Arewa Bloggers tayi Babban Rashi, Yusuf Salisu Blogging
Inna lillahi wa Inna ilaihi Raji'un
Tabbas arewa ko Kuma nace Hausa bloggers ta yi Rashin babban jigo Kuma mutumin kirki Wanda kafin ya rasu dalibi ne a jami'ag mallakan gwamnatin tarayya dake kashere karamar Hukumar Akko a jahar Gomben Nigeria.
Matashi ne Mai wankakkiyar zuciya Wanda zai yi wahala kaji yana cacan baki da wani bare fada, Ni dai tsawon abotan mu dashi ban San wani abokin fadan shi ba.
Wannan bawan Allah da ya rasu sunan da yake amfani dashi a Facebook shine Yusuf Salisu Blogging amma cikakken sunan shi shine Yusuf Salisu Muhammad.
Yusuf Dan Asalin jahar plateau ne a Yankin arewa Maso gabashin Nigeria, Yayi suna sosai a harkan Blogging Kuma Yana daga cikin wadanda basu da Mugunta domin idan kayi mishi tambaya Nan take zai baka amsa ba tare da kyashi ba.
Kusan duk Wanda yake abota dashi a Facebook yasan da wannan Kuma Muna rokon Allah ya jaddada Rahama a gare shi.
Kamar yadda na fara baku takaitaccen tarihin shi a sama, lallai Dan jahar plateau ne a Yankin shen a yelwa kenan Kuma Yana karatun shi na digiri a jami'ar Dana fada a sama.
Ya samu admission din ne a shekaran da ta gabata wato 2019/2020 yanzu haka dai Ina ga yana dab da kammala aji daya kenan, Yusuf Yana karantan Ilimin addinin musulunci ne (Islamic studies).
Na tuna wani rana da ya baiyana Mana cewa ya samu admission a jami'an kashere muka taya shi murna da fatan idan ya taho zamu hadu da juna da yake Nima Ina kusa da kashere ne.
Bayan ya kusa tafiya makaranta sai ya baiyana Mana cewa lallai yanzu kam ya ajiye blogging har sai bayan ya kammala karatu, dama Kuma haka abun yake karatu bai cika haduwa da wasu sabgogin ba.
Yusuf Salisu Blogging shine mawallafin shafin yanan gizo na Yelwaexpress.com akwai bayanai masu muhimmanci a shafin Wanda ya kunshi fasaha, a yanzu dai Babu abun da yake bukata Kamar adu'a.
Akwai Group din shi da ya bude a watsapp Mai suna Yelwaexpress.com duk dai don taimakawa al'umma, Yanzu baya Nan Kuma ya tafi kenan.
Irin wannan mutuwar Akwai shiga jiki domin nayi magana da daya daga cikin abokin shi na makaranta ya shaida min cewa Rashin lafiya ne ya kama shi lokaci daya sai rasuwa.
sannan Kuma Akwai Wanda ya baiyana cewa jiya lahadi 23/02/2020 sun yi sallar isha kenan sai ya fadi Nan take suka dauke shi suka Kai shi asibiti ba a dauki wani lokaci Mai tsayi ba Allah Yayi mishi cikawa.
Insha Allahu yayi kyakkyawan karshe domin yayi sallah kenan Allah ya karbi rayuwar shi, wata rana Kai ma haka za ji labarin mutuwar ka.
Tun da ya Rasu, Zan yi amfani da wannan dama domin na roki musamman abokan shi na Facebook dasu yafe mishi domin zo mu zauna zo mu Saba ne, dole wata rana za a iya sabawa juna.
Muna rokon Allah yajikan Yusuf da Rahama
Ya Allah ka haskaka kabarin shi
Ya Allah kasa Aljannar firdausi ce makomar shi
Ya Allah mu Kuma da muke Raye kasa muyi kyakkyawan karshe.

Allah yaji kasa
ReplyDeleteAmin ya Hayyu Ya Qayyum
Delete