Yadda zaka kirkiri android application a wayar android kashi na 1














Kirkiran android application cikin sauki da waya kirar android kashi na daya (1), Gabatarwa

Kamar yadda na sha fada a wannan shafin cewa lallai hanyoyin hada android application suna da matukar yawan gaske domin a yanzu ba wai sai ka iya programming ko coding bane zaka iya kirkiran android application

A da can babu wata hanya da ake iya gina application na wayar android sai an yi amfani da yarukan programming, zallan code kadai zaka gani wanda ba kowa ne ya iya ba kuma ba kowa nema zai mai da hankali har ya koya ba.

A yanzu kuma da yake ci gaba a harkar fasahan zamani dada karuwa take yi an samar da wasu hanyoyi masu sauki wadanda dasu za a hada android application masu kyau ga wadanda basu iya programming ba kai har wadanda suka iya din ma.

Kwanakin baya a wannan shafin nayi bayanin hanyoyin da ake gina application na wayar android dasu ta yiwu baka karanta ba shiyasa zan dan sake baiyana su a nan amma a takaice.

Daga cikin hanyoyin kirkiran android application nayi bayani mai kama da wannan:

  •  Wadanda ake kirkirar su ta hanyar amfani da yaren programming wanda shi idan baka kware a programming ba gaskiya baza ka gane komai ba a wannan bangaren.





  • Sannan kuma akwai wadanda ake gina su a website, bayan an gama ginawa sai a sauke shi a kan wayar android a ci gaba da amfani dashi a kan waya kuma za a iya turawa duk wanda ake bukata

Shi ma wannan ba bukatan programming a cikin shi sai dai mafi yawan su sai an biya kudi kafin a kirkiri application ko da yake akwai wadanda kyauta suke bada daman hada application.

  • Na uku wanda kuma shine na karshe ana amfani ne da wani android application a gina application na android a ciki, wanda a yanzu haka  da daya daga cikin irin wadannan application zamu yi amfani.

Wadannan guda abubuwa guda uku dana lissafa duk ana amfani dasu a gina application sai dai kuma idan kwarewa kake bukata ko zaka mayar dashi sana'a ka dauki na farko idan kuma babu hali ka dauki na biyun har zuwa na karshe

Zaka iya farawa da na karshen don shi yafi sauki sai na biyu, na farkon dai shi yafi wahala, ka fara da na masu saukin sai ka rika koyon programming a hankali wata rana zaka tsinci kan ka cikin kwararru

Da wane application za a yi amfani?

Kamar yadda na baiyana muku cewa zamu yi amfani ne da wani application don kirkiran android application, sunan application da zamu yi amfani dashi shine "Apk creator"

Apk creator Kyauta ne ko sai an saya?

Application ne na android wanda kuma free ne ma'ana kyauta ne ba sai ka biya kudi zaka yi amfani dashi ba, zan yi cikken bayani a kan shi da irin applications da ake hadawa dashi, Idan ta yiwu har yadda ake gina android application dashi zan yi bayani a wannan shafi kai dai ci gaba da ksancewa da Asagist.

Kamar yadda wata kila ka sani akwai applications da dama wadanda baza ka iya amfani dasu ba sai ka saya wanda kuma ba kowa ne yake da halin saya ba, wani ba wai baya so bane  a'ah kudin ne bai dashi ko kuma akwai amma bana sayan application bane.

Don samar da sauki wa masu bukatan hada android application Apk creator sun samar dashi a kyauta aikin da za kayi kawai shine ka sauke shi a kan wayar ka, ka fara aiki dashi.

Wane irin android Application ake hadawa dashi?

Kamar yadda na riga na fada a sama appplication guda uku ne ake kirkira dashi sannan kuma wadannan applications suna da muhimmanci kwarai da Gaske.
Gasu nan a kasa zan yi bayanin su:

1. Application na Gallery; shine application na farko a jerin applications da ake hadawa da Apk creator, application ne na hotuna wanda zaka hada shi cikin kankanin lokaci.

Maimakon ka a jiye hotuna a gallery na wayar ka kadai zaka iya hada application na hotunan ka a matsayin application ta wannan hanya mai cike da sauki

2. Application na gift; application na gaba shine application na kyauta kamar Happy birthday da sauran su, zaka iya hadawa masoyiyar ka don kara dankon soyayya don wannan na masoya ne.

Har music din da kake bukata zaka iya sawa a cikin wannan application, bayan ka gama kirkira idan kasa music duk, ana hawa application wannan music zai fara tashi.

3. Hada Application na wall paper; Sai wanda yake na karshe shine kirkiran android application na wall paper.
Wadannan sune applications uku da ake ginawa da wannan Application dana baiyana a sama

Ko wace wayar android zata iya?

Wannan tambayar tana da muhimmanci domin kusan kowa zai iya yin ta, Gaskiya ba ko wace waya ce take yi ba kuma rashin yin ba wai ya ta'allaka bane da kankan.ta ko girman waya a'ah kawai dai wasu wayoyin suna yi wasu kuma basa yi.

Daga karshe Dama mun yi wannan ne a matsayin gabatarwa a darasin mu na gaba zamu yi bayani filla-filla a kan yadda zaka hada application da Apk creator, Insha Allahu zan baka link na application din a darasi mai zuwa don idan kaje playstore zaka samu da yawa ba lallai ne ka gane mai kyau din ba.


Karanta: Hanyoyi 5 da zaka samu traffic a sabon blog


Ka taba kirkiran application na Android? 
Ka baiyana mana a comments


Ka taimaka mana kayi sharing link idan kaji dadin rubutun

Kayi subscribe na Newsletter don samun sabbin rubuce-rubucen mu

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky