Tsarin Kira mafi sauki na Layin Glo (Glo Tariff plan) a 2020
![]() |
| Tariff plan mafi Saukin Kira a layin Glo |
Glo daya ne daga cikin layin waya na sadarwa Wanda ake amfani dashi a wannan kasa ta Nigeria
Kamar yadda wata kila ka sani Glo layi ne Wanda yayi kaurin suna a bayar da data, duk ma'abocin yanan gizo zai yi wahala kaga bai mallaki layin Glo ba saboda yadda suke Bada data kamar ba gobe.
Wannan ne babban dalilin da yasa Zan gabatar da wannan rubutu don baiyana muku tsare-tsaren da Glo suka fitar kuka suke amfani dashi bisa ga tsarin su.
Zan yi bayanin Yadda tsarin Glo yake (Glo Tariff plan) da Kuma yadda ake shiga ko wane tsari, duk tsarin Glo a na iya amfani da su a wayar Android, Tablet, Laptop da sauran makarantan su.
Idan kana so kasan tsari masu sauki Na Glo ka karanta wannan rubutu domin har yadda ake shiga ko wane tsari duk nayi bayani a ciki.
Yadda saka kaura zuwa wani tsari a layin Glo
Kaura daga tsarin da kake zuwa wani tsarin a layin Glo yana da matukar sauki ba abu bane Wanda sai ka hada zufa ko ka nemi wani ya maka, a'ah Kai da Kan ka zaka iya yin kayan ka
Idan ka shirya kaura daga tsarin da yanzu haka kake amfani dashi zuwa wani tsari Mai sauki ga yadda za kayi
- Layin ka na Glo ya kasance a kan waya
- Ka Danna *777#
- Sai ka zabi tsarin da kake so (Glo Tariff plan)
- Nan take zaka gan ka a tsarin da ka zaba
Tsarukan Glo Masu sauki
Prepaid plan
Tsarin Kira a wannan tsari shine kamar haka, a ko wane dakika daya suna cire Kobo 11 ne Kuma ko wane zaka Kira ba chanji.
Bayan wannan saukin Kuma Akwai wani garabasa na bayar da daman kiran wasu kasashen waje guda talatin a Kan Kobo 11 a duk dakika (Second).
Daga cikin kasashen waje talatin da zaka iya Kira a wannan tsarin Akwai koriya ta kudu, chana, Canada, Japan, Mexico, Isra'ila, India, Afirka ta kudu da sauran su.
Sai dai Kuma a ko wane rana zasu na cire Naira 5 ko kayi Kira ko ba kayi ba, da wannan nake baka shawara kaci gaba da amfani dashi a kullum saboda kar kayi asara.
Yadda zaka koma tsarin Glo na prepaid plan
Kaura zuwa tsarin Glo na Kira a Kan Kobo 11 duk sakan daya abu ne Mai sauki, Danna *211# ba tare da bata lokaci ba zaka tsinci Kan ka a wannan tsari Mai cike da sauki.
Sai dai tsarin a kullum suna cire Naira 5 a Kiran da za kayi na farko
Idan ka koma tsarin Glo prepaid za kayi amfani da yanan gizo Kyauta na tsawon minti goma a ko wane rana na tsawon wata daya idan kullum kake amfani da layin kenan Kuma datan tsawon kwana 7 yake yi kafin wa'adin shi ya kare
Tsarin Glo na jollific8
A tsarin suna nin ka kudin da a kasa har sai takwas, misali idan kasa katin Naira 100 toh zasu baka Kudi har Naira 800, ya kaga tsarin ya hadu ko?
Sabon layin da a ka sa shi a tsarin Glo na jollific8 suna Bada kyautan data da Kuma Kira don jin dadin ma'abota amfani da Tsarin.
Ga bayanin Yadda tsarin Glo jollific8 Yake
- Idan kasa Naira 100 zasu baka Naira 800 da kyautan data (10mb.
- Idan kasa katin Naira 200 zasu baka Naira 1600 hade da data (25mb).
Wannan kenan a takaice haka Kuma ko nawa kasa zadu ninninka maka su hada maka da Datan Hawa yanan gizo.
Yaya ake komawa Tsarin Glo na jollific8?
Don morewa garabasan jollific8 abunda kawai za kayi shine sayan sabon layin Glo kayi rijista, idan ya hau Kan waya toh dama zaka same shine a wannan tsarin Sai ka dannan *123*lambobinkati# shikenan sai kaci gaba da morewar ka.
Sai dai ka sani sabon layi ne kadai yake yi yauwa kar ka kadewa tsoho kura kace Kai ma da Kai ciki, idan kana bukata sayi sabon layi.
Tsarin Glo G-Bam
Ba wannan kadai ba a kullum suna bayar da kyautan data megabite biyar (5mb) don Hawa yanan gizo, duba sakonnin imel da dai sauran su.
Wannan tsarin an kirkire shine saboda mazauna kasar Nigeria don amfani da yanan gizo a kullum ko da basu da ko sisi.
Yadda zaka koma tsarin Glo G-Bam
Don komawa Glo G-BAM cikin sauki Danna *100*5*1# kaci gaba da more sauki, bayan Hawa shafukan sada zumunta kamar Facebook har Instagram da watsapp zaka iya da wannan Datan kyauta da suke bayarwa
Tsarin Glo Infinito
Wannan tsarin Babu wani boyayyen Kudi da suke ja a rana kenan ba kamar wancan da nayi bayani a sama ba Wanda suke cire Naira biyar a ko wane rana ko kayi Kira ko baka yi ba, wannan ba haka yake ba.
A tsarin cire Kudi na Glo Infinito suna cire Naira 20 ne a ko wane dakika (second) da a kayi a na Kira (20k/S), ko wane layi a haka ake Kira.
Karanta:
Yadda zaka koma tsarin Glo Infinito
Zaka koma tsarin Glo Infinito ne ta hanyar dannan wadannan lambobi *1002# don samun wannan garabasa.
Sannan Kuma zaka iya saka lambobin family and Friends guda goma ta hanyar Danna wadannan lambobi 101*1*Lamban Waya#, zaka Kira family and friends a Kan Kobo 11 duk dakika.
A Nan Zan dakata Insha Allahu zamu ci gaba da kawo muku sauran Tsaruka masu sauki wadanda bamu baiyana su ba a yanzu.
Kai dai kaci gaba da kasancewa da shafin Nan don samun rubuce-tubuce masu amfanarwa.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Kayi Share

Comments
Post a Comment