Website 5 da zaka koyi kirkiran android Application kyauta a 2020














Application na waya yana tallafa mana sosai ta bangaren wasu daga cikin aiyukan mu na yau da kullum.

Idan kana bukatan fara koyon hada android application kuma ka rasa ta wace hanya zaka fara ko kuma kana samun rudewa to ka  kwantar da hankalin ka baka da matsala domin yanzu zaka samu natsuwa saboda kazo inda matsalar ka zata warware da taimakon Allah

Applications da akeyi suna da yawa sai da na android sun fi sanuwa saboda sune su kafi yawa a hannun jama'a a wannan zamani da muke ciki a yanzu

Idan kana da sha'awan fara hada android application tabbas kayi farar dabara domin ka dauki shawara ko kuma nace tunani mai kyau don hakan zai kara fadada maka kwakwalwa da kara samun kwarewa sannan kuma har kudi zaka samu dashi idan ka rike shi da kyau.

Akwai wadanda hada application shine aikin su kuma ya kasance sana'a a gare su domin dashi suke ci kuma suke sha har suke taimakawa 'yan uwan su da sauran mabukata.

Idan zaka fara koyon kirkiran android application akwai hanyoyi da dama wadanda zaka koya, daga cikin wadannan hanyoyi masu dumbin yawa zan nuna maka website guda 5 masu muhimmanci wadanda zaka koyi hada android application dasu

Websites da zaka koyi hada application na android

Akwai websites da dama a yanan gizo da Channel na youtube wadanda ake koyon hada application na android kuma har a cimma gaci, akwai shafuka da yawa wadanda suke karantarwa a yanan gizo kamar Noble worldUdemy Suna nan dai da yawa sai dai su ba kyauta bane sai ka biya kudin registration kafin zasu koyar da kai

Idan kana da kudi kuma ba kada matsala akan kashe su to ina baka shawara kaje ka biya kudi a inda ake koyar da na kudin, idan kuma baka bukatan kashe kudi a wannan darasi zan koyar da kai hanyoyi 5 wadanda zaka koya a kyauta ba tare da kashe kudin ka ba.


Yadda zaka sharing link wanda a kayi blocking a facebook

Menene Niche a blogging?



1. Java code Geek: A wannan website akwai cikakken bayani akan yadda ake yin android application, zai taimaka maka wajen koyon programming da android application daga farko har zuwa karshe a kyauta

Bayan ka kammala karanta tutorial na Java code geek zaka iya hada android application da kan ka.

2. Official developer android: Wannan shafi ne na musamman daga google don koyar da android application, akwai bayani daki-daki a ciki idan ka shiga zaka tabbatar da hakan

Akwai bangarori da dama kuma ko wane bangare a ciki sun yi bayani akan shi saboda masu koyo su gane kuma su fahimci darasin yadda ya kamata

Wannan website na Developer Android yafi kyau da dacewa ga masu koyon hada android application.

3. Vogella:
Vogella shima ya kunshi video ne masu yawa wadanda ake koyar da hada android application daga kan 'yan koyo har zuwa wadanda suka  fara nisa a harkar.

Ko wane bangare a Vogella akwai cikakken bayani a kanshi tun daga farko har zuwa yadda zaka gwada application din ka.

4. New Boston
New Boston kuma ya kunshi video ne masu yawa wadanda zasu kai dari biyu duk dai a kan koyon hada application na waya kirar android. New Boston

Wadannan videon kyauta ne ake kallon su kuma idan ka kalla zaka iya hada android application da kan ka
Wannan shima yana daya cikin hanyoyi masu sauki wadanda ake koyon kirkiran android application

5. Core Servlets
Wannan ma daya ne daga cikin hanyoyin koyon yin application na wayar android kuma shine na karshe daga cikin wadanda zan yi muku bayani a kai

Shi kuma coreservlets yana bukatan ka dan samu ilimin programming na java kafn ka fara shi, shima kuma yana da kyau don akwai bayanai masu gamsarwa

Wadannan sune wasu daga cikin hanyoyin koyon hada android application duk da basu kadai bane amma dai da wadannan din duk abunda kake bukata gameda android application zaka koya ba tare da biyan kudin koyo ba.

Nayi amfani ne da wannan dama domin nayi bayani a kan na kyauta, akwai na kudi kamar yadda na baiyana muku a sama.

Wadannan tambayoyin zasu amfane ka


  • Zaka iya hada applicalication da kan ka?

Eh zaka iya hada android application da kan ka kuma ba dole sai ka iya programming ba


  • Aina zan koyi Hada android application?
A Kwai website da youtube channel da dama wadanda zaka koyi hada application na waya hannun ka, Na fadi wasu daga ciki zaka iya bincike don gano wasu.

  • Hada Android application yana da sauki?
Gaskiya kai tsaye baza a ce yana da sauki ba domin idan kana bukatan koyon hada android application mai tsari dole sai ka iya wasu daga cikin yaren programming  kamar java da sauran su.



Ka taya mu sharing saboda akwai 'yan uwa da suke bukatan wannan rubutun

Ka kasance damu a wannan shafin don samun rubutu masu fa'ida a gare ka, kayi subscribe na News letter

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky