(Telegram Account) Yadda zaka bude telegram

Start Telegram


















Mai karatu barka da zuwa Asagist, a yau kuma cikin ikon Allah zamu yi bayani ne game da yadda ake bude telegram a wayar android cikin sauki

Gabatarwa a kan yadda ake kirkiran account na Telegram

Tambayoyi suna yawo sosai a yanan gizo game da telegram da kuma yadda ake fara yin shi, duk da ba tun yau a ka fara shi ba amma mutane da dama basa amfani dashi saboda wasu dalilai irin na su.

Akwai masu ganin kamar yana da wahala ne budewan saboda basu taba amfani fashi bane yasa suke irin wannan tunanin, wasu kuma basu bude bane kawai saboda sun ji a na cewa kusan kamar daya yake da watsapp.

Eh haka ne suna kama sosai da watsapp sai dai kuma telegram yafi Watsapp abubuwa da dama wanda kuma kafin mu kammala darasin zan yi bayani ko da a takaice a kan Hakan idan Allah yaso

Menene Telegram?

Telegram daya ne daga cikin kafofin sada zumunta na zamani wanda ake tattaunawa tsakanin al'umma daban-daban a cikin shi.
Telegram shima kamar watsapp yake domin application din shine zaka sauke a kan wayar ka kafin ka fara amfani dashi.

Menene Amfanin telegram?

Telegram yana da amfani masu yawa ko da yake kusan kamar ka san su amma dai zan fadi wasu daga ciki saboda wadanda basu sani ba:
  1. Ana Hira (Chat) a telegram: kamar yadda na fada tun farko telegram yana kama da watsapp, kamar yadda ake hirarraki a watsapp to shima telegram a na chatting dashi
  2. Tura hotuna, audio da video: bayan hira da ake gudanarwa a telegram, zaka iya turawa abokin ka hoto, audio ko video domin ya kalla idan da bukatan hakan
  3. Bude Group (Telegram Group chart): bayan wadannan akwai group da ake budewa a telegram kuma dadin shi ko yau ka shiga zaka samu duk abun da a kayi a baya ba kamar watsapp ba, Idan ka shiga yanzu baza kaga sakonnin da aka turo su kafin ka shiga ba.
  4. Bude Makaranta: ana iya bude aji ko makaranta a telegram a na koyarwa ta hanyar amfani da group, Group na telegram yafi na watsapp da wasu abubuwan da ba a rasa ba, Idan ka fara amfani dashi tabbas zaka gane hakan.

Waye ne zai iya budewa ko amfani da telegram?

Duk wanda yake da waya musamman kirar android zai iya budewa matukar yabi matakan budewan kuma kowa zai iya amfani dashi matukar wayar shi zata yi.

Ya ake bude telegram?

A yanzu kuma zan nuna maka yadda zaka bude account na telegram ne da wayar ka don ba sai da computer kadai ake budewa ba, kabi matakan nan daya bayan daya baza ka gama karantawa ba tare da ka bude telegram din ka da kan ka ba.

  • Sauke Application na Telegram: Da farko zaka sauke application na telegram daga playstote, Idan kuma kaso zaka iya bin wannan link ka sauke shi a kan wayar ka, Bayan ka sauke sai kayi installing din telegram din.
Download Telegram Now

  • Rubuta lamban wayar ka: Bayan kayi installing na telegram, Idan ka bude zai kawo ka inda za kasa lamban wayar ka sai ka rubuta.
Telegram zasu turo wasu code (telegram confirmation code) don su tabbatar da cewa lamban wayar taka ce, Idan suka turo sai ka rubuta kayi gaba.
  • Rubuta Suna: Bayan ka rubuta lamban wayar ka kuma ka Nausa zuwa gaba, zasu nuna maka inda zaka saka hoto da sunan ka.
Hoto da sunan zasu baiyana wa abokan ka na telegram domin zai kasance ne kamar na watsapp duk wanda yake da lamban wayar ka idan yaje watsapp din shi zai iya ganin hoto da kuma sunan da kake amfani dashi.

Yadda zaka Nemi abokai a Telegram

Tara abokai a telegram ba abu mai wahala bane domin cikin kankanin lokaci zaka hada abokai masu yawa musamman idan a kayi dace wadanda kake da lambobin wayoyin su suna yin telegram, Duk wanda kake da lamban shi cikin saiki zaka same shi har ma ka tura mishi sako idan yana yi kenan fa.


Karanta:




Idan ka bude sabon account na telegram zaka same shi babu abokai to yadda za kayi ka samu abokai ku fara tattaunawa da juna shine zan yi bayani a yanzu haka sai ka biyo ni don jin yadda za kayi.

Abunda kawai za kayi shine ka shiga menu na instagram din ka
Bayan ka shiga za kaga 'Contacts' sai ka shiga, bayan ka shiga za kaga abokan ka wadanda suke telegram sai ka zabi wanda kake bukata sai ka shiga kan shi.

Wannan shine Yadda zaka bude telegram cikin Sauki, a rubutu na gaba insha Allah zamu dauki wani gaba na telegram nayi bayani a kai, Kar ka bari a baka labari musamman idan kai bakon telegram ne.

Ka kasance kullum da wannan shafin namu mai albarka, zaka iya subscribe da email din ka don samun sabbin rubutun mu.


KA TURAWA ABOKAN KA

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky