Yadda zaka sayi Data 200mb a kan Naira 50 a layin MTN






















Tsarin Sayan Data Mai sauki a layin MTN

Assalam Mai karatu barka da zuwa wannan shafi Mai albarka, a yau Kuma zamu yi bayani ne kan wata hanya Mai sauki ta sayan data a layin waya na MTN.

MTN kamfanin layin sadarwa ne mallakin kasar Afirka ta kudu Amma ta Zama tamkar mallakin Nigeria ne saboda Yawan mutanen dake amfani a Nigeria sun fi shurin masaki.

Wannan kamfani sun yi kaurin suna a wajen karfin Network domin Babu Kamar su yanzu haka a wannan kasa ta mu ta Nigeria

Tabbas MYN Sun ci kirarin su na cewa da suke yi "MTN Everywhere you Go" domin zai yi wahala ka shiga Gidan da Babu Mai layin waya na MTN.

MTN Ya bambanta da sauran Layukan sadarwa musamman karfin Network, Sauran Layukan sadarwan kuma mafi Yawan su sunfi MTN saukin kudin Kira da na Data sai dai kuma matsalar su daya ce rashin karfin Network.

Akwai layin da zaka iya sayan data Amma har yayi expires baka more shi yadda kake bukata ba   saboda karancin Network da suke dashi.

Wasu Layukan kuma basa samun matsalar Rashin Service ko network sai damuna ya shigo ko idan an fara Hazo, A wannan lokacin ne zaka samu mafi Yawan lokaci ba service.

Inda MTN ta cinye su shine karfin Network ko a wane lokaci ne damina ko Rani, a lokacin hazo ne ko Ra'ba basu da matsalar service sai dai Dan abun da ba a rasa ba jifa-jifa amma dai baza a hada shi da sauran ba.

Tsarin Sayan Data na Layin MTN

MTN suna da tsarin su na sayan data Kamar dai sauran layin wayar da a ke amfani dasu
Tsarin Sayan Datan su ya bambanta da sauran domin maganar gaskiya basu da saukin sayan data sai dai wani lokacin suna fito da wani tsari Mai sauki na sayan data kamar dai irin wannan tsari kenan da yanzu Zan Yi maka bayani a kai.

A asalin tsarin Sayan Datan MTN, a na sayan 200mb a kan Naira 200 ne, yanzu Kuma don saukakawa sai suka kawo tsarin Sayan 200mb a kan Naira 50 kacal.

Kaga kenan fa ka samu har saukin Naira dari da hamsin (150) tunda abun 200 ne sai a kace ka kawo Naira 50.

Wane Aiki zaka iya yi da wannan Datan?

Akwai wasu tsarukan da a ke cewa Datan Facebook ne kadai za a iya yi dashi, watsapp ko Kuma Instagram.

Toh shi Kuma wannan Datan ba a iya kance abun da za kayi dashi ba, duk abunda kake yi da data a lokacin da ka saya za kayi shi da wannan Datan.

A wane tsari ne ake iya sayan datan (MTN Tariff Plan)?

MTN Suna iya fitar da wani garabasa Mai sauki Amma wani lokacin sai suce sai Wanda yake tsari kaza ne zai ci moriyar wannan garabasa

Misali a tsarin su na Better talk (MTN better Talk) suna Bada kyautan #250 na Kira da browsing a duk lokacin da Wanda yake tsarin ya saka katin Naira 100, Kuma darin da yasa Yana Nan wannan 250 kyauta ne.

Toh shi Kuma sayan 200mb data Yana yi ko a wane tsatin MTN (MTN Tariff plan) kake.

Ko wane layin MTN za a iya sayan wannan data?

Gaskiya zamu iya cewa ba ko wane layi bane ya keyi sai dai mafi Yawan layin MTN Suna yi

Sun tura sakonnin kar ta kwana (Tex message) a Layukan sadarwa mallakin su da wannan hanyan sayan data, ta yiwu sun tura maka baka sani ba ko ka goge ko ma Yara ne suka goge kila baka sani ba.

Yanzu dai abu mafi muhimmanci shine ka gwada ka gani Idan ka dace sai kaga yayi.




Karanta:



Yadda zaka sayi Datan ka cikin sauki.


Yadda ake sayan Datan ba wata hanya Mai wahala bace, ka taba sayan data na MTN wellcome back?
Idan ka taba saya toh hanyar kusan daya ce sai dai abu daya ne kawai ya bambanta su.

Shi kuma wannan tsarin yadda zaka sayi Datan shine Kamar haka;

Ka Danna *131*25# a fuskan wayar ka sai ka Danna gurin Kira daga Nan zasu baka Datan ka 200mb sai su cire Naira 50 a layin ka.

Wannan tsarin Yana da matukar sauki ya kamata  ka jarraba ko zaka kasance cikin wadanda suka dace, Ni Kam dai yanzu haka ma dashi nake amfani domin layin MTN Dina guda biyu ne Kuma duk sun bani daman wannan tsarin.

Wannan rubutu namu a Nan zai dakata kuma tabbas zamu ci gaba da kawo muku irin wadannan rubuce-tubuce a wannan shafi namu Mai albarka.

Kana bukatan sani lokacin da muka sake sabon rubutu?
Kayi subscribe na Newsletter da emai din ka, duk lokacin mu kayi sabon rubutu Nan take zai tafi email din ka, kana bude data zaka gan shi.

Bayan ka kammala karantawa ka turawa abokan ka ta hanyar sharing don suma su samu daman cin wannan garabasa.

Kana da tambaya?
Akwai hanyoyin da zaka iya turo Mana tambaya, mun fi bukata a turo Mana tambaya a karkashin rubutun da ake bukata a yi tambaya a kai
Sannan Kuma zaka iya turo mana tambaya ta emai din mu alhuda022020@gmail.com.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky