Lambobin kiran Customer care na Guaranty Trust Bank (GT BANK)
![]() |
| Lamban waya, Email address da website na GT Bank |
Customers care na Guaranty Trust Bank daya ne daga cikin customers care masu saurin mayar da amsa da warware matsalolin customers a bankunan da muke dasu a Nigeria.
An kirkiri GT Bank a shekaran 1988 sai dai ta zama cikakkiyar kamfani ne da kuma fara aiki tukuri a watan uku na shekaran 1991 Wanda zuwa yanzu tayi kaurin suna hade da karfi a Nigeria.
Ba a Nigeria kadai tayi karfi ba harda kasashen waje musamman Yankunan mu na afurka, daga cikin kasashen da suke da bankuna akwai koddi buwa, Ruwanda, Gambiya, Ghana, Kenya da wasu kasashen Turawa.
Guaranty Trust Bank sun hada daman yin amfani da bankin ta yanan gizo Wanda a turance a ke kira Internet ko kuma online Banking, Bayar da bashi ga Wanda ya cika ka'idan karban bashi
Karanta: Hanyoyi 5 da zaka samu Kudi ta yanan Gizo kana cikin Gida
Customer care na Bankin GT (GT Bank) zaka iya samun su a ko wane lokaci idan ta waya zaka neme su ba kamar zuwa bankin da kai bane Wanda zaka iya samu sun ta shi idan ba kaje a kan lokaci ba.
Ko wane lokaci zaka same su idan kiran su za kayi ta lamban wayan su ko kuma ta Hira kai tsaye dasu ta (Live Chat) ta manhajar su (Application) ko ta shafin su na yanan Gizo (Website).
Idan kana da tambaya Wanda kake son yi a kan GT bank game da aiyukan su kamar Bude Account, matsalolin da suka shafi katin cire kudi (ATM), Tura kudi daga account din ka zuwa wani, Neman bayanai na Account din ka wato Bank statement ko wata matsalar zaka iya Neman customer care na bankin ta Lamban waya, email ko ta chatting
Lambobin kiran Customer care na GT Bank
Don yin magana da Customer care na ko wane Guaranty Trust Bank zaka iya kiran daya daga cikin wadannan lambobin waya.
- 0803 900 3900
- 0700 4826 66328
- 0802 900 2900
- 234 1 448 0000
Sai dai kuma ka Sani kiran wadannan ba kyauta bane kuma za a ja maka kudi sosai ba kamar yadda kake kiran gama garin mutane ba.
Idan kana bukatan magana dasu Wanda ba sai ka cinye katin ka ba sai ka tuntube su ta chatting (Live Chat).
Zaka iya samun Su a Shafin su na tweeter a @gtbank_help.
Email address da Shafin yanan Gizo (website) na Guaranty Trust (GT) Bank
Don koyo ko sanin abubuwa da dama Wanda ya shafi wannan Banki na GT sun Samar da Shafin yanan Gizo wato website Wanda idan ka shiga zaka samu duk bayanin kake bukata
Ga Likau (Link) na website din GT Bank zaka iya ziyartar Shafin don ganin abubuwan da ya kunsa www.gtbank.com.
Idan kuma Neman Karin bayani kake yi akwai akwatin imel (Email Address) da suka bayar Wanda zaka iya tura musu sako kuma su turo maka da amsa da zaran sakon ya Isa gare su
Suma dai ga nan link na email din, nan take ba tare da bata lokaci ba zai kai gurin tura sako ka tura musu korafin ka complaints@gtbank.com.
Idan baka samu daman magana dasu ta lambobin su dake sama ba, zaka iya cika wani form (Complaints form) Wanda zaka gani a website din su sai ka baiyana musu matsalan ka.

Comments
Post a Comment