje gurin bincike a Facebook (Searching) ka rubuta 'Buy and sale Groups' ka shiga wadanda kake kusa dasu.
- Neman Aiki
Akwai wata hanyar itama ta Neman kudi a Facebook wayo ta Neman aiki.
Ga yadda tsarin yake.
Idan kana yawan hawa Facebook wani lokaci za kaga kamar page ne a botun din za kaga an rubuta 'job' Idan ka taba kai zai kai ka har Inda zaka cika application idan ka dace sai ka zama ma'aikacin wata ma'aikata ta online zaka musu aiki su biya ka.
Sai dai akwai 'yan damfara da suke amfani da irin wannan dama dole ne sai ka kiyaye ba ko wanne zaka rika shiga ba kuma ko da ka shiga kayi taka tsan-tsan da abun da zaka rubuta a wajen cika form din.
A nan zan dakata, kamar yadda na fada tun farko Hanyoyin samun kudi suna da yawa a Facebook.
Idan ka kasance damu nan gaba kadan zamu iya kawo Karin wasu Hanyoyin.
Kayi Share

Comments
Post a Comment