Tsarin Sayan data a layin Airtel Cikin Sauki a 2020























Airtel daya ne daga cikin layin sadarwa da ake amfani dasu a Nigeria Wanda a Kuma wasu sun fi sanin shi da layin Zain.

Ya samu wadannan suna  mabambanta ne dalilin chanjin suna da a kayiwa kamfanin da dadewa, Sai dsi a yanzu haka sunan layin shine Airtel.

Wannan layi na Airtel suna da saukin tsarin sayan data Wanda a yanzu haka Yana daga cikin Layukan waya da ma'abota amfani da yanan gizo suke tururuwan zuwa saya saboda yadda Datan su yake da sauki.

Ko da yake layin Glo ma suna da tsarukan sayan data Mai sauki sai dai yanzu Zan yi bayani ne a Kan Na Airtel, biyo ni sannu a Hankali don ganin yadda zaka more garabasan data.

Airtel suna da Tsari na sayan data Mai matukar kyau Wanda mutanen Nigeria suke musu Allah Sam Barka, Kuma wannan tsari na Airtel yasa Kamar gasa ne a tsakanin sauran layukan sadarwa da muke amfani dasu a Nan Gida Nigeria.

Ba Abun mamaki bane don datan kamfanin layin waya na Airtel ya Zama da sauki domin Layin Glo ma Akwai sauki sosai, a bun da zai fi burge ka da Datan shine zai yi aiki a ko wane irin waya kake aiki.



Rubutu Mai Alaka: Tsarin Kira mafi sauki a layin MTN



Ta yiwu wasu mutanen suyi tunanin ko Kamar tsarin data ne na MTN Wanda suke saukaka Shi a cikin dare kadai, a'ah ba haka bane, wannan sabon tsarin Airtel a ko wane lokaci Yana da sauki da safe ne ko yamma dare ne ko rana.

Zaka iya mallakan datan ba wai sai idan sabon sim Card kake dashi ba, masu tsohon sim card ma suna darawa a wannan data Mai sauki na Airtel.

A kasan Nan zan baiyana maka tsarin sayan data Mai sauki da Kuma Yadda zaka sayi Datan a layin Airtel cikin sauki

Tsarin data a layin Airtel Mai Sauki

Don saukaka maka Zan yi bayani har da Ranar da Datan zai Daina aiki (Expiring date).

Tsarin Sayan Datan Airtel

Kafin yanzu a na samun data ne (10mb) a Kan Naira 100, ko da yake layin Airtel Dama suna da sauki a wajen saya da amfani da yanan gizo a bangaren Data.


  • Tsarin Data 50mb a Kan Naira 100:

A wannan tsarin zaka sayi Data ne Na Naira 100 Wanda zasu baka data Guda 50mb.

Wannan tsarin Na kwana daya ne kacal Ko da Datan ka ya rage idan ya wuce kwana daya to sauran zasu Zama Babu su.

Don sayan wannan data, ka tabbata akwai Naira 50 a layin ka na Airtel sai ka dannan wadannan lambobi a fuskan wayar ka sai kabi matakan sayan.


  • Tsarin Data 200mb a Kan Naira 200:

Wannan shima tsari ne na Sayan data Wanda Airtel suka bullo dashi don saukakawa masu amfani da layin su na Airtel Wanda zaka sayi megabytes 200 (200mb) a Kan Naira 200 kacal.

Zai dauki tsawon kwana uku kafin ya daina aiki, kenan dai 200mb zaka yi kwana uku kana moran shi, bayan kwana ukun ne zai yi expire Idan baka karar dashi ba kenan.

Don sayan wannan data dannan *412# sai kabi matakan da zasu iya baiyana a fuskan wayar ka.




Rubutu Mai Alaka: Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN



Tsarin Datan Airtel na Sati-Sati (Airtel Data weekly plan)


  • Tsarin sayan 750mb a Kan Naira 500:

A Tsarin data na Sati-Sati a layin Airtel zaka sayi 750mb ne a Kan Naira 500 Wanda zai dauke ka tsawon Sati biyu.

Ko da Yake MTN Suna da Tsarin sayan data Mai kama da wannan Amma sai dai na Airtel din ya fi saboda har sati biyu zai yi kafin ya 'kare aiki.

Danna *418# don sayan 750mb data a Kan #200 a layin Airtel.

Tsarin Data na wata-Wata (Airtel Data Monthly Plan)

Layin Airtel sun fitar da Tsarin sayan data har na tsawon wata saboda jin dadin masu amfani da Layukan na su na Airtel a wannan kasa ta mu ta Nigeria.

Tsarin data na Wata yana da matukar tasiri musamman ga wadanda ko wane lokaci suke amfani da yanan gizo tun daga Kan 'Yan kasuwan Yanan gizo har zuwa Kan sauran dai-daikun mutane.

  • Tsarin 1.5GB a Kan Naira 1000:
Airtel zasu baka data 1.5GB a Kan Naira dubu daya. Kuma dadin ma shine zaka iya amfani dashi a ko wace irin waya ko computer don hawa yanan gizo da sauran su.

Idan ka sayi Datan zai Kai ka tsawon wata daya kafin ya daina aiki, don Says Danna *496#
  • Tsarin Airtel na 3GB a Kan Naira 1500
Da Naira 1500 zaka samu data fiye da Ninki biyu na tsarin da Nayi bayani a sama, Tabbai Airtel suna da saukin sayan data, Yanzu Kam ka tabbatar ko?


Shima dai kwanaki talatin zai yi cif kafin yayi expire Wanda Zan baka shawara gara ka saye shi a Kan ka sayi na Dubu dayan can duba da yadda zasu ninninka maka Datan idan ka Kara Naira 500.

Don sayan data 3GB a Kan Naira 1500 dannan wadannan lambobi *435#.

Wannan Datan Yana da matukar sauki Amma kafin ka saye shi ka dubi Wanda Nayi bayanin shi a kasa.

  • Tsarin Datan Airtel 5GB a Kan Naira 2500:
Shima dai wannan kaga yadda yake da sauki, haka tsarin su yake a na haurawa sama suna Kara sauki, Kai dai ka dubi dai-dai da Kai ka saya ma'ana dai kar ka wuce tsayin ka.

Shima Datan na tsawon wata daya ne Wanda a Kan Naira 2500 zaka mallaki data har 3GB Wanda zaka more har tsawon kwanaki 30.

*437*1# su zaka dannan a fuskan wayar ka don sayan wannan data Mai sauki.

Ga wasu tsare-tsaren Datan Kuma da yadda ake sayan su a layin Airtel



A Nan Zan dakata, da fatan ka samu tsarin Data Mai sauki cikin wannan tsarin Airtel?




Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.


Kayi Share

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky