Yadda za kayi Fix na ads.txt file a Blogger


























Bayan ka Gina blog har ka Kai matakin samun karbuwa a duniyar AdSense Wanda za a iya cewa ka kusa fara girbe romon dadi wato sakaiya na wahala da ka Sha da gwagwarmaya kafin blog din ka ya kawo wannan mataki.

Burin ko wane BLogger shine shafin shi ya samu karbuwa a gurin mutane da Samun AdSense domin samun 'yan chanji a ko wane wata.

Ko da Yake ba ko wane BLogger bane Yake kawo wannan mataki saboda dalilai da dama suna iya jawo cikas a blogging domin ba kowa bane Yake iya jurewa bin dokokin Su.



Karanta: Hanyoyi guda 5 da ake samun kudi da blog



Ta yiwu ka dau lokaci Mai tsayi kana Gina blog din ka, ta yiwu ma ka dau watanni ko shekaru kafin AdSense su kayi approve na blog din ka, Bayan sun yi approved Kuma sai ka sake samun Kan ka a wata matsalar ta ads.txt a gurin Notification na AdSense din ka.

Zaka iya samun Approved na AdSense sai yazo maka da Gargadin ads.txt a ta sama Wanda hakan Yana shafan kudin da zaka samu da AdSense a blog din ka

Ko da an taba tallan da Google ya baka baza ka samu lakadan din ka yadda yadda yadda yadda dace ba dole zasu Dan samu tasgaro, bazai dawo normal ba har sai ka kirkiri ads.txt file a Blogger site din ka.

Ni ma dai na taba samun irin Wannan matsala a baya Nan take na kama bincike don gano hanyar da Zan magance matsalar, Nayi bincike sosai Wanda a lokacin da nake binciken na Bata lokaci da Kudi domin sayan datan bincike a yanan gizo da YouTube.

Cikin binciken ne Na samu maganin matsalar Kuma ba tare da Bata lokaci Mai tsayi ba wannan Gargadin da su kayi min ya Fece a kasa da awa 24.

Ko da Yake sun ce Yana iya Kai wata, Akwai wani aboki na ma da na shi ya Kai wata biyu Amma matsalar Bata kau ba, Ni Kuma da dare Nayi waahe gari da safe sai ya gyaru.

Abun dace ne idan kayi sa'a cikin kankanin lokaci komai zai dai-daita, Kai dai biyo ni don ganin yadda zaka samu warakan ads.txt a Blogger.

Da Yake platform da ake Blogging dasu suna da Yawa Kuma kusan ko wanne da yadda a ke amfani dashi, a Blogger nafi kwarewa Kuma Nayi amfayi da wannan method a BLogger matsalar ta kau.

Shiyasa nace a Blogger domin na warware irin Wannan matsalan ne a wani shafi na na Blogger.






Yadda ake fix na ads.txt a shafin Blogger

Don magance wannan matsalar ga Hanyoyin da za kabi, ka natsu da kyau kar ka shiga inda ba a ce ka shiga ba domin zaka iya haifar da wats matsalar wa blog din ka.

A Gargadin da AdSense su ka maka, za kaga Akwai Fix Akwai Kuma Learn More.
A learn more sun yi bayanin yadda ake kirkiran ada.txt sai ka shiga domin ganin bayanan da su kayi a Kai.

Ko da Yake ba lallai ne ka Gane ba domin ba suyi cikakken bayani ba Amma dai a yanzu Zan to maka cikakken bayani Wanda kafin ka gama karanta wannan rubutun zaka gane yadda zaka samu mafita a wannan matsalar.

Bayan kaje kaga bayanan da su kayi a learn more, ko da Yake ba dole bane sai kaje,
Zamu fara fix ads.txt kasa hankalin ka gaba daya a Nan.

  • Shiga Fix Now: Abu na farko da zaka fara shine ka shiga Account na Google AdSense din ka sai kaje gurin da suka ce Fix Now.
  • Sauke ads.txt file: Bayan ka shiga Fix Now, za kaga inda a ka rubuta DiwnlDow sai ka shiga kayi Downloading, Nan take zai sauka a Kan wayar ka.
  • Copying ads.txt: Abu na gaba shine zaka copy wannan abunda ka sauke a lokacin da ka shiga Fix Now.
Kaje Kan wayar ka sai ka bude wannan abun da kayi Downloading Amma bazai bude ba Sai da text editor, zaka iya budewa ko da ES Explorer ko wani text editor da kake dashi.

Bayan ka bude za kaga want rubutu Mai Kama da wannan google......., pub-............., DIRECT, ........ Sai kayi copy din su.

  • Shiga Blogger: daga Nan sai ka shiga shafin ka na Blogger—>Settings—>Search preference
Bayan ka shiga Search preference, a kasa gurin monitization za kaga edit sai ka shiga, 
NOTE: ka duba da kyau ka tabbata shi ka shiga domin idan ka taba want Abu a gurin zai iya lalata maka blog.

  • Ajiye ads.txt: Idan ka shiga Edit za kaga zabi guda biyu Yes da No sai ka taba Yes, zai kawo ka wani gurin rubutu sai kayi paste na rubutun da dazu nace kayi copy din shi a gurin Sai ka shiga Save changes.
  • Saka ads.txt a Gaban Url: Abu na karshe shine rubuta ads.txt a Gaban sunan Blogger site din ka.
Abun da za kayi a Nan shine, ka hau browser sai ka rubuta sunan Blogger site din ka a karshen sai kasa ads.txt ka Danna search.
Misali: https://www.asagist.com.ng/ads.txt sai kayi search



Insha Allah ka magance wannan matsalar kenan har abada.

Wannan itace hanyar da za kabi domin kirkiran ads.txt file a Blogger site.





Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.


Turawa abokan ka

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky