Gwamnatin Jahar Gombe ta kafa dokan Hana zirga-zirga saboda coronavirus
Gwamnatin Jahar Gombe ta kafa dokan zaman Gida saboda gujewa yaduwan coronavirus
Gwamnatin Jahar Gombe ta kafa dokan Hana zirga-zirga a fadin Jahar daga karfe bakwai na safe zuwa karfe shida na Yamma (7:00am-6:pm)
Da yake jawabi a yammacin laraba 22/04/2020 Gwamnan Jahar Gombe Alhaji Muhammad Inuwa Yahya Yace dokan zata fara aiki ne daga ranar Alhamis 23/042020 Idan Allah ya Kai mu
Sai dai dokan ta Sha bamban Dana sauran jahohin Nigeria domin dokar Bata Hana fita neman na sawa a bakin salati ba, Sai dai ba zuwa cin kasuwanni da zirga-zirga daga wata karamar hukuma zuwa wata.
Ana umartan kowa da zaran karfe 6 na Yamma tayi ya koma Gida har sai zuwa 7 na safiya Kafin zai sake fitowa.
Ba a bukatan Hidima da taron jama'a a ko wane lungu da sako na jahar Gombe saboda Yana daga cikin matakan Kariya daga coronavirus.
Wannan dokan ya biyo bayan samun Mutum biyar ne da suke dauke da cutan a cikin jahar Gombe.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments
Post a Comment