Gurare 5 da zaka koyi Gina websites a 2020
Akwai bukatan ka iya gina website musamman idan kana harkar blogging, a matsayin ka na blogger ya kamata kayi kokari ka koyi abubuwa da dama wanda suke alaka da yanan gizo da abubuwan da suka kewaye ta musamman idan kana blogging akan abunda ya shafi internet da social media ne
Don koyon hada website zaka iya neman wanda ya iya ka biya shi ya koya maka sai dai inda za a iya samun matsala shine ba lallai ne ka samu mai koya maka a kan lokacin da kake bukata ba saboda yanayin aiyukan masu koyarwan
Nasan zaka iya tunanin kirkiran website yana da wahala ko kana ga kamar baza ka iya ba ko wani abu mai kama da haka, Ka kasance da irin wannan tunanin?
Idan har wannan shine tunanin ka kai tsaye zan iya cewa wannan tunani naka yana kan kuskure domin babu abunda zai kasance mai wahala a gare ka sai dai idan baka nemi ilimin yadda ake yin shi ba nan ne zai zama mai wahala a gare ka
Amma duk abunda zaka tsaya duk tsawon lokaci ka koya har ka iya shi to kai kam fa ba zaka ga wahalan shi ba saboda ka riga ka iya wanda kuma bai koya ba shine zai na ganin wahalan abun.
Zaka iya koyon hada website cikin sauki ba tare da kayi haya ko ka nemi wani ya koya maka ba, akwai hanyoyi da dama a yanan gizo da zaka koya gina website tun daga farko har zuwa karshe.
Duk da akwai dubban hanyoyi a yanan gizo, mu nan zamu taimaka maka da hanyoyi na musamman masu sauki wanda zaka koyi gina website da yaddan Allah.
Zan iya kirkiran website ta hanyar koya a yanan gizo?
Eh tabbas zaka iya domin a wannan zamani da muke ciki ba kalan karatun da ba a yi a yanan gizo, akwai makarantun yanan gizo da yawa wadanda har certificate zasu baka bayan ka kammala karatun ka.
Kuma akwai wasu hanyoyin ma a yanzu wadanda ba sai ka iya yaren programming bane zaka iya hada wensite, idan kaci gaba da kasancewa da wannan shafi zaka ji su kuma tabbas zaka samu karuwa sosai, In dai hada website kake son koya to kaci gaba da karanta wannan rubutun.
Wadannan website da zan ambato duk suna da matukar kyau kuma ko wanne ka dauka a cikin su zaka iya gina website kai ba iyawa kadai ba hatta koyarwa wadanda basu iya ba za kayi idan kana bukatan hakan kenan.
Ko kasan zaka iya samun kudi masu yawa idan ka iya gina website?
1. Codecademyi: codecademy daya ne daga cikin hanyoyin koyon hada website, idan ka kasance da wannan makaranta zaka koyi abubuwa da yawa akan koyon yin website kyauta ba tare da biyan kudi ba.
Babban abunda ya bambanta tsakanin Codecademy da sauran shine hanyar da zaka koyi abubuwa.
Wannan makaranta tana koyarwa ne ta yadda mai koyon zai koya da sauri ba tare da bata lokaci mai yawa ba
Suna da Html editor wanda za kayi amfani dashi kuma ka gwada don tabbatar da cewa aikin ka yana tafiya dai-dai ne ko ka samu matsala?
Akwai bukatan ka samu lokaci na musamman don koya, idan zaka koyi hada website a codecademy ba sai ka sauke wani application a kan computer ko wayar ka ba, babu bukatan yin hakan domin sun tanadi komai a website din su
A matsayin ka na mai koyo kawai abunda zaka tanada shine lokaci da data domin a online za kayi aiki, Kayi shiri na musamman saboda sai ka bata lokci mai tsayi ko da yake ya danganci yanayin kane, idan kana da saurin ganewa ba zaka bata lokaci mai tsayi ba zaka hada website din ka.
Idan kaje wannan makaranta zaka koyi duk yaren da ake hada website dasu kamar html, css da sauran su.
2. Udemy: Wannan ita ma wata makaranta ce wacce ta kware a harkar koyar da Kirkiran website wa ma'abota koyo. Udemy Ba a koyar da hada website kadai suka kware ba, sun kware a koyar da bangarori da dama wanda ya shafi fasahar zamani.
Zaka iya samun bangarorin da zaka karanta a kyauta wasun kuma tsaka-tsaki, duk lokacin da ka saya wani darasi, zaka iya amfani dashi tun daga farko zuwa karshen shi, ko kasan wani abunda zai burge ka dasu?
Bayan ka sayi darasi, idan kana da bukata zaka iya sauke videos na darasin a wayar ka sai ka rika kallo ba tare da kashe data ba, idan kuma kaga dama zaka rika kallon su a shafin su a online.
Duk bangaren da zaka saya ina baka shawara ka duba da kyau kuma ka dubi abubuwan da mutane suka fada a kan wannan darasin, ganin abunda a kace zai taimaka maka wajen saya ko rashin saya.
Karanta: Hanyoyi 5 da zaka koyi Html da Css
3. W3schools: w3schools daya ne daga cikin tsoffi kuma hanyoyi masu matukar kyau na koyon kirkiran website a yanan gizo, ko wane irin yare na gina website zaka iya koya da W3schools.
Ko da yake basa dora video domin babu ko daya a website din su, amma zaka iya searching na ko wane darasi kuma zaka koya gina website a wannan shafin yanan gizo na w3schools.
Zaka iya mallakan certificate bayan ka kammala karanta ko wane darasi daga cikin darussan da suke koyarwa sai dai ba kyauta bane certificate din.
Idan karatu kake bukatan yi a harkar web design da development Kaje W3schools, idan kana bukatan video sai dai kayi searching a yanan gizo na darasin da kake bukatan karin haske domin ba video a shafin su.
4. Free code camp: wannan wensite gaba daya darussan ciki kyauta ne, zaka koyi web design ba kashe ko Naira a free code camp, daga sunan zaka fahimci hakan.
Idan da zaka tambayi wani kwararre cewa ta wace hanya zaka fara koyon gina website?
Zai yi wahala idan bai ce maka Kayi amfani da free code camp ba wanda zaka koyi hada website a kyauta
Abu mafi burgewa dasu shine suma kamar dau w3achool bayan ka gama karanta wani course zaka iya mallakan certificate.
Duk lokacin da ka samu lokaci zaka iya zuwa kaci gaba da hada code din ka.
Free code camp suna bayar da lokacin da ya kamata ka kammala karanta wani sabon darasi da ka dauka, misali idan zaka fara css toh zasu fada maka awannin da ya dace ka gama karantawa wannan kuma zai taimaka sosai domin zai sa ka samu isashshen lokaci na koya.
5. Simpliv: shi kuma Simpliv yana kama ne da Udemy domin akwai abubuwa da yawa da zaka same kusan iri daya.
Ko da yake akwai bambanci mai yawa a tsakanin su saboda udemy suna bada wasu darussa a kyauta amma a simpliv ba na kyauta
Sannan wani abun da zai burge ka da simpliv shine kai ma zaka iya samun kudi dasu ta hanyar tura wani yayi register ta hanyar amfani da link din ka, Kana mamaki ne? Toh ga yadda abun yake.
Abunda kwai za kayi shine kayi rijista a matsayin dan koyo zasu baka wani link to wannan link din ne idan ka turawa wani shima yayi rijista zasu baka wani kaso a cikin kudin rijistan shi.
Wadannan dai sune manyan hanyoyi 5 da zaka koyi gina website dasu, daga cikin su akwai na kyauta kuma akwai na kudi, duk wanda ka dauka zai kai ka har inda kake bukata a harkar web design.
Karanta: Channel 6 na youtube da zaka koyi hada application na android cikin sauki
Muna bukatan ji daga gare ka, ko akwai wani website da kake ganin ya kamata mu saka a cikin wadannan?
Ka taya mu sharing idan da Hali

Comments
Post a Comment