Yadda zaka samu kyautan 1.GB data a Layin Airtel (Airtel App)
Yadda zaka samu kyautan data sama da 1GB a Layin Airtel bayan ka sauke My Airtel App a Kan wayar ka.
Kamfanin layin waya na Airtel sun Samar da wata hanya ta musamman na bayar da kyautan data ga ma'abota amfani da layin sadarwa na Airtel don shiga yanan Gizo da sauran guraren da a ke iya shiga da data
Wannan Data na kyauta zaka same shine Bayan ka sauke Application na Airtel, wata Kila me karatu Yana da layin waya na MTN Kuma ta yiwu Yana amfani da My MTN App, Airtel suma sun Samar da wannan fasata ta Manhaja.
A cikin wannan rubutu Zan baka link na application din sai ka sauke Kai ma ka samu wannan kyautan data Mai tsoka na Airtel
Amfanin My Airtel App
Ana yin Abubuwa da yawa da wannan Application Zan Fadi wasu daga cikin amfanin shi, sauran sai ka fara aiki dashi zaka gani;
- Ana sa katin waya
- Sayan data
- Duba balance na data
- Duba balance na kudin kira
Wadannan wasu kenan daga cikin amfanin Manhajar Kamfanin sadarwa na Airtel (My Airtel App)
Yadda zaka sauke My Airtel App a Kan wayar ka
Don sauke my Airtel Application zuwa Kan wayar ka zaka iya zuwa playstore kayi searching, ko da Yake zai iya kasancewa ka samu da yawa Kuma ba lallai bane ka iya tantance ingantaccen.
Wannan ne yasa na dauko maka link na Application din don saukaka maka shiga cikin jerin Wadanda zasu samu data fiye da 1GB a Layin su na Aitel
Bayan ka sauke kuma kayi installing sai ka bude shi, Idan ka bude zasu baka daman saka lamban wayan ka na Airtel sai kasa shi.
Idan ka Gama saitawa Bayan wasu awanni zasu turo maka sakon karta kwana Wanda zasu tabbatar maka da cewa sun baka kyautan data 1..GB Wanda zaka more yanan Gizo dashi.
Da zaran ka Hau Kan application din za kaga Datan ka a gurin duba balance, Shikenan sai kaci gaba da amfani da Datan ka na kyauta daga layin Airtel.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment