Sakamakon Gwajin Sunusi Lamido Sunusi na Coronavirus Ya Fito

























Sakamakon Gwajin Coronavirus da a ka yiwa tsohon Sarkin Kano malam Muhammad Sunusi Lamido Sunusi ya Fito.

Idan baku baku manta ba Gwamnan Jahar kaduna ya kamu da cutar dake sakale numfashin na Covid 19 Wanda a kafi Sani da Coronavirus.

A jiye ne 28 ga watan uku sakamakon gwajin da a kayi mishi ya fito Wanda ya nuna ya kamu da cutar Kuma yanzu Haka an killace shi domin gabatar mishi da jinya.


Karanta: Malam Nasir Elrufa'i ya kamu da Coronavirus


Da yake cutan a na kamuwa da ita ne ta hanyar mu'amala da Wanda ya kamu da cutar Kuma an Samu mu'amala Mai karfi a tsakanin Sunusi Lamido Sunusi da Gwamnan Kano.

Tun Bayan da a ka tabbatar da Gwamnan kaduna ya kamu da cutar,  mutane da dama suke Kira ga tsohon Sarkin Kano malam Sunusi Lamido Sunusi da yaje a mishi gwajin coronavirus Sakamakon cudanya da su kayi da Nasir Elrufa'i Bayan an sauke shi daga sarautar Sarkin Kano.

Idan baku manta ba Bayan an sauke Sarkin Kano daga sarautar shi malam Nasir Elrufa'i ya ziyarce shi Kuma sun yi tafiya mai nisan Gaske a Mota daya.

Bayan sun yi wannan tafiyar tun daga jahar sanarawa har zuwa jahar lagos, Elrufa'i ya sake Kai mishi ziyara a yayin da suka gana da juna.

Wannan babban dalilin da yasa tsohon Sarkin yayi gwaji da iyalan shi Kuma sakamakon gwajin ya fito in da a ka tabbatar da cewa Wannan cuta ta Covid 19 Bata kama shi ba.


Karanta: Sauke Application Wanda ake rubuta JAMB CBT dashi a wayar ka


'Dan Sunusi Lamido Sunusi ne mai suna Adam ya tabbatar da Sakamakon gwajin a shafin shi na Tuwita Kuma yace kaf gidan su Babu Wanda ya kamu da cutar.

Mutane da dama musamman masoyan tsohon Sarkin sun nuna farin ciki da nuna godiyar su ga Allah da yasa ba a Same su da cutar ba.












Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky