Yadda zaka Hada Business Card Kyauta a wayar Android
Assalamualaikum Yan uwa
Barkan ku da wannan lokaci
Wannan Training ne Wanda Asagist ta gabatar a Group din ta na watsapp a Kan yadda ake hada Business Card da 3d video animation
Kamar yadda na sanar cewa yau ne zamu fara gabatar da training na koyar da 3d video animation da Business Card
Allah ya kawo mu Kuma ya amince farawa a yau, Toh Muna Masa godiya daya bamu aron rayuwa, Muna rokon ya bamu ikon farawa da kammalawa lafiya
Na shirya wannan training ne domin 'yan Uwa na Arewa su amfana shiyasa na zabi Harshen Hausa a matsayin yaren da Zan yi amfani dashi a dai-dai wannan lokaci
Ko da Yake ta yiwu Turanci kadan ya iya Shiga ciki amma dai koma Yaya ne Insha Allah kowa zai fahimta
Wadannan Abubuwa guda 2 da Zan koyar daku suna da matukar muhimmanci saboda yadda ake samun kudi dasu
Wani zai ce, "ashe Zan samu kudi bayan na iya hada 3d video animation da Business Card?
Karanta: Sauke Application Wanda ake rubuta JAMB CBT dashi a wayar ka
Eyh kwarai kuwa ana samun kudi sosai, Kafin mu kammala training Zan sanar daku Hanyoyin da zaku samu kudi bayan Kun iya hada 3d animation video da business card.
Sai dai akwai bukatan kasan menene 3d video animation?
Sannan Kuma menene Business Card?
Da Yake ko wanne daga cikin su Yana zaman kansa ne, hakan nema yasa zamu dauke su daya Bayan daya
Zamu fara ne da *Business Card*
Sai Mun kammala duk abun da ya shafe shi kafin mu tsunduma Kan 3d video animation
Menene Business Card?
Business Card shine katin shaida na kasuwanci, Kamar Yadda kasan I.D Card Haka Yake
Daidaikun 'Yan kasuwa da kamfanoni suna amfani dashi don baiyana Kan su a Duk inda suka tsinci Kan su a duniya.
Hanyoyin samun kudi da Business Card
Akwai Hanyoyin samun kudi masu Yawa a gare ka Bayan ka iya hada Business Card, Ga wasu daga cikin su;
1. Kamfanoni da 'yan kasuwa zasu na baka kwangilan yi musu Business card na kasuwanci ko kamfanin su
2. Zaka Rika tallatawa a kafafen sada zumunta na zamani kuma zaka iya samun Wanda Yake bukata a mishi, kyauta za kayi ko kudi zai baka?🤔
3. Idan ka iya zaka iya bude ajin koyarwa Kuma zaka samu kudi ta wannan Hanyar ba Dan kadan ba
Karamin Misalin da zaka gane Business Card shine, Akwai wasu shagunan da idan kaje zaka iya ganin ID Card Mai dauke da sunan shagon da sauran bayanai na me I.D card din, Ko ka taba lura?
Haka kamfani ma zaka iya ganin ID card Mai dauke da sunan kamfanin, sunan me ID Card din da sauran bayanai da suka danganci kamfanin
A takaice wannan shine misalin da kusan kowa zai iya fahimtar Business Card
Yadda zaka Hada Business Card
Toh yanzu ne Kuma zamu tafi Kai tsaye zuwa Kan Yadda zaka Hada Business Card da wayar ka.
Kowa yaje play store yayi downloading na Business Card maker
Ko da Yake suna da Yawa kubi wannan link ku sauke wannan dashi zamu yi amfani https://play.google.com/store/apps/details?id=com.visiting.businesscardmaker
Bayan ka sauke sai ka Shiga Kan application din zai kawo ka Nan
Sai dai daga cikin su akwai na Kudi, duk want kaga ansa 'PRO' Toh na Kudi ne, Na farko Kuma idan kana bukatan yin komai da Kan kane sai ka Shiga kayi shi yadda kake so
Bayan ka kammala komai za kaga download sai kaje kayi download na business card din ka, shikenan ka gama da Wannan.
Business card Gaba ne da Bata, idan ka hada Gaban a sama ta gefen dama za kaga 'Back end' ka Shiga ka gyara bayan card din ka.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.



Comments
Post a Comment