Yadda za a Ninka Kudin da kasa sau 5 a Layin MTN (MTN Awuf Bonus)
Barka da zuwa shafin Asagist, yau Kuma zamu yi bayani ne game da yadda zaka samu Ninki biyar na Kudin da kasa a layin ka na MTN
MTN daya ne daga cikin Layukan sadarwa a Nigeria Wanda yayi fice Kuma ya kasance daban da sauran Layukan waya da ake amfani dasu a wannan kasa ta mu ta Nigeria.
kamfanin layin MTN mallakin kasar Afirka ta Gudu ne sai dai ba kowa ne yasan da hakan ba a Nigeria saboda yadda ake amfani da ita ba kakkautawa.
Suna da tsare-tsare da dama na samun kyautan Kati ko Kuma Ninka Kudin da a kasa a layin su.
MTN kusan shi a kafi dashi a kafi amfani a Nigeria, hakan ya biyo Bayan karfin Network ne da suke dashi Wanda ake musu lakabi da MTN every where You Go
Rubutu Mai Alaka: Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN
Tabbas wannan layi suna da matukar karfin Network sai dai Kuma ba kowa ne yake jin dadin amfani da layin ba saboda yadda mutane da dama suke Cece-kuce a Kan saurin Cinye data ko kurin kira.
Wani ma cewa yake tun da Yake bai taba samun kyautan kudi ko data ba daga gare su
Kana cikin masu irin wanna tunani?
Toh tabbas wannan rubutun musamman saboda irin ka a kayi shi domin zaka samu Ninki har biyar na Kudin da ka saka a wannan tsari da na baiyana cikin wannan rubutun
Ko da Yake sun Dade da wanna tsari sai dai ba duka Jama'a bane suka San dashi, don sanar da wadanda basu sani ba da Kuma tunatar da wadanda kila suka manta yasa Nayi wanna rubutun.
Yadda tsarin Ninka Kudi na MTN Awuf yake
- Idan kasa katin Naira 100 zasu baka Naira 500
- Idan kasa katin Naira 200 zasu baka Naira 1000
- Idan kasa Naira 400 zasu baka Naira 2000
Haka dai tsarin Yake ko nawa kasa zasu Ninka maka shi sau biyar.
Rubutu Mai Alaka: Tsarin Kira mafi sauki a layin MTN
Yadda MTN Zasu baka Bonus Mai Yawa ta hanyar Ninka kudin da kasa
Ga yadda zaka Ninka katin da kasa har sau biyar a Sim Card din ka na MTN:
- Sayan Kati: Abu na farko da za kayi shine ka sayi katin MTN Wanda kake da bukatan sakawa misali Na dari ne ko sama da haka, Bayan ka saya sai ka tafi mataki na gaba.
- Idan ka sayi katin ba sa shi Kai tsaye za kayi a layin ba Kamar yadda ka Saba sawa, a'ah ga hanyar da za kabi a mataki na gaba kasa katin har su Ninka maka shi sau biyar.
- Zaka Danna *888*lambobin katin#.
Karin Bayani
Wato Idan ka sayi katin zaka Danna *888*pin#, wannan shine hanyar da za kabi.
Da zaran kasa ka Danna gurin Kira Nan take za kaga kudin ka ya shiga har da Ninki biyar na Kudin da kasa.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Turawa abokan ka

Comments
Post a Comment