Zan Iya Gina Website da Html kadai?
Ma'anar Html da Abubuwan da ya kunsa
Uhmm wani zai iya cewa wannan ai tambaya Mai sauki ne.
Eh hakane Kam Amma sai dai Akwai Wanda Yake bukatan a fara baiyana mishi ne tun daga tushe.
Akwai wadanda yanzu ne suka fara shigowa duniyar Html kaga kenan Akwai bukatan a fara bayani tun daga farko ta yadda zai Gane sosai ba tare da ya Sha wahala ba.
Kana daga cikin wadanda suke son bayanai da koyon Html?
Tabbas wannan rubutun don Kai a kayi, zaka samu cikakkiyar bayani a Kan Html da abubuwan da ya kunsa.
A cikin wannan rubutun zaka San ma'anan Html, yadda Html Yake aiki, zaka Dauki lokaci Mai tsayi ne kafin ka koyi Html?, Sai ka kasance online ne a kullum?, Shin Akwai wani abun da Html ba zai iya yi ba a Gina shafukan yanan gizo?.
Wadannan sune zamu tattauna a wannan darasin da zamu gabatar a yau Kuma a wannan lokaci.
Menene Html?
Html yare ne Wanda ake amfani dashi don Gina shafukan yanan Gizo ta hanyar amfani da computer ko babban wayar Hannu.
A fagen Gina shafukan yanan gizo, Html ya kasance tamtar kwarangwal wato Kamar skeleton Wanda za a iya cewa Kamar dai Mutum ne tsirara Wanda ba lallai bane ya kasance da kyan gani a wannan yanayin.
Zamu iya cewa Html Kamar mace ba kwalliya, zata yi kyau Sosai kuwa? Uhmmm! Toh wannan dai a takaice shine kwatancen da zaka iya Gane Html dashi.
Ana Gina shafuka ne na yanan Gizo da Html wato Websites sai dai kwalliyan da a ke yiwa website har ake ganin yayi kyau Sosai ba da Html a ke yi ba.
Akwai abun da a ke Kira Cascading style sheet (CSS) shine yake kayatar da shafukan da a ka kirkira da Html
CSS Shine Kamar riga da wando na jikin wannan kwarangwal da na bada misali a sama, ko Kuma kayan kwalliya ga mace Wanda shike Kara kayatar da ita.
Idan an Gina website da zallan Html bazai kayayar ba shiyasa a ke hadawa da CSS domin shi zai kayatar dashi.
Karanta: Hanyoyi 5 da zaka koyi Html da Css
Menene ma'anar Html?
Html an takaitashi ne Amma cikakken ma'anar shine Hypertext Markup Language, wannan shine ma'anar Html.
Yadda Html Yake Aiki
Html ya kunshi wasu code ne wadanda a ke rubuta su a Html editor sai a Yi saving din shi a matsayin Html file, daga Nan sai a je a duba sakamakon a bun da a ka rubuta a Browser Kamar Internet explorer ko Chrome.
Browser Yana karanta rubutun da a kayi a Editor na Html ta yadda kowa zai ga abun da a ka rubuta a shafin.
Zai Dade ne kafin Na koyi Gina website da Html?
ya danganta ne da yanayin koyon ka da Kuma abunda kake so ka iya yi da Html din, In dai kasa a ran ka zaka koya Kuma ka ba da lokaci a Kai zaka koya ne cikin kwanski kadan.
Ko da Yake kowa da irin kwakwalkwar sa, wani Yana da saurin koyo wani Kuma ana dadewa kafin ya iya, koma a wane bangare kake zaka iya koton Html cikin kwanaki kalilan domin bai da wahala abun say Ka ne kawai.
Matukar kasa Kan ka Ina baka tabbacin baza a ja lokaci ba zaka iya, domin zaka iya running code din ka kana kallon tag din ka.
Zaka iya hada website Mai kyau da Html sai ka Dan yi Mata kwalliya da CSS, Kai dai abunda a ke bukata shine ka natsu sosai a lokacin koyon.
Ba sai ka haddace ko wane Code ba domin ba duka ne zaka iya haddacewa ba, Akwai masu sauki su Kam lokaci daya zaka iya haddace su sauran Kuma a Hankali zaka fahimce su.
Sai nayi Amfani da data ne idan Zan Gina website da Html?
A'ah baka bukatan saya ko data a yayin da kake Gina shafin ka na yanan Gizo da Html, Zaka kammla codes din ka gaba daya ba tare da amfani da data ba ka ajiye shi a Kan Computer ka.
Bayan ka gama komai na Gina website din ka, a yanzu ne kake bukatan data domin kafin website din ya hau Yanan gizo sai ka sayi Hosting da Domain sai ka dauko wancan aikin da kayi kasa shi a hosting din ka.
Daga Nan website din ka ya hau Kan Internet duk Wanda yayi searching a online zai same shi Kuma zaka iya sharing link domin mutane su San dashi su Rika ziyarta.
Idan zaka Kara wani sabon abu a website din ka gurin hosting din ka za kaje wato Online sai ka Kara a can Nan take zai baiyana a yanan Gizo.
Karanta: Hanyoyi guda 5 masu sauki da zaka koyi Gina website
Ko da kayi Kari a wanda kayi na farko Wanda ba kayi amfani da data ba bazai hau online ba, gurin da ka ajiye a hosting din ka za kaje sai kayi Karin da za kayi a can.
Akwai abunda Html bazai yi ba a Gina Website?
Eyh tabbas Akwai abubuwa da dama wadanda Html bazai yi su ba a kirkiran website har sai an hada da wasu languages wadanda sune zasu karawa website din kyau da sanuwa a duniyar.
Daga cikin Abubuwan da za kayi amfani dasu akwai CSS Kamar yadda Nayi bayanin shi a sama, Sai Java script (JS) Wanda shima Yana da matukar muhimmanci a ginin website.
Shawara da Zan baka itace! Idan baka San Wadannan languages guda uku ba Html, CSS da jS ka fara da Html tukun har sai ka iya shi kafin ka tafi Kan CSS sai daga Karshe ka koyi JS.
Bayan wadannan ma Akwai Karin wasu languages na Gina website Amma dai wadannan din ma idan ka iya su zaka iya Gina website Masu kayatarwa da ban sha'awa.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Turawa abokan ka

Comments
Post a Comment