Federal Universities masu sauki da kudin registration din su a Nigeria



























Jami'o'i mallakin Gwamnatin taraiya masu saukin kudin registeration

Yau Kuma zamu yi bayani ne a Kan wasu jami'o'i mallakin Gwamnatin taraiya masu sauki da Kuma adadin kudin registration din su da a ke biya duk shekara.

Akwai masu tambayoyi masu alaka da wannan musamman neman sanin kudin registration na makarantun jami'a domin wani sai yaji kudin kafin zai San matsayin shi ya Kai Yaje ne ko sai ya Kara taru.

A wasu lokuta a baya Kudin registration na  jami'o'in Nigeria ya haura sama Wannan ne ma yasa masu sha'awan tafiya karatu da dama suke kasawa saboda Rashin abun Hannu ba tare da sanin tun a wancan lokacin ma Akwai universities masu sauki dai-dai talaka ba.

Idan har kana bukatan Sanin Universities a Nigeria masu saukin kudin registeration to wannan rubutun na kane kabi shi daki-daki har zuwa karshe domin sanin jami'ar da yafi dacewa ka nema.

Jami'o'i a Nigeria sun Fi shurin masaki, ma'ana Yawan su ya Kai inda ya Kai domin Bayan mallakin Gwamnatin taraiya (Federal Universities) Akwai mallakin Gwamnatin jahohi (State Universities) sannan Kuma Akwai universities masu zaman  kan su (Private Universities)

Universities masu saukin kudin registeration a Nigeria (Nigerian Cheapest Universities)

1. jami'an Ahmadu Bello dake zaria (ABU Zaria)

Ahmadu Bello University zaria babban jami'a ne Wanda a ke ji dashi a Nigeria musamman yankin arewa, Ba a sunan kadai ya tsaya ba har da saukin kudaden da a ke kashewa musamman na registration.



Rubutu Mai alaka: Jami'o'i da suke Distance Learning a Nigeria



Wannan jami'a tana jahar Kaduna ne a yankin zaria shi yasa za kaji ana cewa ABU Zaria, jami'a ce da a ke ji da ita Kuma tana da saukin kashe Kudi Kai in takaita maka ma wannan makaranta dai-dai talaka ne.

An bude ABU Zaria ne ranar 4 ga watan 4 a shekaran 1962 a garin Zaria jahar Kaduna, ABU ta girma Wanda har ta shiga jerin jami'o'i da a kafi ji dashi a kasar mu ta Nigeria.

Kudin makarantan kwata-kwata bai da Yawa ko da Yake bangarorin karatun suna da Yawa Kuma kudin kusan ko wane bangare da irin yanayin kudin da a ke kashewa Amma dai a takaice zamu iya cewa #27000 wannan shine kamar estimate na kudin makarantar.

Makarantar tana da bangarorin karatu (department) guda 82, Fakwalti 12 da guraren bincike 12, ABU Zaria a na saka ta cikin jami'o'i mallakin Gwamnatin taraiya masu karantar da ingantaccen karatu wa Dalibai.

ABU Zaria ta yaye manyan mutane a wannan kasa ta mu ta Nigeria wadanda a ke ji dasu har ma a ke ga kamar idan Babu su Nigeria zata kasance cikin yanayi na babban Rashi.

Daga cikin wadanda Abu Zaria ta yaye su Akwai wadannan manyan mutane kamar Haka:

  1. Sunusi Lamido Sunusi (Sarkin Kano na Yanzu)
  2. Ibrahim Shekarau (Tsohon Gwamnan jahar Kano kuma sanatan Nigeria Mai wakiltan Kano ta tsakiya a yanzu haka)
  3. Ahmad Makarfi (tsohon Gwamnan jahar Kaduna)
  4. Ibrahim Shema (tsohon Gwamnan jahat katsina)
Wadannan sune kadan daga cikin wadanda su kayi karatu a jami'ar Abu Zaria a jahar Kaduna Nigeria.

2. Jami'an Usman Dan Fodio dake sokoto

Jami'an Dan Fodio daya ne daga cikin tsoffin jami'o'i a Nigeria Wanda a ka kirkire ta a shekaran 1975 Kuma a na Mata lakabi da UDUS.

Tsayayyar jami'a ce Wanda take jahar sokoto wato birnin shehu, a yankin arewacin Nigeria.

Jami'an Usman Fodio an saka sunan ne domin tunawa da Mujaddadi marigayi Usman Dan Fodio Allah ya gafarta mishi.

Jami'an tana da bangarorin karatu da dama kuma suna yi har da remedial da koyar da ilimin addinin musulunci Wanda a turance a ke Kira da Islamic studies (IRS).

Kudin makarantan shi Kuma a takaicen takaitawa ya Kai #37000.



4. Jami'an Abuja (UA)

Ita Kuma jami'an Abuja tana Birnin tarayyar Nigeria ne wato Abuja Wanda a ka kirkire ta a ranar daya ga watan uku na shekaran 1988 (01 March, 1988)

Shi Kuma jami'an Abuja ana Kiran shi da U.A Ma'ana University of Abuja, shi Kuma kudin makarantan ya Kai Naira dubu talatin da shida (#36,000).

Jami'an Abuja ta kasance daya daga cikin manyan Jami'o'i na Nigeria Kuma Akwai tsarin karantarwa yadda ya dace a makarantar.

Ko da Yake ba bukatan sai an ce maka suna da Tsari tun da a Birnin tarayya take.
5. Jami'an Bayero dake Kano

Bayero University jami'a ce mallakin Gwamnatin taraiya dake Jahar Kano Wanda a da can kwakeji ne daga baya sai ta samu daman Zama jami'an Gwamnatin taraiya.

An kirki Bayero University ne a shekaran 1977 a jahar Kano a yankin arewacin Nigeria kuma ana mata lakabi da suna BUK wato Bayero University Kano.

Kudin makarantan zai iya Kai wa Naira #33,000.

6. Jami'an Alqalam dake katsina (Alqalam University katsina)

Jami'an Alqalam an fi Sanin shi da suna jami'an katsina, Shine jami'an musulunci na farko a tarihin Nigeria, jami'an a jahar katsina take.

Jami'an an bude tane a shekaran 2015 kaga ba a Dade ma da bude ta ba Kuma suna da bangarorin karatu, idan kana bukatan shiga ko neman karin bayani kaje Google ka rubuta sunan makarantan.

Kudin makaranta na wannan jami'a ya Kai kusan Naira 43,000.

Wadannan jami'o'i suna daga cikin jami'o'i Masu sauki a wannan kasa ta mu ta Nigeria.



Kayi like na shafin mu na Facebook a Nan
Asagist Facebook Page don ganin sabbin rubutun mu na gaba.

Kayi subscribes na blog din mu da email din ka don samun sabbin rubuce-tubucen mu ta akwatin email din ka.

Turawa abokan ka

Comments

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky