Kalli Videon matashin da yayi kokarin Damko Buhari a Argungu
Mutumin kwatsam sai gashi a Gaban shugaba Buhari da sauri Yana kokarin Mika Hannu domin ya riko Buhari yayin da jami'an tsaron dake gurin suke jan shi domin nesantar dashi daga inda Buharin Yake. Shugaban kasa Alhaji Muhammadu Buhari ya halarci taron biki na al'adun gargajiya Wanda a ka gabatar a Argungu dake cikin jahar kebbi. Wannan taro an Saba gabatar dashi ne duk shekara a jahar kebbi sai dai Kuma an Dauki tsawon shekaru goma Sha daya (11) ba tare da an Gabatar dashi ba sai wannan shekaran a ka dawo dashi. Jaridan Daily Trust ta ruwaito cewa an harbi matashin a kafa a lokacin da ya kutso Kai domin kusantar shugaban kasan na Nigeria Karanta: Osibanjo ya Sha da kyar a Hatsarin mota a Abuja Ko da Yake majiyar mu ta tabbatar Mana da cewa daga baya daily trust ta Bada Hakuri, tace lallai ba a Harbi matashin ba sai dai jami'an tsaro sun ja shi zuwa gefe. Abun da wasu daga cikin jama'an Nigeria kenan suke CeCe kuce a Kai, Was...