Hanyoyi 3 masu Sauki da zaka kirkiri android application
Barka da zuwa asagist da fatan kana jin dadin kasancewa damu, Idan kana da wani korafi ko tambaya zaka iya turo mana ta daya daga cikin hanyoyin da muka bayar na tuntuba. Yau kuma zamu yi darasi ne wanda ya shafi kirkiran application na wayar android wanda baza ka kammala karanta wannan rubutun ba har sai ka san yadda zaka kirkiri application irin wanda kake bukata. Akwai hanyoyi da dama na hada android application kamar yadda wata kila ka sani sai dai ba ta hanyar programming ko coding ne kadai ake hada android application ba, a'ah ko baka san programming ba zaka iya hada application kuma ka turawa duk wanda kake bukata Hanyoyin gina android Application Kamar yadda na baiyana a sama hanyoyin da ake hada android application dasu suna da yawa ba wai lallai sai ka iya harshe ko yaren programming ba wanda shi za a dauki tsawon lokaci kafin ka koya bare kuma har ka fara ginawa da kan ka. 1. Gina application da yaren programming: Ana kirkiran android applicatio...