Yadda za kayi transfer daga account din ka na polaris Bank
Polaris Bank daya ne daga cikin bankunan da ake amfani dasu a Nigeria, kasancewan bankuna suna da Yawa Kuma ko wanne da yadda ake amfani dashi shiyasa Nayi kokarin baiyana yadda zaka yi transfer na Kudin dake ajiye a account din ka na Bankin polaris.
Akwai Hanyoyin transfer da dama Wanda bankuna suke Bada daman tura kudi zuwa lamban account na Wanda ake so a turawa Kudi Sai dai a yanzu Zan yi bayani ne a Kan lambobin da ake amfani dasu (USSD Code) don yin transfer.
Ko da Yake ba transfer ake ake iya yi da lambobin ba ana yin Abubuwa da dama wadanda Zan yi maka bayanin cikin wannan rubutun da kake karantawa a yanzu Haka.
Karanta: Hanyoyi 5 da zaka samu Kudi ta yanan Gizo kana cikin Gida
Amfanin USSD Code na polaris Bank
Kafin na fara bayanin anfanin USSD Code Zan yi bayani a Kan menene USSD Code?
USSD Code sune lambobin da ake amfani dasu don yin wani aiki na musamman Wanda a ka samar dasu, misalin USSD Code sune Kamar haka;
- Lambobin duba balance na bankuna
- Lambobin duba balance na Layukan
- sadarwa misali MTN Ko Zain
- Lambobin sa Kudi na Layukan sadarwa
Wadannan sune daga cikin misalai na USSD Code.
Daga cikin amfanin wadannan Lambobin tura kudi na Bankin Polaris a kwai wadannan abubuwa guda uku.
- Ana duba balance na Kudin dake account din ka na Bankin
- Zaka iya turawa ko wane account Kudi
- Zaka iya biyan kudin wuta Dana makaranta.
Lambobin da ake amfani dasu na Bankin Polaris sune Kamar haka *833#, dashi ne za kayi duk wadannan abubuwa Dana ambata a sama.
Yadda zaka yi amfani da Lambobin transfer na Polaris Bank
Amfani da wadannan lambobi na transfer na Polaris Bank ba wani abu Mai wahala bane, don yin transfer ga matakan da za kabi;
Yadda zaka yi amfani da Lambobin transfer na Polaris Bank
Amfani da wadannan lambobi na transfer na Polaris Bank ba wani abu Mai wahala bane, don yin transfer ga matakan da za kabi;
- A fuskan wayar ka sai ka dannan *833#
- Ka zabi sunan Bankin Wanda zaka turawa kudin a cikin jerin Bankunan da suka nuna maka.
- Ka rubuta lamban account na Wanda zaka turawa kudin da Kuma adadin yawan kudin da kake da bukatan turawa.
- Daga Karshe zaka rubuta lambobin da kake amfani dasu idan za kayi transfer, daga Nan kudin zai tafi zuwa ga Wanda ka turawa.
Abubuwan da zaka lura dasu yayin ransfer a Polaris Bank da wayar ka
Kafin kayi transfer akwai abubuwan da ya kamata ka sani, daga cikin su Akwai wadannan:
- Idan transfer da za kayi a yanzu shine na farko, Bayan ka rubuta lambobin zasu turo maka wasu matakai da za kabi kafin ka fara yin transfer.
- Idan kana amfani da current da saving account ne da lamban waya daya, a tsarin su idan za kayi transfer Current account din ka zasu fara tabawa.
- Kafin kudin ya fita daga account din ka sai sun nuna maka lamban account da sunan me account don ka duba da kyau saboda kar ka turawa wani Mutum daban.
- Kudin da zaka iya cirewa daga account din ka na Polaris Bank a rana shine Naira dubu 20, Sai dai zai yiwu su iya chanjawa duk lokacin da suka so.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Turawa abokan ka

Comments
Post a Comment