Posts

Showing posts from April, 2020

NITDA ta shirya Training kyauta a yanan Gizo (NITDA Academy online training)

Image
NITDA ta shirya free Training a makarantar ta na yanan Gizo Hukumar NITDA ta kaddamar da makarantar yanan Gizo Wanda ta samarwa 'yan Nigeria domin su yi karatu kyauta suna zaune daga Gida Hukumar wacce take karkashin Hukumar sadarwar Nigeria Wanda Sheikh Dr. Isa Ali Ibrahim pantami tare da Shugaban NITDA Malam Muhammad kashifu ne suka kaddamar da makarantar Gwamnatin taraiya ta samar da wannan makaranta ne don bawa 'yan Nigeria daman fadada ilimin sune a harkar fasahar zamani Wanda kusan a wannan harka Nigeria tana baya ne sosai Akwai bangarorin karatu (Courses) a makarantar da daman Gaske sai dai kawai idan ka shiga ka zabi Wanda kake bukata kayi shi a kyauta. Ganin cewa duk karatun da za kayi a NITDA academy kyauta ne, Bayan ka kammala course zaka iya sake daukan wani course kaci gaba da karantawa Ka dage kayi register a NITDA academy don zaka amfana fiye da yadda kake tsammani, courses da su keyi da a online school na kudi ne ba karamin ...

Subhanallah, Sako Mai muhimmaci daga Alaramma Ahmad suleman Kano

Image
Sako mai muhimmaci daga Alaramma Ahmad suleman Kano An yi kutse wa lamban alramma sheikh Ahmad suleman Ibrahim Kano kuma ana Kiran mutane da ita ana neman kudi da sunan Sadaqa. Sakon ya fito ne daga shafin Alaramma na Facebook inda ya baiyana abun da yake faruwa a matsayin abun takaici ne Kuma ya tabbatar da cewa a na Nan ana bincike a Kan lamarin don shawo Kan al'amarin. Alaramman yayi bayani ne Kamar Haka "Sakon  Anyi hacking din number ta, Ana kiran mutane ana cewa su aika kudi za ayi musu addua,ko za a sayi wata dabba a yanka ayi sadaka.Duk wanda aka kira da lamba ta aka nemi wani abu kada ya bayar,kuma muna nan muna bincike Allah zai tona asirin masu yi,in shaa Allaah" Kutse a arewacin Nigeria kusan ya Zama Kamar ruwan dare ne musamman a wannan zamani da fasaha ke dada karuwa a tsakanin al'umma.

Anga watan Ramadan a Saudi Arabia

Image
Anga watan Ramadan a kasar Saudi Arabia Hukumomi a kasar saudia sun tabbatar da ganin watan Ramadan a yau Alhamis Wanda yau ne kenan sha'aban yake karewa Kuma yazo dai-dai da 23/04/2020 Mu ma a Nan Gida Nigeria Sarkin musulmi ya Bada umarnin fara duba ganin wata a yau Alhamis sai dai ya zuwa yanzu ba a samu labarin ganin watan ba tukuna. Muna rokon Allah madaukakin sarki ya nuna Ramadan da Rai da lafiya da Kuma imani  Allah ya kawo Mana karshen coronavirus

Gwamnatin Jahar Gombe ta kafa dokan Hana zirga-zirga saboda coronavirus

Image
Gwamnatin Jahar Gombe ta kafa dokan zaman Gida saboda gujewa yaduwan coronavirus Gwamnatin Jahar Gombe ta kafa dokan Hana zirga-zirga a fadin Jahar daga karfe bakwai na safe zuwa karfe shida na Yamma (7:00am-6:pm) Da yake jawabi a yammacin laraba 22/04/2020 Gwamnan Jahar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahya Yace dokan zata fara aiki ne daga ranar Alhamis 23/042020 Idan Allah ya Kai mu Sai dai dokan ta Sha bamban Dana sauran jahohin Nigeria domin dokar Bata Hana fita neman na sawa a bakin salati ba, Sai dai ba zuwa cin kasuwanni da zirga-zirga daga wata karamar hukuma zuwa wata. Ana umartan kowa da zaran karfe 6 na Yamma tayi ya koma Gida har sai zuwa 7 na safiya Kafin zai sake fitowa. Ba a bukatan Hidima da taron jama'a a ko wane lungu da sako na jahar Gombe saboda Yana daga cikin matakan Kariya daga coronavirus. Wannan dokan ya biyo bayan samun Mutum biyar ne da suke dauke da cutan a cikin jahar Gombe. Kayi like na shafin mu na...

Yadda zaka samu kyautan 1.GB data a Layin Airtel (Airtel App)

Image
Yadda zaka samu kyautan data sama da 1GB a Layin Airtel bayan ka sauke My Airtel App a Kan wayar ka. Kamfanin layin waya na Airtel sun Samar da wata hanya ta musamman na bayar da kyautan data ga ma'abota amfani da layin sadarwa na Airtel don shiga yanan Gizo da sauran guraren da a ke iya shiga da data Wannan Data na kyauta zaka same shine Bayan ka sauke Application na Airtel, wata Kila me karatu Yana da layin waya na MTN Kuma ta yiwu Yana amfani da My MTN App, Airtel suma sun Samar da wannan fasata ta Manhaja. A cikin wannan rubutu Zan baka link na application din sai ka sauke Kai ma ka samu wannan kyautan data Mai tsoka na Airtel Amfanin My Airtel App Ana yin Abubuwa da yawa da wannan Application Zan Fadi wasu daga cikin amfanin shi, sauran sai ka fara aiki dashi zaka gani; Ana sa katin waya Sayan data Duba balance na data Duba balance na kudin kira Wadannan wasu kenan daga cikin amfanin Manhajar Kamfanin sadarwa na Airtel (My A...

Hanyoyin da zaka rabu da yin Istimna'i, wasa da Al'aura

Image
Yadda zaka rabu da yin Istimna'i, wasa da Al'aura Mutane da dama sun Dauki istimna'i a matsayin hanyar gamsar da Kan su ba tare da sanin illolin da Yake dasu a jikin su ba musamman bayan sun yi aure domin Yana jawo tarin matsaloli bayan Mai yi yayi aure ko mace ne ko namiji. Duk da tarin illolin shi bai Hana wasu aikatawa saboda Dan jin dadin dake Ciki, abunda ya kamata ka Sani shine Bayan haramtawa da Allah yayi toh a likitance ma Yana da illoli masu tarin yawa Duk dai a cikin wannan rubutu za kaga illolin shi, hanyoyin da za kabi har ka daina da taimakon Allah, Hukuncin da ma'anar shi. Karanta:  Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN Menene Istimna'i? Istimna'i shine Mutum ya biyawa Kan shi bukata da Kan shi ta hanyar wasa da Gaban shi har ya kawo ruwa ne Mace ko namiji Wannan shine ma'anar Istimna'i a saukakakken Harshe Kuma na San Mai karatu ya fahimta ko da bai Sani ba a da. Menene Huk...

Yadda zaka Hada Business Card Kyauta a wayar Android

Image
Assalamualaikum Yan uwa Barkan ku da wannan lokaci Wannan Training ne Wanda Asagist ta gabatar a Group din ta na watsapp a Kan yadda ake hada Business Card da 3d video animation Kamar yadda na sanar cewa yau ne zamu fara gabatar da training na koyar da 3d video animation da Business Card Allah ya kawo mu Kuma ya amince farawa a yau, Toh Muna Masa godiya daya bamu aron rayuwa, Muna rokon ya bamu ikon farawa da kammalawa lafiya Na shirya wannan training ne domin 'yan Uwa na Arewa su amfana shiyasa na zabi Harshen Hausa a matsayin yaren da Zan yi amfani dashi a dai-dai wannan lokaci Ko da Yake ta yiwu Turanci kadan ya iya Shiga ciki amma dai koma Yaya ne Insha Allah kowa zai fahimta Wadannan Abubuwa guda 2 da Zan koyar daku suna da matukar muhimmanci saboda yadda ake samun kudi dasu Wani zai ce, "ashe Zan samu kudi bayan na iya hada 3d video animation da Business Card? Karanta:  Sauke Application Wanda ake rubuta JAMB CBT dashi a wayar ...