Jerin Universities a Nigeria da suke Distance Learning
Jami'o'in da suke Distance Learning a Nigeria
Distance Learning tsari ne Wanda a ka fito dashi domin saukaka karatun digiri wa wadanda ba su da cikakken lokaci ko daman karatu a Duk Kan ranakun karatu da muke dasu a mako
Nigeria ta kasance da wannan tsarin sai dai ba ko wane jami'a bane suke yi saboda doka da Tsarin Jami'o'i na Kasa wato National University Commission.
Yadda tsarin Distance Learning Yake shine, wata jami'a ce zata nemi wani bangare musamman a cikin wata makaranta sai a samar da Dalibai wadanda zasu ke zuwa karatu misali Kamar sau uku a sati ko bisa ga yadda suka tsara
Duk da ba a cikin wancan jami'ar suke ba ta yiwu ma makarantar ba a garin da jami'ar take Yake ba Amma duk da haka suna karatun ne da sunan wancan jami'a.
Bugu da Kari Kuma zasu fita ne da result na wancan jami'ar sannan Kuma har searvice suna zuwa Bayan sun kammala karatun su.
An samu sauki sosai a wannan tsarin da a ka fito dashi, wadanda suka manyanta ne da 'Yan kasuwa su kafi jin dadin wannan tsari domin sune masu karancin lokaci.
Mutane da dama sun samu daman Karin karatu ta distance learning, ba don distance learning ba da mutane da dama baza su yi karatun digiri ba.
Kamar dai yadda na fara bayani a sama ba duka jami'an Nigeria bane suke distance learning, wasu ne daga cikin su keyi Don haka biyo ni sannu a Hankali don sanin su.
Ba wai za a saka bane a cikin aji a yi ta karantar da Kai Kamar yadda tsarin sauran karatu yake gudana ba, sun Fi bayar da kayan karatu Wanda ko daga gida ne zaka Rika karatun ka.
Bayan Kun yi jarabawa Kun sakamako ya fito, Result din zai kasance iri daya ne da Wanda yaje cikin makarantan yayi karatu.
Ga wani misali, Jami'ar Mai duguri tana Distance Learning, sai ta samu wani bangare a cikin makarantar FCE na jahar Gombe Wanda yanzu haka Akwai 'yan distance a gurin
Karanta: Tsarin Kira mafi sauki a layin MTN
Idan suka gama Result din su zai fito ne da sunan Jami'ar Mai duguri, Kamar dai a cikin garin Maiduguri su kayi karatun.
Jami'o'in Nigeria da suke Distance Learning
1. Jami'an Maiduguri
Jami'an Maiduguri tana daya daga cikin tsoffin jami'o'i a Nigeria Wanda Kuma tana daya daga cikin wadanda suke Distance Learning
Suna da Tsarin karantarwa Mai kyau Wanda kowa Yana yabawa bisa irin tsarin koyarwa da suke yi.
Mafi karancin shekarun da suke karba a makarantan su shine shekaru 16, Idan ka zaka wadannan shekaru baza su baka admission sannan Kuma idan kana bukatan fara distance learning za kaje portal din makarantan ne ya cika a yanan gizo (Online Application).
Kana bukatan neman karin bayani a Kan tsarin Distance Learning na jami'an Maiduguri?
Ba kada matsala ga Link na Webster din Su Nan ka duba zaka samu cikakken bayani a kai www.unimaidcdl.edu.ng
2. Jami'an Ahmadu Bello dake zaria
Ahmadi Bello University zaria ma tana daya daga cikin jami'o'in da suke yin Distance Learning Kuma ita ma dai tsohuwar jami'a ce Kamar yadda wata kila ka sani.
Bayan Digiri har da Diploma su keyi a wannan tsarin karatu na Distance Learning, kenan idan WASC ko NECO da kake amfani dashi bai Kai ka samu daman gurbin karatu na digiri ba zaka iya cika diploma.
Akwai bayanai masu Yawa a website din su, ba Sai na cika ka da surutu ba kaje ka duba don samun cikakken bayani a Kai. www.abudlc.edu.ng
Karanta: Yadda zaka sayi 200mb a kan Naira 50 a layin MTN
3. University na lagos
Jami'an Lagos dake akoka suma suna daga cikin masu yin Distance Learning a Nigeria, jami'an a na Mata lakabi da suna Unilag.
Suna da Tsarin karatu na distance learning Kuma suna da bangarorin karatu da dama sai dai Wanda ka zaba Ko Kuma kake da bukatan yin shi a rayuwar ka.
Daga cikin tsarin su, basa bada admission wa Wanda Yake kasa da shekaru 21, Wanda Baida result a Hannu jira Yake shima bai da daman neman Wannan makaranta ta Distance Learning na jahar Lagos.
Suma dai zaka iya samun Karin bayani idan kana bukata kenan a website din su www.dli.unilag.edu.ng
4. Jami'ar Ibadan
Jami'ar Ibadan tana daga cikin makarantun da a ke distance learning, suma suna da bangarorin karatu masu Yawa.
Zaka iya bincikawa kaga ko zaka ji sha'awan kasamkewa daya daga cikin daliban su.
Don shiga aji daya Ana bukata dalibi ya kasance Yana da credit 5 a Zama daya ko Kuma 6 a Zama biyu, masu yin D.E Kuma (Direct Entry) a na basu aji biyu ne idan sun cika ka'ida.
Shima dai application din a online a ke cikawa Kuma ya Zama wajibi kafin ka tura kudin ka duba da kyau kar ka turawa wani bankin na daban.
Akwai bayanai masu Yawa Wanda suka you a website din su, ba bukatan sai na cika ka da surutu Mai Yawa ka shiga ka ganewa idanun ka. www.dic.ui.edu.ng/admission
Jami'o'i da suke Distance Learning a Nigeria suna da Dan Yawa sai dai ka Kara fahimta ko wace jami'a bace take yi, Idan a Nan Babu jami'an da kake so sai kayi bincike ka gano ko tana yi ko Kuma ba ta yi.
Sauran jami'o'in sun hada Jami'an Modibbo Adama dake Jahar Adamawa, jami'an Abuja, da jami'an obafemi owolowo dake ile ife da jami'an fasaha na ladoke akintola dake ogbomoso.
Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.
Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.
Kayi Share

Comments
Post a Comment