Channel na youtube 6 wadanda zaka koyi hada android application



















Kana sha'awan koyon hada android application da kan ka?

Akwai hanyoyi wadanda sun fi shurin masaki yawa kuma an samar dasu ne musamman don koyon kirkiran application na waya kirar android sai dai matsalar da ake samu shine ba kowa ne yasan da wannan ba.

Wayar android ta zama hantsi leka gidan kowa don kusan duk inda kaje zaka same shi a hannun mutane, android an fi amfani da shi fiye da ko wace irin waya a wannan zamani da muke ciki.

Saboda yawan masu amfani da android, da zaka samu mutane dari masu waya zaka samu sama da hamsin andoid ce suke mora kuma suna jin dadin aiki da ita.

Akwai hanyoyin koyo da dama a yanan gizo sai dai koyon programming wanda za a hada application an fi jin dadin video domin kana kallon duk abun da a keyi kai ma kana yi sai kaga ka koya cikin Sauki fiye da wata hanyar

Maimakon ka biya kudi don a turo maka videon koyo, Channel na youtube zasu taimaka maka sosai ba tare da kasu wasu kudade ba.
A wannan darasi zan nuna maka channel guda shida na youtube wadanda zaka koyi kirkiran application na android ta hanyar kallon videos kyauta kuma masu kayatarwa.

Akwai gurare da yawa na koyon kirkiran android application sai dai akwai na kyauta akwai na kudi, wadanda zan yi bayanin su yanzu kyauta ne ba sai ka biya ko sisi ba

Channel na youtube 6 wadanda zaka koyi hada android application

1. Arewa Teach
Arewa teach channel ne na youtube wadanda suka kware a wajen hada videos wanda ya shafi fasahar zamani suna dorawa a channel din su don wayar da kan al'umma.

Daga cikin tutorial na video wanda suke hadawa akwai na koyar da kirkiran application na wayar android kuma abun burgewan shine da Hausa suke hada videon su.

Don gani da koyon hada application na wayar android da koyon sauran abubuwan da suka shafi fasahar zamani kayi kokari ka ziyarci Arewa Teach Channel don gani, sauraro da koya.

2. The New Boston
Wannan shima wani shahararren channel ne kuma yana daga cikin wadanda suka shahara a duniya, suna dora videos da dama kuma na bangarori daban-daban, ba a harkar android application kadai suka tsaya ba.

Idan ka ziyarci wannan channel na Thenewboston zaka karu da abubuwa da dama musamman wanda ya shafi koyon hada application ta wayar android kuma sun kware fiya da yadda kake tsammani

Wannan channel yana matukar kokari gashi kuma yana da harshen isar da sako, duk abunda nake fada bazan iya gamsar da kai ba amma da zaran ka ziyarci channel din zaka tabbatar da abunda nake fada maka a yanzu

Akwai videos sama da dari biyu (200) wanda suka baiyana komai tun daga farko har zuwa karshe.

3. Android Developers
Shi kuma android developers channel ne na youtube kuma mallakin shahararren kamfanin nan ne wanda duk mai amfani da shafukan yanan gizo yasan dashi wato Google.

Suma sun kware a hada video na koyon programming da hada application na android, su kuma ba turanci kadai bane a'ah akwai wasu yaruka na daban wanda suna dora video da wadancan yarukan, kenan ba masu jin turanci bane kadai zasu iya moran shi

Wannan yana daya daga cikin manyan hanyoyin koyan hada application ko da ka kasance kwararre ne ko dan koyo.

Ba a nan kadai wannan channel na Android developers suka tsaya ba hatta sabbin labarai wadanda suka shafi wayar android suna wallafawa a channel din na su.

4. Android online training
Su kuma Android online training suna da videos kusan 200 musamman don koyar da hada application na android

Suma suna da kwarewa zaka iya zuwa channel din su  ka leko kaga yadda suke tsara videon su, Ko wane video sun yi bayani dalla-dalla tun daga yadda zaka fara kirkiran application har zuwa yadda zaka sauke shi a wayar ka

5. Slidenerd
Sai channel na kusa dana karshe shine
Slidenerd, Idan kai dan koyo ne to wannan channel din zai tallafa maka.

Wannan channel na
Slidenerd ya samu karbuwa a idon duniya domin yayi suna musamman a harkar koyar da kirkiran application na wayar android

Akwai video masu yawa wadanda su kayi baya sosai a kan koyon hada application, don kashe kwarkwatan idanun ka, ka ziyarci channel din don zaka samu karuwa.

6. Channel na Derek Banas
Derek Banas shima yana da irin na shi kwarewan a harkar koyarwa, ya sanu koyar da programming na hada application da sauran yaren programming

Akwai videos duk da basu da yawa sosai amma sun ishe ka koyon kirkiran application na wayar android

Videon sun fita da kyau ga haske da Murya, zaka koyi abubuwa da yawa a wannan channel.

Wadannan wasu youtube channel kenan guda shida wadanda zaka koyi abubuwa da dama domin ba android application kadai suke koyarwa ba, sai dai idan ka shiga za kaba wasu labari.

Bayan wadannan channel guda 6 akwai wani youtube channel da ka sani wanda suke koyar da hada application na android?
Fada mana wanda ka sani a comment.


Karanta: Kuskure 5 da sabbin bloggers keyi
Yadda zaka fara Blogging


Ka taimaka mana da sharing saboda masu bukata suna da yawa.

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky