Hanyoyi 3 masu Sauki da zaka kirkiri android application
Barka da zuwa asagist da fatan kana jin dadin kasancewa damu, Idan kana da wani korafi ko tambaya zaka iya turo mana ta daya daga cikin hanyoyin da muka bayar na tuntuba.
Yau kuma zamu yi darasi ne wanda ya shafi kirkiran application na wayar android wanda baza ka kammala karanta wannan rubutun ba har sai ka san yadda zaka kirkiri application irin wanda kake bukata.
Akwai hanyoyi da dama na hada android application kamar yadda wata kila ka sani sai dai ba ta hanyar programming ko coding ne kadai ake hada android application ba, a'ah ko baka san programming ba zaka iya hada application kuma ka turawa duk wanda kake bukata
Hanyoyin gina android Application
Kamar yadda na baiyana a sama hanyoyin da ake hada android application dasu suna da yawa ba wai lallai sai ka iya harshe ko yaren programming ba wanda shi za a dauki tsawon lokaci kafin ka koya bare kuma har ka fara ginawa da kan ka.
1. Gina application da yaren programming: Ana kirkiran android application ta hanyar amfani da yaren programming musamman java wanda idan ka koye shi babu irin applicatio da baza kayi dashi ba.
Matukar kana son zama Android app developer to akwai bukatar sai ka koyi java amma ba wai daga java zaka fara ba domin akwai abubuwan da ya kamata ka fara dasu wato html da css.
A programming, Html da Css sune abu na farko da ake bukata ka fara koyo, da farko dai zaka fara ne da html bayan ka gama dashi ka zama kwararre sai ka fara Css, bazai yiwu baka iya html ba ka tafi kan Css. A'ah hakan ba mai yiwuwa bane.
Karanta: Hanyoyi 5 da zaka koyi Html da Css
Idan baka fara koyo tun daga kan html ba baza ka gane komai ba domin html shine mafari, za a iya kwatanta html da ajin farko da za a sa yaro idan ya kai munzalin shiga makaranta, zamu iya cewa aji daya kenan ko nursery.
Idan baka iya html ba ka fara koyon Css ko java kamar ba kayi primary bane a kai ka makarantar sakandare, akwai abunda zaka gane na karatu?
2. Application da ake yi a website: bayan kirkiran android application da java akwai kuma wata hanyar da ake bi don ginawa kuma wannan yana da sauki ba kamar na farkon ba, wannan hanyar kuwa itace hada application a shafin yanan gizo (Website).
Akwai website da dama a yanan gizo wadanda ake gina application na wayar android dasu kamar andromo da appsgeyser, wadannan guda biyun misalai ne kawai amma sun fi a kirga a yanan gizo.
An kirkire su ne musamman don gina application na wayar android wadanda kuma har kudi zaka iya samu ta hanyar application da ka koya.
Wani zai ce har kudi zan samu? Eh kwarai kuwa zaka samu kudi mai yawa, zan yi bayani a kai kai dai ci gaba da kasancewa da asagist.
Kyauta ne zan gina application a website da ake ginawa?
Wannan tambayar tana da muhimmanci domin akwai bukata kasan yadda tsarin yake kafin ka fara, ga tsarin irin wadannan website;
- Akwai wadanda suke bada dama a gina application a cikin su kyauta kuma ka sauke shi a kan wayar ka sannan ka turawa wanda kake so ba sai ka biya wani kudi ba, kudin da zaka kashe kawai bai wuce na datan da zaka yi amfani dasshi ba.
- Wasun kuma sai ka biya su kudi kafin ka fara gina application a cikin su
3. Amfani da Android application (Apk creator:
abunda zai iya rikitarwa ko bada mamaki shine ana iya gina application na wayar android da application na wayar android din.
Zaka iya mamaki amma a wannan zamanin ba abun mamaki bane domin abubuwa da yawa wadanda ba a san su ba a da can yanzu ana sanin su saboda yadda fasaha ta yawaita.
Yadda ake wannan kuma shine, zaka samu an gina application ne na android musamman don kirkiran wasu application na wayar android a kan su, misalin irin wadannan application akwa Apk creator wanda ake hada application har guda uku a ciki.
Sai dai shi kuma Apk creator ba ko wace waya ce take yi ba, zaka iya hada application sai zaka sauke shi kuma yaki sauka, ba kankanta waya ce matsalar ba.
Shi dai wannan application haka yake.
Wannan rubutun ya amfane ka?
Baiyana mana ra'ayin ka a comment
Ka taimaka mana da sharing


Comments
Post a Comment