Ma'anar Valentine Day da abubuwan da ya kunsa

Valentine Day
















A wannan shafin yau kuma zamu tattauna ne akan wani al'amari wanda ya zama kusan kamar ruwan dare ne gama duniya, wannan abun kuwa shine Valentine day, ko da yake da yawan mutane sun san shi amma batun gaskiya akwai wadanda basu san ma menene Valentine ba bare su san abubuwan da a keyi a ranar.

Wasu kawai sunan suke ji kuma har suke aikatawa ba tare da sun yi bincike sun gano irin masha'an da ake aikatawa a wannan rana ta Valentine ba, wannan ne abun da ya jawo hankali na har nake wannan rubutun.

Bayan ka kammala karantawa zaka fahimci menene Valentine da kuma wasu daga cikin abubuwan da ake aikatawa a ranar valentine.

Menene Valentines Day❓

Valentines day rana ce da ake cewa Ranar masoya, Masoya ne zasu hadu a wannan ranar domin su cusawa junan su farin ciki, wannan ranar tana maimaituwa ne duk ranar 14/02 na ko wace shekara a fadin duniya.

Abubuwan da a keyi a valentine day

Abubuwan da ake aikatawa a ranar masoya ta duniya suna da matukar yawa sai dai kawai zan yi kokari na tsakuro wasu 'yan kadan,
Daga cikin abubuwan da a keyi a Valentine day akwai wadannan:

1. Girka Abinci mai Dadi: a wannan rana da ake kira ranar masoya, masoyan suna dafa abinci mai dadi suci su sha a wannan ranar da a ka mata lakabi da suna ranar Masoya.

Ba wai a kan ma'aurata kadai ake magana ba har wadanda basu da aure wato saurayi da Budurwa, ita budurwar tana dafa abinci ta kaiwa saurayin ta a wannan rana.

2. Zuwa Hotel: Masoyan suna iya haduwa a Hotel su kama Daki domin su nuna wa junan su soyayya, ba a shafa fatiha ba kuma ba Muharraman juna bane, Daga ita Sai shi a cikin daki Wane irin iskanci ne baza suyi ba❓

Wadanda kuma basu da kudin kama daki a hotel jeji ko bayan gari suke zuwa kai wasu dakunan su suke kai 'yan mata su sheke ayar su wai duk dai da sunan Nunawa juna soyayya

3. Yin Rawa: Daga cikin shedancin da a keyi a ranar masoya akwai gabatar da rawa, yadda abun yake shine Saurayi da Budurwa ne zasu yi rawa saboda farin cikin zuwan wannan rana ta masoya.

A wasu guraren har gidajen rawa ake zuwa inda kuma basu samu wannan ci gaba na mai tonon rijiya ba, a jeji da dakunan kwanan su suke yi.

4. Shaye-shaye: wasu daga cikin masu wannan dabi'a ta Valentine day suna shaye-shaye har da na maye a tsakanin su, wani ba yayi amma a wannan rana yake farawa saboda kasancewa cikin masu yi.

5. Wanka a tare: Ba wannan kadai a keyi a Valentines day ba, masoyan suna iya wanka a tare wannan shima dai bai yi kama da addini da al'adan Bahaushe ba amma wasun su sun bi sun dauke shi kamar addini ne ya shar'anta.

6. Tausa da sauran Nau'ukan Fitsara: Abu na karshe da suke yi shine Tausa da sauran abubuwa marassa kyau, ko a nan aka tsaya kasan dai anzo dab da Aikata mumunar Kaba'ira ko?❓

Wani abun da zai kara tabbatar maka da cewa Valentine Iskanci ne ziriyan shine a wannan ranar ta Valentine duk abunda saurayi zai yiwa masoyiyar shi wai kar tace komai, duk abunda zai tambaye ta kawai ta bashi ba jayayya.

Haka ita ma idan ta bukaci abu a gurin shi ba tare da jayayya ba kawai yi mata zai yi, kome zasu yi Valentine ya Halatta musu, wannan yasa zina da fasikanci suke yawaita a irin wannan ranar.

Wannan duk dabi'a ce ta yahudawa Sai wasu musulmai suka ara suka yafa a kan su, wannan sam ba dai-dai bane Iskanci da zinace-zinace kawai ake aikatawa a wannan rana.

Wani bai taba yin zina ba amma a dalilin wannan rana ya fara, Allah ne kadai yasan irin barnar da a ke aikatawa a wannan ranar.

Shawara zuwa ga iyaye

Hakki ne da ya rataya a wuyan iyaye da su kara kokari dasa ido wa 'ya'yan su musamman mata ba sai a ranar Valentine kadai ba, zata iya fita baka san inda taje ba kila taje wani gurin da bai dace ba.

Ba mata kadai ba har mazan akwai bukatan a san shiga da fitan su, an fi magana ne a kan mata saboda idan mace daya ta lalace kamar al'umma ce gaba daya ta lalace domin ita ake bari a gida da yara.

Daga karshe

Duk wanda ya haifi 'ya'ya amana Allah ya damka mishi idan yaki tarbiyantar dasu tabbas basu kadai bane suka fada cikin Halaka shima uban ko kuma nace iyayen sun ci amana kuma Allah sai ya tambaye su game da amanar da ya basu.


Karanta:




  • Yadda zaka kirkiri Sticker na Watsapp (Watsapp Sticker)
  • Channel 6 da zaka koyi kirkiran android application
  • Hanyoyi 5 da zaka samu kudi da blog din ka





  • KAYI SHARE

    Comments

    Popular posts from this blog

    Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

    Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky