Yadda zaka fara internet da mobile Banking na Eco Bank da wayar ka

Rijistan internet da mobile Banking na Eco Bank cikin sauki



























Cikin wannan rubutu Zan yi cikakken bayani game da yadda zaka fara amfani da Bankin Eco ta yanan gizo (Online/Internet Banking) da Kuma yadda zaka yi amfani da manhajar su ta waya (Mobile App).

Kana da account a Bankin Eco kuma baka iya ko baka San yadda zaka fara online banking da amfani da mobile application na Eco Bank ba?

Toh dakata a Nan domin wannan rubutun don Kai a kayi shi, abunda a ke bukata shine ka samu natsuwa don ganin yadda zaka fara internet Banking da wayar ka.

Kafin kasan yadda zaka fara Akwai bukatan kasan abubuwan da a keyi a online da mobile Banking na Eco Bank.



KarantaFederal Universities masu sauki da kudin registeration a Nigeria



Abubuwan da ake yi a internet da mobile Banking na Bankin Eco.

Ga wasu daga cikin amfanin mobile da online Banking;
  1. Ana tura Kudi wa duk Wanda a ke son turawa (Transfer)
  2. Zaka iya duba sauran kudin da ya rage a cikin asusun ajiyan ka na Bankin.
  3. Zaka iya fitar da (printing) na bayanai na asusun ajiyan ka.
  4. Sannan Kuma zaka iya tuntuban Su idan bukatan hakan ta tashi.
  5. Zaka iya Neman cheque ko Kuma ka Dakatar dashi.
Wadannan kadan ne daga cikin amfanin online da mobile Application Banking.

Yadda zaka fara amfani da Bankin Eco Bank ta yanan Gizo (Internet Banking)

Kafin ka fara amfani da internet banking Na Eco Bank Sai kayi register tukun, yanzu zaka ga yadda a keyi tun daga farko har zuwa karshe.

Akwai form da zaka cika kafin ka fara amfani da Bankin a yanan Gizo
  • Zaka sauke form a wayar ka Wanda ake Kira e-product, zaka iya samun shi a Nan https://www.ecobank.com/_proxucts.aspx
  • Zaka cike wannan form, ka tabbatar ka cika shi ba tare da wani kuskure ba Kuma ka duba zabin da kyau saboda gudun kuskure.
  • Bayan ka cika shi, zaka Kai Bankin Eco ne mafi kusa da Kai.
Ko da Yake ba shi kadai zaka Kai ba har da wani form (Indemnity) shima zaka cika Sai ka hada su ka Kai Bankin Eco Wanda yafi kusa da Kai


Karanta: Tsarin Kira mafi sauki a layin MTN


  • Bayan sun kammala komai zasu turo maka password ta emai din ka.
  • Idan suka turo maka sai kaje shafin yanan gizo na Bankin Eco wato www.ecobank.com, ka shiga login, bayan ka shiga zasu ce kasa password Sai ka rubuta Wanda suka turo maka ta email.
  • Bayan ka tura, za a bukaci ka chanja password, Idan ka chanja shikenan ka gama register na internet Banking na Bankin Eco.
  • Kayi Kokari kana amfani dashi da sannu zaka kware, kaci gaba da Moran Bankin Eco ta yanan gizo.

Yadda zaka fara amfani da manhajar Bankin Eco (Mobile banking) da wayar ka.

Shima saita Shi a keyi kamar Na Online Banking, Da yake wayoyi suna da Yawa akwai Android, iPhone da sauran su, Eco bank ta tanadi Application na duka wayoyin.

1. Da farko zaka sauke manhajar Eco Bank (Application) a wayar ka.
Sai ka duba na irin wayar ka kar kaje kana da Android misali ka sauke na windows.

2. Zaka dannan wadannan lambobi *326# ta lamaban wayan da ka bude account din ka na Bankin.

3. Ka shiga Kan Application din ka Bayan ka kammala Installing sai kaje New User don ci gaba da register.

4. Sai kayi abunda suka bukata daga Nan ka gama saita mobile app na Eco bank a wayar ka Sai dai kawai kaci gaba da aiki dashi don ta haka ne zaka kware.

A takaice wannan shine yadda ake mobile da Online Banking na Bankin Eco.




Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Turawa abokan ka

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky