Hanyoyi 5 masu sauki da zaka koyi Html da Css














Html da Css yare ne guda biyu wadanda ake gina website dasu musamman ga wanda bai yi nisa sosai a harkar gina website, kana neman inda zaka koyi Html da Css?

Idan amsar ka 'Eh ne' toh tabbas kana inda ya dace kuma a sannu zaka gamsu da abunda nake fada maka Idan ka kammala karanta wannan rubutu, zai taimaka maka sosai a matsayin ka na Dan koyo.

Menene ma'anar Html da Css?

Kamar yadda na fada maka a baya html daban Css daban kar ka dauka ko duk abu daya ne a'a abu biyu ne
Html kalma ce ta turanci wacce aka takaita ta (abbreviatio) Haka shima Css.

Ma'anar Html shine 'Hypertex Markup Language Css kuma Cascading style sheets. Wadannan yare ana hada website mai zafi dasu, abunda ake bukata kawai shine ka dage ka koye su yadda ya kamata

Idan ka gina website da Html da Css da sauran yarukan da ake hada website dasu, ba kada matsalan komai domin kai ne mai kula da komai ba kamar websites da ake ginawa a wasu shafukan yanan gizo ba.

Dalilin da yasa nace kai kadai ne mai alhakin kula da website din ka shine ai kai ne ka gina abun ka tun daga farko har karshe ba wai wani shafin yanan gizo kaje ka gina shi ba.
Akwai website din da ake gina su a wasu website, ba dogon bayani a kan wannan domin ba shine babban dalilin rubutun ba.

Wani abu mai kayayarwa da html da Css shine duk wani design da kake bukata za kayi shi, idan ka dauko code sai kawai kasa shine a inda ya dace  ka ajiye shi. Abu mai muhimmanci shine kasan code din kawai.

Zaka iya hada website mai kyau tun farkon lokacin da kake koyo saboda duk abunda kayi zaka adana ne akan computer ko wayar ka ma'ana saving kenan, Duk lokacin da za kaci gaba kana budewa za kaga aiyukan da kayi a baya sai dai ka dora a kai.

Zaka iya chanja duk abunda kaga bai maka ba daga baya, misali bayan kayi wani sabon abu a website din ka sai kayi running kuma kaga bai maka ba toh zaka iya editing din shi ta yadda kake bukata.

1. W3schools
Kamar yadda kusan kowa ya sani w3schools tsohuwar makaranta ce kuma nayi bayanai da dama a kan ta a wannan shafi mai albarka sai dai duk da haka baza a rasa abunda za a kara a kai ba.

Duk da W3schools ba ta yau bace amma har yanzu tashen ta bai durkushe ba, dubban mutane sun koyi Css da html a cikin ta kuma har yanzu mutane suna tururuwan zuwa koyo a wannan makaranta ta w3school saboda kwarewar su na tsara darrusa daban-daban.

Ba wannan bane kadai abun burgewa dasu, duk kayan karatun su kyauta ne ba kudin da zaka bayar na rijista ko sayan darasi.
Kyauta zaka koya har ka iya kuma ka fara hada website irin wanda ran ka yake so.

Bayan wadannan garabasa akwai wani ma wanda muhimmancin sa yafi a kirga, wannan abu kuwa shine certificate. Bayan ka  kammala karatu zaka iya yin jarrabawa kuma zasu baka har da certificate amma certificate din ba kyauta bane sai ka biya zasu baka.

2. Lynda
Su ma lynda suna cikin na gaba-gaba a harkar koyar da Html da Css kuma ba a nan kadai suka tsaya ba har graphic design zaka koya, Zaka kware sosai Idan ka shiga wannan makaranta.

Tsarin curriculum din su kusan yana tafiya ne dai-dai da na makarantu don haka idan kai dan koyo ne wannan zai fi dacewa da kai, a wannan makaranta ma zaka samu karuwan ilimi na programming.

Bayan ka zama Member a lynder zaka samu daman kallon videon su har da karin garabasar na kyauta, zaka iya gina website amma ka fara da html tukuna domin shine abu na farko da ake farawa idan za a gina website musamman ga dan koyo.

3. Codecademy
Wannan ma ba sai nayi dogon bayani a kan shi domin shima sananne ne a gurin masu koyon Html da Css musamman wadanda suke ziyartan wannan shafi na mu mai albarka.

Suma dai kamar sauran ne kuma suna da Hikima sosai na tsarawa da kuma iya koyarwa, idan kana bin darasin su cikin kankanin lokaci zaka koyi abubuwa da yawa wadanda da can baka iya su ba

Suna karantarwa yadda ya dace domin wanda bai da ilimin yaren programming ya gane ba tare da cin lokaci mai tsayi ba, ka shiga Codecademy domin fara loyo

4. Udemy
Udemy daya ne daga cikin makarantu masu dadin mu'amala da daliban su, suna koyarwa tun daga yadda ake koyon Html da Css har zuwa yadda zaka kirkiri website mallakin ka

Udemy zaka koyi Html da Css cikin sauki sai dai kuma ba kyauta bane kamar su w3schools, a wannan makarantar yanan gizo ta Udemy sai kayi register kafin zaka fara koyon Html, Css har ka hada website din ka.

5. Simplilearn
Simplilearn suma suna daga cikin sanannu kuma suna bayar da certificate kamar w3schools, Bangarorin na su da fadi saboda ba Html da Css kadai zaka koya ba hatta hada Game ma zaka iya idan ka kaaance da makarantar

Sai dai suma na kudi ne sai kayi register zaka iya koyan komai a ciki.

Wadanna sune hanyoyi guda biyar (5) da zaka koyi Html da Css wadanda suka kunshi na kudi da na kyauta kuma duk wanda ka dauka a cikin su zaka koyi Wadannan abubuwa 2 kamar yadda kake bukata

Wasu suna ganin wai a na kyauta baza a iya koya yadda ya dace ba wai sai a na kudi ne mutum zai koya da kyau wanda kuma wannan zance ba haka take ba domin wadanda suka koya a na kyauta sun fi shurin masaki

Karanta: Yadda zaka kirkiri privacy policy cikin sauki

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Baturiyar da tazo ganin saurayin ta a Nigeria ta mutu Sanadin Rashin Lafiya

Bluegrass Spirit Bursary for International Students at University of Kentucky