Yadda zaka kirkiri Sticker na watsapp cikin sauki
















Assalam mai karatu barka da zuwa Asagist yau kuma zamu bayani ne a kan yadda ake Kirkiran watsapp sticker cikin sauki, bayan ka gama karanta wannan rubutun tabbas zaka kirkiri watsapp sticker da hanun ka har ka koyar wa wanda bai iya ba.

A 'yan kwanakin nan ina ganin tambayoyin jama'a daban-daban suna tambaya wai shin ta yaya zasu hada sticker na watsapp?

Wadannan tambayoyi sun biyo bayan yadda watsapp sticker su ka yawaita a wannan lokaci, kusan kowa yana so ne ya iya hadawa saboda dalilai irin na shi na son iya kirkiran watsapp sticker.

Akwai masu wadannan tambayoyi

1. Hada watsapp sticker yana da wahala ne?

2. Shin akwai bukatan sai na iya programming, html ko Css ne zan iya kirkiran watsapp sticker?

3. Da Application ake yin sticker na watsapp?

4. Ana iya yi da wayar android ko sai da Computer?

5. Idan da Application ake hada watsapp sticker, Application din kyauta ne ko sai na saya?

Amsoshin wadannan tambayoyi suna da muhimmanci a wannan darasi domin ta yiwu kai ma akwai tambayar da kake haratowa a cikin zuciyar ka mai kama da daya daga cikin wadannan, kasa ido sosai domin amsoshin daya bayan daya zasu zo:

1. Hada watsapp sticker yana da wahala ne?: Hada watsapp sticker ba abu bane mai wahala domin cikin kankanin likaci zaka hada kuma ka fara amfani dashi a watsapp ba tare da wata matsala ba, Natsuwa kawai ake bukata.

2. Shin akwai bukatan sai na iya programming, html ko Css ne zan iya kirkiran watsapp sticker?: a'ah babu bukatan wannan kai bama programming ba ko da turanci ne baka iya ba baka da matsala zaka iya hada sticker na watsapp

3. Da Application ake yin sticker na watsapp?:  Eh da application ake hada sticker na watsapp

4. Ana iya yi da wayar android ko sai da Computer?: a hada watsapp sticker ba sai kana da compiter ba domin wayar ka ta android ta ishe ka yin watsapp sticker

5. Idan da Application ake hada watsapp sticker, Application din kyauta ne ko sai na saya?: a'ah application da ake hada sticker dasu sun fi shurin masaki saboda tsaban yawa kuka zaka iya aiki da wanne daga ciki ta hanyar koyi da kan ka

Me zan bukata kafin na fara hada watsapp sticker?

Abubuwan da zaka tana da ba wasu abubuwa bane masu yawa gasu nan kamar haka;

1. Data: amfanin data anan shine Sauke application na yin watsapp sticker daga playstore zuwa kan wayar ka.

2. Application: Baza ka fara hada sticker ba har sai ka mallaki application na hadawa.

3. Lokaci: Idan ka hada wadannan abubuwa guda biyu da na fada a sama sai ya zamana ba kada lokacin da zaka zauna ka fara aikin hada sticker kaga kenan aikin ka bazai yiwu ba, lokaci yana taka muhimmiyar rawa a ko wane aiki.

Wadannan sune abubuwa mafi muhimmanci da zaka tanada kafin fara kirkiran watsapp sticker a wayar ka ta android.

Yadda kirkiri watsapp sticker a wayar android

Idan zaka kirkiri sticker na watsapp abu na farko da zaka fara yi shine sauke application wanda ake amfani dashi don gina watsapp sticker a kan wayar ka ta android.

  • Application da zamu yi amfani dashi shine 'Sticker Maker' don haka yanzu sai kaje playstore ka sauke shi, Bayan ka sauke sai ka shiga application din da ka sauken.


  • Idan ka sauke sai ka bude shi, bayan ka bude sai ka shiga 'Create New'
  • Zai kai ka Gallery sai ka shiga hoton da kake so ka mishi sticker, ka zabi yadda kake so sticker ya kasance Sai ka shiga Crop.
Zai kawo ka wannan hoto dake kasa
  • Ka shiga Eraser ka fitar da iya hoton
  • Idan kana bukatan yin rubutu ka shiga text kayi rubutun ka
  • Akwai Decoration shi kuma gurin yiwa sticker ado ne, misali idan zaka saka mishi gilashi ko wani abu daban a decoration za kayi.
  • Bayan ka kammala sai ka shiga Save
Shike nan ka kirkiri sticker na watsapp ta hanyar amfani da sticker maker.

Tambayoyi da Amsoshin su

  • Bayan sticker maker, akwai wasu Apps da ake hada watsapp sticker?

Ba sticker maker bane kadai ake hada watsapp sticker dashi a'ah akwai hanyoyin hadawa da yawa domin yanzu haka akwai applications masu dumbin yawa da a ke amfani dasu don kirkiran sticker na watsapp.
Daga cikin su akwai wadannan;
  1. Sticker maker for watsapp
  2. Mega Sticker Maker
  3. WAstickerApps
  4. Stickers for wataspp-sticker Maker

  • Bayan na hada sticker, Yaya zan kai shi zuwa watsapp?
Kana gama hadawa bayan kayi saving zaka same shi a watsapp din ka kuma zaka iya turawa duk wanda kake bukata, ko da yake applications da ake amfani dasu suna da yawa kuma suna iya bambanta da juna ko wanne dai za kaga yadda a ke amfani dashi a fuskan wayar ka.

Kayi Subscribe don samun sabbin rubutun mu ta email din ka


Ka taimaka kayi sharing

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky