Hanyoyi 5 da zaka samu kudi a Internet














Hanyoyi 5 da zaka samu kudi a Internet

Mutane da dama suna yawan tambayar cewa wai ta wace Hanya ne zasu samu kudi a yanan gizo, Online, Internet ko kuma a hausance wato yanan gizo?

Duk dai ana nufin abu daya ne sai dai kawai sigogin tambayar ne suke bambanta kamar yadda kake gani a sama, kana daya daga cikin masu irin wannan tambaya ta hanyoyin samun kudi a yanan Gizo?

Nasan amsar ka baza ta wuce 'eh' ba domin da baka cikin su baza ka fara karanta wannan rubutu ba, toh ina maka albishir domin na tabo inda yake maka kaikayi ne kuma zan fede biri har wutsiya a kan batun yadda ake samun kudi a internet.

Baka taba samun kudi ta yanan gizo ba kuma kullum kana online?

Ta yiwu kai mai karamin karfi ne kila ma wani lokacin baka hawa online saboda rashin kudi, ta yiwu wani lokacin  kana free mode ne a Facebook, Hakane?

Tabbas kasancewa cikin irin wannan yanayi baida dadi, zan share maka hawaye yanzun nan bayan ka kammala karantawa kuma zaka tsaya da kafafun ka idan Kabi matakai da zan zaiyana idan Allah yaso.

A wannan rubutu zan baiyana hanyoyi daban-daban wadanda zaka samu kudi dasu, duk wanda ka dauka a cikin su zaka samu makodan kudi dashi.

Hanyoyin samun kudi a Internet

Ba tare da bata lokaci ba ga wasu daga cikin hanyoyin da ake samun kudi a online:

1. Sayar da kayan wasu (Affliate marketing):

Zaka iya sayar da kayan wasu a matsayin ka na sabon shiga a harkar neman kudi a internet, ko da yake hatta wadanda suka dade a harkar yanan gizo suna wannan kasuwanci saboda ana samun riba dashi fiye da yadda kake tsammani.

Yadda tsarin yake shine zaka fara sayar da kayan mutane ne a yanan gizo, bayan ka sayar kai kuma zasu baka kaso ma'ana ladan sayar musu da kaya kenan, zamu iya cewa ka fito a dillali kenan ko?

Wannan hanya ce mai kawo kudi a online sai dai abunda ake bukata shine kayi bincike kuma ka koyi yadda ake kasuwancin, ka rika bincika saboda ta yiwu a bullo da wata sabuwar hanya wanda ba bincika kayi ba sai a yi babu kai.

Da wannan kasuwancin akwai masu samun sama da dala 400 duk wata wanda idan ka kwatanta shi da Naira ba karamin kudi bane.

Daga cikin shafukan yanan gizo da zaka iya fara wannan kasuwancin akwai amazon affliate programming, jumia,  konga, Aliexpress da sauran su.

Akwai hanyoyi da yawa da zaka fara kasuwancin affliate kuma zaka iya farawa ba tare da ka kashe ko Naira ba, kai dai abun da ya dace da kai shine kayi binciken yadda zaka fara affliate marketing da daya daga cikin website da na lissafa maka a sama.

2. Yin Logo:

Idan ka iya hada logo masu kyau tabbas zaka samu kudi masu yawa idan ka mayar dashi kasuwanci ko sana'a

Duk kasuwancin da a keyi tun daga kan na yanan gizo har wanda a keyi a nan duniyar ta mu akwai bukatan logo, Rashin logo ba karamin illa bane ga ma'abota kasuwanci.

Logo shine alama, misali logon Facebook shine 'f' na Goggle kuma 'G', Nayi wannan misalin ne saboda wadanda basu sani ba.

Hatta masu blog site da website suna da bukatan logo don dorawa a shafin su saboda duk inda a kaga logon ko ba a ga sunan shafin ba za a gane cewa shafi kaza ne.

Mutane zasu rika neman ka ta yanan gizo su biya ka, ka hada kuma ka tura musu ta yanan gizo

Zaka hada logo ne a kyauta ba tare da ka kashe kudi ba, abun da za kayi kawai shine samun lokacin da zaka hada da kuma ilimin hadawa.

Don fara hada logo ka koyi Corel draw, photoshop da sauran su.

Idan kuma baka iya ba zaka iya koya ko a internet da channel na youtube, ka bincika zaka iya har ka fara hada na kudi.

Yanzu dai zan iya cewa ka riga ka iya hada logo, sai ka fara hadawa kana sharing a social media Idan a kasan kana yi za a neme ka musamman idan kana hada masu kyau

3. Gina Website:

wannan ma wata hanya ce da ake samun kudi a yanan gizo sai dai ba kowa ne yake yi ba kila ko saboda lalaci ko wani dalilin na daban.

Idan ka zama maginin website ka more domin duk wanda ka ginawa bayan ya biya ka kudin ginawan toh duk shekara a na yin renew na domain da Hosting kuma kai ne za ka rika mishi kaga kenan fa duk shekara sai ya biya ka ba wai an rabu ba kenan.

Kayi kokari ka koya kar sai dai za kayi hakuri da bata lokaci kafin ka iya amma kar wannan ya dame ka kai dai ka tuna alherin da zaka na samu bayan ka iya.

Zaka fara ne da Html da Css ko da yake ana yin na WordPress ma wanda shi kuma ba ruwan shi da coding na html ko css, Koyon su duka shine zai tabbatar da kwarewan ka.


Karanta:
  1. Yadda zaka koyi Gina Website
  2. Hanyoyi 5 masu sauki da zaka koyi Html da Css


4. Bude channel na youtube:

Bayan ka bude channel a youtube zaka rika kirkiran video ne kana dorawa mutane suna kalla kai kuma kana samun kudi.

Bayan wani lokaci idan channel din ka ya kai wani mataki zaka dora Google adsense a channel din ka wanda zaka rika samun kudi dashi.

Ba adsense bane kadai hanyar samun kudi a channel na youtube ba, za kana tallata wasu aiyukan da kake yi a cikin videon ka, akwai wadanda zasu bukaci ka musu wani aiki kuma kudi zasu biya ka

Bayan channel din ka ya samu karbuwa kana samun masu kallon videon ka zaka iya tallatawa ga masu bukata ka tallata musu channel, blog ko website din su kaga shima kudi zasu biya ka shima.

5. Fara Blogging:

Abu na karshe shine blogging, kusan kowa yasan blogging kuma yasan akwai hanyoyin samun kudi da yawa da blogging.

Da yawan masu yin blogging suna yi ne saboda sun ni a na cewa ana samun kudi dashi sai bai kuma ba kowa ne yake iya jurewa ba.

Eh tabbas ana samun kudi amma sai ka gina blog din sosai yadda zai bawa masu shiga daman karatu ba tare da tangarda ba.

Idan za kayi blogging don neman kudi ne dole ne ka Zabi Niche Mai kyau, ta haka ne zaka samu abunda kake nema

Akwai wanda duk wata sai ya cire kudi mai yawa saboda adsense da ya dora a blog din shi.

Ana samun kudi ta hanyar dora tallan wani, Koyarwa da dai sauran su.

Karanta:

A nan zan dakata , kayi kokari ko daya ne daga cikin su ka fara idan Allah ya sawa abun albarka sai kaga ya zama hamyar arzikin ka.

Kasance da Asagist a ko da haishe, Yi subscribe na blog din nan da emai din kq, duk lokacin da mu kayi sabon rubutu zai tafi har email din ka


Kayi Share

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky